
______________
Sukumbiya Danye Me Kyau 1
Tattasai 2
Attaruhu 3
Cabbage
Albasa 1
Curry
Maggi
Mai
:
Zaki Wanke Kifinki Da Lemon Tsami Ko Toka Domin Fidda Karninsa Da Kuma Yaukin Dake Jikinsa Sai Ki Yanyankashi Amma Sai Kinyi Sauri Domin Idan Kankarar Jikinsa Ta Narke Zai Iya Dagargaje Miki Wajen Aikinsa, Sai Ki Barshi Yasha Iska Domin Ya Tsane,in Ya Tsane Sai Ki Barbadeshe Da Magi Ki Jerashi A Farantin Gashi Kisa Shi A Oven Idan Kuma Baki Da Oven Din Sai Ki Soyashi A Mai Amma Karki Yawaita Juyashi Gudun Dagargajewa,
Idan Yayi Sai Ki Aje Ki Ki Dauko Attaruhu Albasa Tattasai Da Cabbage Da Kika Yanyanka Kika Wanke Ki Dora Kasko A Wuta Kisa Mai Ki Soyasu Kisa Maggi Da Curry Idan Sun Fara Hade Jikinsu Sai Ki Dan Sa Ruwa A Ciki,sannan Ki Kawo Kifin Kisa A ciki Yayi Kaman 10minutes Saiki Sauke,ana Ci Da Bread Ko Haka Kawai Da Dan Juice.
-------------------------------------------------------------
Enter your comment...Masha Allah
ReplyDelete