
KAYAN HADI
A) Abarba (Madaidaiciciya)
B) Kwakwa ( Babba)
C) Madara Peak (Gwangwani 1)
D) Sukari (kadan idan anaso)
E) Flavour (mai ƙamshin Abarba da ƙamshin Kwawa)
YADDA AKE HADAWA:
Uwargida ki fere abarbarki tayi tas, sannan ki yankata madaidaiciya Ki saka a blender ki markada bayan kin juye sai ki tace. Agefe ɗaya kuma ki fasa kwakwarki ki yanka kisa acikin blender, ki markaɗa sai ki tace akan abarbar. Sannan ki juye madarar peak aciki. Ki narka sukarinki ki zuba kisaka a fridge ko ki fasa kankara akai. Asha dadi lafiya.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.