[10/24, 8:15 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
5⃣3⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
Cikin sanyin murya nace na gode kuma insha Alllah zanyi amfani da shawaranki.
Ta juyo wajen yarinyar da ta kira da aysha suna hada ido tayi saurin fita. Bayan ta gama dubani na dawo kujera na zauna tana murmushi tace kinga muna ta kallonii koh? Ina zaune aysha tace taga mai kama da dady kamar kanwarsa ni kaina dana ganki nayi mamaki sosai ina son yayana sosai dan haka da naga kuna kama kema sai naji ina sonki a raina" nace haka lamarin Allah yake sai kaga baka san mutum ba amma in wasu suka ganka sai suce kana kama da wani, wanda suke fadan baka sansuba ba ka kuma taba ganinsa ba
ta zaro wani dan kati ta mikamin ga wannan duk ran daki kazo ki dinga nema na ba tare da kin bi dogon layi ba na karba ina godiya mun jima tana ban shawarwari.
Ina fitowa na samu a daidaita sahu na shiga har kofan gida ya kaini babah tana zaune tana kada abu na shigo ta hau raba ido baba me kike kallo ina alhajin da kuka tafi tare ai tunda ya kaini ya taho na karasa na zauna a kusa da ita ta mike bara na miko miki abinci.
Bayan na gama na juyo wajen baba nace nayiwa alhaji magana kan ya rage zuwa kinga babu aure a tsakaninmu bai kamata ya dinga shigemin ba har ma ya dinga kaini unguwa maganar mutane bata da dadi in haka nayi masa magana ga mallam nan shine wakilina tunda daman a wajensa ya aureni duk wani hakkina ya dinga bashi. Babah tayi saurin katse ni kice kin koreshi ya barki da wahala kinyi daidai kin kyauta bab...." kinga yi min shiru har kinda da maganar da zaki gayamin wayasan abinda ki kayiwa alhaji mukhtar ya barki da yarki gashi yanzu ta gudi ta barki shine wannan ma kike so ki cuci abinda zaki haifa, kina ganin nan gaba haka zaki zama mana tashin hankali ina hawaye na dago babu auren na kuma ga kullum yana gidannan zai iya zama matsala ayi mama mummunar zato
Sannu wadda bata so ayi mata sharri ke gak...." kan ta karasa mallam ya shigo naji duk maganar da kuke rakiya tafiki gaskiya tasan meye rayuwa kuma yanzu alhaji nasir ya bar wajena mun gama magana don haka ban san na kara jin kina wata magana mara amfani ya juyo wajena ke kuma maganar da zsn gaya miki karki dora SANADIN batar safiyya a wuyan alhaji nasir ki dora SANADIN batan ta a wuyan magajiya, to inda bata gaya mata wannan mummunar zancen ba babu abinda zaisa tabar gabanki kuma kici gaba da kai kukanki wajen ubangiji har Allah ya juyo da hankalinta ta dawo wajenki.
Ya miko min kudi munyi da alhaji nasir duk wata zai dinga kawo kudin abincinki gashi kuma ya bayar wannan ko bakida lafiya za'a dauka a sai magani sannan kuma da zuwa awo, don haka dukk wata zai dinga zuwa ya kawo.
Ni dai bance komai ba nasa hannu na karba dan basune a gabana ba tunanin yata ya cikemin zuciya.
Ina kika shiga safiyya ki taimaka ki dawo ina maganar cikin zuciyata ashe har ta fito fili maganar babah naji daga baya tace: yanzu ko kunyata bakya ji kike fadar haka? Nayi saurin juyowa babah ba magabar da nayi ta hau salati yanzu bakin san kina maganar safiyya ba? To Allah ya kyauta miki wallahi in baki rage tunaniba, sai ciwon zuciya ya kamaji tana fadar haka ta shiga cikin daki.
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[10/25, 9:16 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
5⃣4⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
www.abbagana.blogmr.com
**** **** **** **** ***
waike malama ba kya jin wayarki na karane? na dago fuskata a hade nace ina jinta toh zaki daga bane? momy bana raayin dagawa in kinsan bazaki daga ba meyasa kika bada lambarki? wa nake bawa numberta? wannan dinnan ne da yake kirana wai bashi da sunane? ta fada tana haranta wanda yazo ranan oh muhammad na daga kai, mikomin wayar banyi musu ba na miki mata; Assalamu alaikum, muhammad kana lafiya? lafiya klau aunty momy safiyya bata nan ne? muhammad tana toilet ne ya akayi? aunty momy daman ce mata zanyi yau zanzo mu gaisa ta kuma ki dagawa" kayi hakuri kasan babyn tawa sai na kaita an duba kwakwalwarta ina tunani akwai matsala me yasa kikace haka aunty momy? to muhammad inna gaya mata magana bata yarda ga dan banzan taurin kai, dan haka dole na kaita a dubata yana dariya yace shikenan innazo sai muyi maganar inta fito ki mikamin gaisuwata okey muhammad muna jiranka ka gaida mutanen gida tana gama wayar ta juyo tana kallona banda ruwan hawaye babu abinda yake bin fuskat kan tayi magana na katset momy ni kike cewa banda hankali zaki kaini a dubani koh? kai tsaye taban amsa to kina da hankalinne? na girgiza mata kai na mike zan fita jinayi kamar zan fadi nakai hannuna na dafe kaina da sakin wata razannaniyar kara wannanda harnima ya razanani🙂.
A hankali na dinga kokarin bude idona naji na kasa hannu na kai fuska naji wani sassanyar murya ta doki zuciyata sannu safiyy.
kin tashi abin kamar a mafarki naji muryan ba shiri nayi saurin bude idona ina kallonsa tare da juyaw ina kallon inda nakw kwance ban wahalar da kwakwalwata ba wajen gane inda nake ba wata asibiti to waye ya kaw....... maganarshi ce ta dawo dani daga tunani sannu safiyya bara na kirawo likita ya dubaki momy ce ta shigo najuyo wajen tare da fadin me ya kawoni asibiti, bakya jin dadine shine na kira muhammad ya kawo mu asibiti inajin haka nayi saurin mikewa ina kokarin saukowa daga gadon ta karaso da sauri"meye haka bakya ganin drip ne a hannunki. na juya ina kallon hannu na kai zan cire naji an rike hannun "karki cire safiyya ki bari ya kare." na zabga masa harara bazan bari ya kare ba meye ruwanka da rayuwata."
🅰bbagana hausa novels @ faceebook.
[10/25, 9:41 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
5⃣5⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
na juyo wajen momy nace ce miki nayi banda lafiya da zaki dauko mara hankali ku kawo asibiti ta rike hannuna tana murmushi am sorry nasan nayi laifi a min afuwa. na juyo wajensa kasake min hannu ko nidin ba yar isaka bace irinka nika dakain zan bada shaidar haka amma kiyi hakuri ki bar drip din ya kare kyaji karfin jikinki, dan Allah ki taimaka safiyy yana maganar yana girgiza kai cikin tsawa nace to hannunka ne da ba zaka sakar min ba? to kimin alkawarin bazaki cire ba ki taimaka kanwata. waye kanwartaka? kiyi hakuri don Allah kibar drip din nan momy tace muhammad sakar mata hannun bara na kira abba shi yayi mata magana.
ta zaro wayarta tare da kiransa kira daya a dauka hello Abba bayan sun gaisa take gaya masa tana gama gaya masa ta sa wayar a kunnen naji muryansa safiyya kiyi hakuri ki bari ya kare. abba ce min tayi fah bani da hankali kinga ki rabu da ita ranar monday zanzo amma ki bari ruwan ya rake saiku tafi kinji yat ina kuka nace to abb yayi saurin cewa bana son kukan nan kiyi shiru kar kanki yayi ciwo ina jin ya katse na kaudar da kaina na kwanta momt tace har kun gama banko tankataba na mayar da idona na rufe baby bara naje na samo miki abinci.
ya karaso ya tsugunna kiyi hakuri safiyya me nayi miki kike min haka? ki tausayamin safiyya duk wanda yake nuna maka kulawa bai kamata ya zama abin gudunka ba dan Allah ki tausayamin na yarda bakya sona amma ki amince na zama dan uwanki ki ban matsayin yayanki koh kaninki na miki alkawarin maganar soyayya ba zata taba shiga tsakaninmu ba har abada, dan Allah ki tausayamin duk maganar da yake idona suna rufe sai da naji muryarsa tana rawa yasa na bude idona cikin dabara ba tare da ya gane ba, ji nayi kirjina yana bugawa sakamakon ganin ruwan hawaye a kwance cikin kyakkyawan fuskarsa.
Dan Allah kiyi magana safiyya ko zanji dadi ki gayamin kin amince mu dinga gaisawa.
bansan lokacin da bakina ya furta na amince, yaji maganar kamar cikin barci yayi sauri dago kai yana murmushi safiyya na gode, na gode ya mike da sauri bara na kira likita. momy ta shigo tare dasu sadiya. farida tace yanzu wannan ce mara lafiya? ruky kika wani daga hankalinki haka, na juyo ina haranta sadiya tace sannunki kam nasan ciwon love ne kawai tana kunyar gaya mana amma ba komaii ni zan shigar dake, ban ko mata magana ba.
sallama yayi tare da shigowa shi da wata nurse, ta karaso wajenta bayan ta gama ta fita sadiya ta juyo wajen muhammad tana dariya yau daiga muhammad angon safiyya rike baki yayi yana dariya sadiya bar fadan haka kar kisa ta janye amincewa da mukayi yanzu yana maganar yana kallon agogo dake jingene a sama. karfe takwas ruwa ya kare na azakzali momy taje takirasu a ciremin....
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[10/31, 8:01 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
5⃣6⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
bayan ta gama waya ta juyo waike malama ba zaki bari ya kare ba kin..... kan ta karasa nasa hannuna na cire da kaina, na shiga uku me yasa kika cire na mike tsaye niba ce miki nayi banda lafiya ba kuka kawo ni nan, wai ya akayi kuka kawoni ina barci? abin ya baya momy mamaki ta tabbatar abinda zuciyarta take gaya mata tabbas saffiya tana da matsalar aljannu ina mafita ta tambayi kanta kan ta samu mafita maganarta ne ta katse mata tunani.
momy ya akayi kika daukoni ina barci? toma ya akayi nayi barci kinga bara na kira dr a dubaki tana fita muhammad ya shiga safiyya har ya kare na daga masa kai ina aunty momy ya tambayeta taje kiran likita okey bari nayi sallah nazo mu tafi.
momy ce ta fito bako sallam ta juyo tana kallon muhammad tace gaskiya muhammad ina ganin ciwon safiyya bana zuwa asibiti bane cikin mamaki ya juyo rukayya saboda me kikace haka? nan take ta gaya masa maganganun da sukayi da safiyya ya girgiza kai to momy wannan wani irin ciwone? kan ta bashi amsa ya cigab sa cewa ina ganin tan da mutanen boye, nima haka nake tunani yaceto ina mafita tace kaine zaka samar mana mafita mu din wa muka sani a garin nan? yadi minti uku baiyi magana ba can yaja dogon numfashi shikenan rukayya zanyi duk wani kokari don neman lafiyar safiyya.shikenan muhammad na gode rukayya me abin godiya? muhammad sole na maka godiya yana dari yace aunty momy imran shine sunana na gaskiya ina amfani da muhammad ne dan kada safiyya ta ganeni tace ban gane ba au momy baki da labarin aljani imran da yake kiran safiyya lokacin da kuke makaranta, ta rike baki tana dariya kaine imran aljanin wayar safiyya? kai ya daga amma kaban mamaki kaine mutumin da ya haukata baby gaskiya saina gaya mata anty momy ki rufan asiri karkija a janye alkawarin da aka min. wani alkawarine daban sani ba? na gaya mata babu maganar soyayya tsakaninmu da ita za dai mu dinga gaisawa hmm lallai imran har yanzu baka san wacce safiyya ba bara naje daki kada ayi minu fushi okey aunty momy gobe zanzo hudu na yamma amma kan sannan zanje wajen wajen malami nayi masa bayani.
ina sallah ta shigo toilet ta zarce ta dauro alwala ta fito bayan ta idar ta juyo shine kika wucw bako salkama? to momy dole ne sai nayi sallama? babu sole amma kin masa alkawarin zaki dinga sauraransa ku dinga gaisawa kuma kinsan muhimmancin alkawari to inya dawo wata rana zan masa sallama momy yunwa bakeji toh waye zai fita a wannan darwn ga take away dinda imram ya siyamana nima shi zanci na kwanta.
sai karfe uku na fito daga dakinmu kai tsaye na wuce cikin makaranta sanye nake da doguwar riga baka na nade fuskat da dan mayafina babu komai a hannuna sai book guda daya muryar momy naji daga bayana tace sai yanzu akaga damar zuwa class din? kuka kama hanya koh jirana kunkiyi, keh dakika tsaya shiritanki shine zamu jiraki? kai momy kefa aunty nace kuma abba yace ki dinga lallabani'zan lallabaki ko dan darajar yaya imran kai momy har yafi abba matsayi? ba haka nake nufi ba kowa da matsayinsa.
karfe biyar wayata ta hau kara ina dubawa labar na wayar imran ne na ajje can wata zuciyar ta tunamin alkawarin da nayi masa nayi saurin daukan wayar
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[10/31, 8:36 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
5⃣7⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
safiyya kina lafiya? can kasan makokorona na amsa da lafiya kuna cikin makaranta ne? na girgiza kai kamar yana ganina baki ban amsa ba ina tambayarki, bana girgiza kaiba to ai safiyya kin san ba ganinki nake ba ballantana na ga kin girgiza kai kiyi hakuri ki ban amsa ni ina hostel momy kuma tana cikin makarant su dasu farida shi kenan amsar da kake so na baka. shi kenan kanwata nima gaya miki zanyi nazo mu gaisa ina jiranki cikin makaranya da fatan kina sane da alkawarinmu na zuwa muna gaisawa yana fadar haka ya katse nabi wayar da kallo.
wannan mutumin zai dinga fakewa da nayi masa alkawari ya takurawa rayuwata gaskiya sai na taka masa birki, hijabi nasa na na fito yana zaune cikin motarsa tunda na tawo ya kasa dauke idonsa akaina babu wata kwalliy a fuskata amma hakan ta masa wani irin kyau mai makantar da zuciya gabaki daya, yana yin komai na yana burgeshi ya Allah ka mallakan safiyya ya furta a hankali tare da lumshe ido ta karaso fuskanta a hade.
jin alamun an tsaya a ganansa yayi saurin bude ido yan murmushi muka hada ido nayi saurin dauke idona"safiyya ki shigo mana? nan ma ya isa sauri nake ina aiki a daki fitowa yayi daga cikin motar ya dawo kusa dani sanye yake da kananun kaya wanda suka dace da kallar fatar jikinsa, tunda bazaki shigo ba ni na fito sai na tsaya kusa da kanwata. da sauri nace wacece kanwar taka?? safiyya man koba kanwata bace? gaskiya ni ba kanwarka bace saboda me kika ce ha? ni daya ummana ta haifa banda yaya bare kanne to aii ummance ta haifen kinga na zama yayanki ko babu kara, kan na bashi amsa wayarsa tayi kara yayi saurin zarota daga aljihunsa hello khadija ya akayi? sun jima suna hira sannan sukayi sallama ya juyo wajena yace wata kanwatace yae rigima wai na dawo gida bata gaji da ganina ba.
nace to ka koma mana nima na gaya maka aiki nake, in gaisuwane kazo yi mun gaisa bari na tafi ina san ganin momy zan zauna na jirata ki tsaya muyi dan hira kafin tazo.
nafa gayamak aiki nake ka rabu dani in kanaso muci gaba da gaisawa to duk abinda na gaya maka karkace zaka gyaran koka takuramin ina fadar haka najuya na tafi.
yana tsaye cikin mamaki yaji sallamar momy imran yanzu kazo? yayi saurin juyowa yana kallonta aunty momy na juma ke nake jira harm safiyya tazo mun gaisa, aunty momy naje wajen mallami nayi masa bayani to shine yace nazo da ita.... momy ta dago kai da sauri hmm imran kasan inzamu to safiyya bazata taba yarda muje ba "ai aunty momy baki tsaya na gama gaya miki ba, yana gayan haka nace mallam baza ta taba zuwa ba. wani rubutu ne ya bani nakai mata in ya kare sai na dawo 'imran bansan wani irin godiya zan maka ba nasan kanason safiyya tsakani da Allah ina maka fatan Allah ya baka safiyya amin aunty kasan wani abu imran? ya girgiza kai tunanin yadda zann mata ta dinga shan rubutun nake nima nayi tunanin haka dan na hango taurin kan safiyy za a sha wahala kan ta amince.
momy ta hau dariya karka samu damuwa imran yanzu zanwa abba waya nayi masa bayani. kai naji dadi kin iya kawo shawara bari naje gidan kanwarmu ta damu na dawo kisan nima dan gatane kamar safiyya na au har ta zama taka? momy ba kekika bani ita ba.
ina kwance ta shigo hannunt dauke da jakar rubutu kan nayi mata magana tace yanzu muka gawa waya da abba, amma koki kawo da gudu mugaisa ke nima ba hira mukayi ba turo abonkisa yayi ya kawo mana rubutu. cikin mamaki nace rubutu kuma? ta daga kanta tare da nunamin jakar hannunta. to ce mai kikayi bamu da lafiya? kewa yayi na tsari ne saboda mutane kuma bamu san zuciyarsu ba na hau dariy gaskiya abba yana sonmu da yawa, gara ana taimakawa da rubutu saboda mayu irinsu saifu da .....sai kuma nayi shiru ta dago kai ta harareni da kuma wa?? momy ba wani abu zance bafa.
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Waye Sanadi?? 53--57
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.