[10/19, 9:27 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
To mallam yaushe zamu tafi? Rakiya insha Allah gobe zamu tafi ku hada kayanku, da sauri rakiya ta mike dan ita duk ta gaji da zaman garin tana shigowa dattijuwar da take sakar mata fuska ta shigo tana dariya tace rakiya kina murna zaki gudu ki bar mahaifarki? Ta juyo wajen babah yanzu sofi in kin tafi sai yaushe? Nan take babah ta juya baki tayi magana da fillanci rakiya sai kallonsu take cikin mamaki har suka kare maganarsu.
Karshe bakwai suka rakomu tasha, shabiyu daidai muka shigo cikin garin kano mota muka dauko har kofar gida ta kawo mu koda yana zaune a kofar gida yana ganin tsayawar mota yayi sauri tashi tare da karasowa yana dariya sannunku baffa yanzu Alhaji nasir ya bar nan sai muka fara shiga gidan mallam mado habi tace rakiya kin dagawa alhaji nasir hankaki kullum ai sai yazo nan yanzu haka gobe suke shirin tafiya da kado.
Sai da mukayi sallah sannan muka fito karfe takwas mukaji sallamar alhaji nasir lokacin ina sallah sai babah ce ta amsa masa yayi saurin shigowa har yana tuntube sannunku banah kun dawo lafiya? Lafiya klau alhaji ya iyali, lafiyansu klau. bayan na idar na juyo muka gaisa muna gaisawa na mike nayi daki, sai karfe goma ya mike, nabah ina son magana da rakiya har na fara barci naji babah tana tashina kizo Alhaji zai tafi na mike ya fito yana tsaye a sororo na karasa rukkaya in sati biyu sai da akayi wata daya, fuskata a hade nace haka Allah ya tsara, rukayya ya kamata ki fara zuwa awo dan haka gobe zanzo na kaiki na mika masa ledar da babah ta ban na bashi tsaraba.
Ina komawa daki na dauko hoton safiyya ina kallo naji hawaye yana zubar mini kina ina nana ki dawo na ganki kin saka rayuwata cikin matsala ban san wane hali kike ba kina ina nana? Nan dake zuciyarta ta hau rawa tana son tayi kuka.
Washe gari kare tara alhaji nasir yazo muka tafi asibiti nasarrawa, muka nufa bayan yayi parking ya juyo yana kallona fukarshi dauke da murmushi ya zaro kudi ya mikomin karfe sha biyu zan dawo na dauke ki. Bana bukatar ka dawo ka daukeni zan koma da kaina me ka dauken ne babu aure a tsakaninmu meye kuma kake shiga rayuwata fatana na haihu lafiya ka karbi abinka cikin mamaki yace rukayya wani abu na miki kike gayamin wannan munanan kalaman? Bakayi komai ba gaskiya nake gaya maka wani irin kallo kake so ai mana ka riga ka sakeni meye kuma kake bibiyar rayuwata kana so mutane suyi mana mummunar zargi? Na gode rukayya amma karki manta kina dauke a cikina hakkina ne na kula da lafiyarki da abinda yake cikinki, to daga yau bana bukatar haduwarmu ga mallam nan shine wakilina duk wani abu da zaka bamu to ya biyo ta hannunsa na gaji da ganin fuskarka kullum muka hadu sai na tuna yata wadda kukayi min sanadin rabamu da ita". Rukayya daman kalkon da kike min kenan, naji dadi da kika gayan abinda yaje ranki amma nayi mamaki sosai da har kika iya budan baki kika gayan haka ashe zaki iya mancewa da alkhairina a gareki, ban taba zaton haka a gareki ba laifin wani bayan shafan wani uhum daman ance dan adam tara yake bai cika goma ba rukayya wani irin wulakanci da cin mutunci ne safiyya batamin ba, amma albarkacinki bana taba nuna mata damuwata ba wai yau an wayi gari dan wani abu ya faru bisa kaddara ki.......' kan ya karasa ta tari numfashinsa.
🅰bbagana hausa novels @ faceebook.
[10/20, 7:57 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
5⃣2⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
09039016969
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
Tun kan ka aureni na gaya maka halin yata ka kuma yarda ka auren da yata alkhairi kuma kai kayi niyya kai mana tunda nake banta ba tambayarka wani abu ba, dan haka ka bar tunanin kayi mana wani alkairi da kai mun, in kuma safiyya kake tunani kawai alkhairi ka mance cikin sharadun aurena da kayi ta gaya maka duk abinda take so zaka yi mata ka kuka yarda in koh har yanxu wannan sharadin yana nan to duk abinda kayi mata kayine cikin sharadinku dan haka babu wani alhairi da kai mata sai sharudin da yake tsakaninku, mahaifiyarka da danka da kuma mahaifiyata kunyi min babban SANADI kuma rabani da farin cikin zuciyata ta tafi da kiyayyata a zuciyarta nasan halin nana koda zan gaya mata gaskiya ba zata taba yarda ba, duk lokacin da naga fuskarka sai na tuna nana dan haka dan Allah ka taimakamin ka daina zuwa wajena."
Naji rukayya kuma na miki alkawarin har abada ba zan kara zuwa wajenki ba, ba tare da kemeni ba duk kuma nauyin da ubangiji ya dauramin zanyi kokarin saukewa mallam ne ya ban ke dan haka zan dinga komai ta hannun mallam kar kuma ki mance da abu daya har abada ba zan taba zama SANADIN batan safiyya ba Allah yasan zuciyata na rike safiyya kamar yadda nake rike yayana.
Har abada ba zan taba cire cikin wadanda sukayi min SANADIN batan nana ba tana fadar haka ta bude motar ta fita.
File taje ta bude bayan ta gama komai taje tabi layin wadanda za'ayi wa awo tunda ta zauna babu abinda take sai tunani, ji tayi an mata sallama tayi saurin dagowa sannu mama" wata yarinya ce ta fada wadda ba zata gaza shekarun nana ba nace yauwa sannu yata tun dazun ake kiran sunanki nayi saurin tashi wani dakin zan shiga? Ai sun gama sun zaya bakya nab nayi saurin dafe kai yata yanzu bazasu taimaka suyi minba tana murmushi tace karki damu bari na yiwa babban magana sai ta dubaki to na gode ta tafi tana waigena kamar zan gudu abin ya ban mamaki ba tafi minti biyu ba ta dawo.
Mama ki shigo ta dubaki tace dani, muna shiga naga matar ta cire glass din idonta wanda da alama na kara karfin ganine ta hau girgiza kai har na karasa wajenta tana kallona ikon Allah ta furta yarinyarce ta dawo dani daga tunanin da nake momy kinga dan Allah basu kama?? Humm aysha kama sosai kamar an tsaga kara ta juyo wajena kece rukayya nasir?? Na amsa mata, meyasa tun dazun ana kiran sunanki baki amsa ba? Hajiya banji bane tana murmushi tace kina dai tunani shine yasa bakiji ba me yake damunki har akayi ta kiran sunanki bakiji ba , shawara zan baki kina da juna biyu ki rage tunani dan lafiyarki da ta yayanki yawan tunani zai iya kawo miki matsala da kuma barazana a rayuwarki kanwata komaii yayi zafi ki kai kukanki ga ubangiji wanda na tabbata zai amsa miki...........
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Wednesday, 26 October 2016
Popular Posts
-
Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin “Abba...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 76 BY MIEMIEBEE Hannunsu ta had’a tana murzawa a hankali, “I’m ready Habeebi.” Har yanzu ya kasa yarda, “Flower are...
-
TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 56 BY MIEMIEBEE Wani irin tausayin daya jima be mata irinsa ba ya soma jimata yau, azabarcaccen k...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 89 BY MIEMIEBEE Daidai tashiwan Anas daga bacci kenan, da k’yar ya iya ya raba jikin Fannah da nasa dan wani s...
-
[9:09PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 1 na BABY ZAHRA Kayatatciyar daki ne mai dauke da ko mai na more rayuwa, alarm ce ke bu...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 74 BY MIEMIEBEE D’ayan hannunsa ya aza a hab’arta tare da d’ago fuskartata. “Flower you don’t have to be sorry baki...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 68 BY MIEMIEBEE Kasa koda amsashi tayi wani kunya taji ya rufeta, she can’t believe abinda ta aikata sede kuma ...
-
TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 61 BY MIEMIEBEE ★‡★‡★‡ PRISON HOUSE MAIDUGURI, BORNO STATE. K’aramin gate ne ya bud’u...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 75 BY MIEMIEBEE Sede still bayason miyan kukan yafison ire-iren abincin daya saba ci a London su burger, pizza, buf...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 01 BY MIEMIEBEE ANAS K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno. Da yammacin ranan Asab...
About Me
- Muhammad Abba Gana
- Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
Blog Archive
-
▼
2016
(217)
-
▼
October
(27)
- Waye sanadi? 51&52
- waye sanadi? 46---50
- waye sanadi? 41---45
- TANA TARE DANI (end)
- TANA TARE DANI 98
- TANA TARE DANI 97
- PHERTY 1___END
- WAYE SANADI?? 36___41
- hy
- WAYE SANADI?? 30___35
- WAYE SANADI?? 21____29
- WAYE SANADI?? 17___20
- WAYE SANACI?? 15&16
- WAYE SANADI?? 13&14
- WAYE SANADI?? 11&12
- WAYE SANADI? 8-9 & 10
- WAYE SANADI? 5-6 & 7
- WAYE SANADI? 4
- WAYE SANADI? 3
- WAYE SANADI? 2
- Shafin hausa novels Na Bankwana Da MyWapBlog
- hy
- wow
- WAYE SANADI? 31---35
- TANA TARE DA NI... PAGE 95&96
- TANA TARE DA NI... PAGE 93&94
- TANA TARE DA NI... PAGE 91&92
-
▼
October
(27)
Sassa
- AMINAN JUNA
- BANA KAUNARKA HAUSA NOVEL
- DAN ALHAJI HAUSA NOVEL
- DILKA & HALWA
- DOMIN KE DA MIJINKI
- GUZIRI MAFI KYAWU
- HAUSA NOVELS
- INSIYA
- KAUNA CE SILA HAUSA NOVEL
- KUKAN KURCIYA
- MU DAUKI DARASI
- mu koyi sana'a
- MY kitchen
- NA DAINA SO HAUSA NOVEL
- RAYUWAN NIHILA
- rayuwar fauziya hausa novel
- SASHIN YAN UWA MATA
- siffofin uwa
- TSORATARWA.
- WAYE SANADI
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.