shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 26 November 2016

Waye sanadi? 71 & 72


[11/21, 8:09 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣1⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com wani irin bakin ciki ya cikan zuciya tare da tahowar hawaye "na koyi uwaka in har zan yi kewarka zanyi kewar fitowata daga cikin wutar da na shekara ina shan azabar ta na fada a fili. haka na zauna babu abinda nake sai kuka babu kuka abinda yake tsaidani daga yinsa sai sallah tunda na idar da sallah isha'i na fara jin tsoro yar hayaniyar da nake ji da kuma surutan mutane a baya tunda akayi sallah ban kara jiba don haka duk hankalina ya tashi koh motsi naji sai na hau dube-dube har wajen karfe daya lokacin ina bakin kofar falon a zaune, kaina ya hau ciwo ga zazzabin daya rufeni ina zaune naga kofar tana budewa ya shigo kwata-kwata na kasa dago kaina na kalleshi. har yanzu baki bar kukan nan ba, kina nema ki haifar wada kanki ciwo ki daga min hankali. ganin ban dago kaina ba yasa ya karaso ta tsugunna a gabana mu wife me yake faruwa? ya kai hannunsa kaina yana kokarin dagawa iya karfina nasa na hankade shi na dago fuskata idanuna da kyar naiya daga su nace. kada wannan munanan hannunka su kara karambanin taba jikina na tsaneka wallahi imran da na bude ido na ganka gara ace idanuna sun dauwama a rufe ka kauce a gabana bana kaunar ganinka," ina fadar haka naja jikina na shiga cikin dakin. **** **** **** **** **** *** Don Allah rukayya kiyi hakuri ki bar kukan nan karkija wata cutar ta kama ki tunda kuka dawo kullum kina cikin kuka da damuwa, insha Allahu safiyya tana nan lafiya, kuma zata dawo duk irin damuwar da kika shiga baki kai yaran nan ba hajiya hassana (mahaifiyar rukayya) ta dago idonta cike da ruwan hawaye ni dai don Allah hajiya ku barni na koma can na dubo ta, ki taimaka kisa baki abba ya barni wallahi yaya salim ba zai dubata sosai ba... kuka yaci karfinta ta kasa karasawa gaskiya ba zan saka baki ya barki ba, kiyi hakuri insha Allah salim ba zai dawo ba sai tare da ita, kina ganin alhaji da kawunki har can suka je suka bada cigiyarta kina ganin jiya kawunki ya dawo aka tura salim rukayya yanda kike kaunar safiyya haka muke kaunarta, wallahi inason safiyya kamar yanda nake sonki ki duba kiga yanda hankalin kawunki ya tashi kamar ke kika bata. hajiya ni dai ki min taimakon nan kisa abba ya barni koda kawu ne mu kara zuwa na san sadiya za a bar ta muje mu kuma bamu san halin da imran yake ciki ba, tun ranar da yazo muka gaya masa ya suma aka kai shi asibiti washe gari muka kirawo wayarshi baya shiga ina tunanin ko ranar da ya fadi yan makaranta suka zare masa abu ina ganin harda wayansa. in har kinaso nayi wa alhaji magana sai kin daina wannan kukan to wai me zana ki gayawa iyayenta halin da ake ciki kinga yau sati biyu kar suyi tunanin har yanzu baku dawo ba, hajiya su iyayen safiyya suna tunanin tafi shekara da bata saboda tun ranar dazamu tafi har muka zo nan ta kwana ta bar gidansu da zummar bazata koma ba." cikin rashin fahimta hajiya hassana tace ban gana ba, nan take ta zayyane mata labarin da safiyya tabata, Allah sarki baiwar Allah dole yarinyar nan ta shiga damuwa, amma wannan kakar tata batayi mata adalci ba data gaya mata wannan labarin ita kuma safiyya tayi wauta da bata tsaya ta saurari abinda mahaifiyarta zata gaya mata ba nasan ita kanta mahaifiyar tata baza taso haka ya faru a kanta ba, kuma ita safiyya bai kamata ta yanke hukunci cikin bacin rai ba, data bari ta saurari bayanin ummanta idar har vai gamsheta ba sai tayi tunanin mafita wallahi hajiya kullum haka nake nuna mata tun muna makaranta amma taki ganewa ku... kema da laifinki rukayya hajiya hassaja ta katse ta hajiya wani irin laifi? me yasa tun ranar da kukazo kuka kwana baki gaya min ba??? 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/22, 8:29 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣2⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.abbagana.cf hajiya nima a lokacin bata gayan ba sai da muka je makaranta take gayan halin da take ciki, to me yasa baki bugo waya kin gaya min ba har kukazo duba alhaji amma baki gayan halin da take ciki ba? ni fa hajiya nayi zaton fadan dana yi mata ta hakur yanzu ke kina tunanin safiyya tafiya tayi da kanta ko dauke ta akayi? gaskiya hajiya tunanina yafi karkata a kan dauke safiyya akayi, saboda ana gobe zamu taho mukayi fada ta dawo tana bani hakuri da kanta kuma harda ita muka hada kayanmu fitarmu da sadiya bamufi munti goma ba muka dawo bata nan. Dan Allah hajiya ku barni na nemo safiyya ban san a wani hali take cik.... kuka yaci karfinta ta kasa karasawa hajiya ta juyo ta jikinta tana shafa kanta kamar karamar yarinya tare da gaya mata maganganu dazasu kwantar mata da hankali haka har barci ya dauketa. hajiya hassana ta rafka tagumi ta fada cikin tunani wannan wace irin kauna rukayya takewa safiyya yarda batanta yake neman wargaza farin cikin yata mace guda daya bama ita daya ba harda ni kaina da duk wasu makusantanmu. ya Allah ka bayyana yarinyar nan, kasa tana hannun na gari don girmanka. ta durt a fili tare da zubowar hawaye a fuskarta. sai wajen karfe biyar rukayya ta tashi ta ganta a falo ita daya dakinta ta shiga. tana toilet wayarta tayi kara data kammala alwala sannan ta fito tana fitowa aka kara kira tayi saurin dagawa hello kawu' daga can barin da akayi kira aka amsa mata cikin katuwar mury ba kawunki bane, muna bukatar miliyan biyar in har kina kaunar kawarki kina kuna kaunar taci gaba da shakar numfashi mun baki kwana uku, ana fadar haka aka katse jikinta na rawa ta fito tana kiran hajiya sukaci karo da kawunta yayi saurin rike ta yana girgiza ta lafiya rukayya, tana mayar da numfashi kamar tayi gudun shekara tayi mishi bayani. ina number ta aka kira dashi? tayi saurin bincikar received call tana dubawa taga hidding number bata san lokacin datayi wurgi da wayar ba tana kuka daidai lokacin hajiya ta fito tana tambayar lafiya ganinta da kawu ta tsaya tana kallonta sannu da zuwa tace wa kawu bai samu damar amsawaba har sai daya lallabata tayi shiru tare suka zauna akan kujera yana cigaba da lallabata ya juyo wajen hajiya hassan yana tambayarta alhaji ibrahim yana ciki? kanta bashi amsa yashigo bayan sun gaisa ya maida kallonsa ga rukayya wadda take ta faman share hawaye har yanzu kukan kike koh? bazakiyi hakuri ba abba kirafa akayi ta waya wai na bada miliyan biyar a kawo safiyya don Allah ku hada kai da kawu a ba su har imran zanwa waya shima ya bada wani abu a hada son Allah ku taimaka abba yace ina number da aka kiraki muyi magana in har zasu kawo ta ko miliyan nawa ne sai a basu kawu yace nifa ina tunanin wasu macuta ne suke so su karbi kudi a banza, hidding number sukayi suka kira hajiya hassana tace ni kam ina ganin a bari in suka kara kira sai su fadi inda suke a kai musu su bamu safiyyan ko hankalinmu zai kwanta, shi kenan rukayya kiyi shiru bana san kukan nan zamuyi shawara da kawun inyaso har in sun kara kira kice suyi miki kwayancen inda za a same su sai a kai musu kudin. sun jima suna lallabata har sai datayi dariya ta mike kawu bara na debo maka hotunanmu tana shiga dakin ta dauko jakarta ta zaro hotuna cikin album ta fito bata kula da farar takarsa ta fado ba sai bayan sallar magariba ya tafi tareda yaya isa hajiya ta mike bara na kaiwa alhaji abinci tana shiga dakinta taci karo da yar farar takardar har ta wuce ta dawo tq dauka ganin rubutun yasa tayi saurin warwarewa don taga me aka rubuta. ta dora idonta akan rubutun. ta fara karantawa:...... 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).