[9:24PM, 5/10/2016] Ábbā-Gãñå WAYE SANADI?
11
)MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
haba nana Allah ya tsareki da iskanci,fatana Allah
ya tsareki ya rabaki da dukkan mai sharri bara na
baki dubu goma ki rike a hannunki ranar sai karfe
takwas suka tafi suka kaita lokacin bana gidan
karfe goma da rabi na dawo gidan kaka na tarar
a zaune a soro "ina kika je tun dazu nake jiranki
zan rufe kofata inda kika aiken wajen naje
uwata,ai da kin sani kin rufe wallahi da sai na
karya kofar kuma na tara miki mutane wani
azababban mari ta sakar wanda ya sani yin shiru
"shegiya mara kunya wadda bata neman albarka
bankadaddiya ki kara gayan magana ta mai da
kofar ta rufe ta biyo ni tana bambami ina zuwa
na nufi kicin wata sungumemiyar tabarya na
dauko n shigo dakin ina dai kin isa dan girman
Allah ki kara marina sai in balla miki kai dan
kinga ina rabuwa dake bafa tsoronki nake ba,ki
kara marina ki gani ina magana ina tura mata
fuskata ki mare ni mana ido kawai ta zuban
jikinta yana rawa,na saki murmushi "mutum sai
tsoron tsiya wallahi yau mu biyu ne ki mun ki ga
karyar rashin kunya dama ina ragonta miki dan
darajar ummata,to dan Allah yanzu kimin abin da
kike min ki gani koh zan rabu dake,wallahi zan
yanka ki matsa malama ki ban waje na karasa na
kwanta jakata na bude 2 miss call mamaki ne ya
kamani ganin har miss call two ni dai nasan bbu
wanda yasan number ta duka duka yau kwana
uku dasa layin abin ya kara bani mamaki da naga
number wata iri dagani lambar wata kasarce sai
kuwa naga text message abin da nagani "my
momy lafiya nayi ta kewar momina na kira kuma
anki dauka please momy a dau wayata. tsaki naja
ji wani wahalallen wayar na kashe na jawo
littafina ina dubawa.washe gari bbu wanda ya
kula wani tsakani da babs nayi wanka na shirya
ina jiran lokacin makaranta yayi na fice na jawo
jakata na dauko waya na kunna ban fi minti uku
da kunnawa ba naji kira number jiya ce a zuciyata
nace bara dan na okey wata ajiyar zuciya naji an
saki.uhum my momi laifi nayi akai min wannan
hukuncin naji wata daddadar murya ta furta
momy ki min magana please ko naji dadi " cikin
tsawa nace mallam wrong number ka kira kan
yayi magana na katse wayar na mayar jaka ina
mita na mike na fita ina fita titi na samu
adaidaita sahu,bayan na sauka ina tsallaka na
shiga ina cikin tafiya naji magana daga bayana
sannu ko nayi saurin juyowa ina kallonta ganin
yar uwata ce mace yasa na saki fuska tana zuwa
sannu tana murmushinta mikon hannu tace jiya
kece aka kawo ki class dinmu koh? ke yar ajince?
eh ai tun da aka sauke ki a adaidaita sahu na
keta miki magana baki ji ba."
12
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
kawai naji ta kwanta mina tare muke har muka
karasa class din daga baya muka zauna.baki
gayan sunan ki ba ta tambayeni tana murmushi
oh am sorry,nana safiyya mukhtar nake,kuma
gaskiya sunan nice name ni kuma sadiya adam
nake da fatan zamu zama kawaye kuma mu
zauna da juna tsakani da Allah ina murmushi
nace na gode da zabata da ki kayi a matsayin
kawa kuma insha Allahu zaki same ni kawa ta
gari mai kuma......' malami ne ya shigo dan haka
mukai shuru bayan ya gama ya fita na juya ina
kallon sadiya kawata.kai karatun jami'a akwai
wuya musamman ma course dinmu,kai nana ai
irinku karatu bazai muku wiya ba saboda me
kikace baya mana wuya? nana kin ban mamaki
sosai banyi zaton ki haka ba sai naga kin fi haka"
kin fa sani a duhu kai kawata kamar ba kya jin
hausa.Allah ban zata kina da kokari ba okey
zagina zaki bbu batun zagi sai......"waya tace
tayi kara na zaro ta a jaka number jiya naga naja
tsaki na katse.a'a kawata sweety ne yayi laifi aka
ki daga wayarsa na gwalo ido nace waye kuma
seweety Allah ya kiyaye dariya tayi sosai."amma
kawata ba zaki gayan gaskiya ba duka duka yau
muka hadu,dan haka ake boyan mai tsadar to ni
dai shawarar da zan baki karki tsaya jan aji har
ajin yazo ya tsinke dan yanzu mu muke da tsada
muka ji ance daga bayanmu muka yi saurin
juyawa.sadiya ta washe baki tana murmushi
yayin da ni kuma na hada fuska ina harararsa.kai
mun zuwan bazata saukar yaushe tun dare na
sauka kina barci kuma yanzu zan wuce kai yaya
dan Allah daga zuwanka,to ka zo ka zauna""ta
juya tana kallona lokacin na mai da hankalina kan
littafina "nana ga yaya na na daga fuskata ba
yabo ba fallasa sannu ya gida? lafiya kawarmu ya
karatu? na mike sadiya bara na shiga class okey
kawata sai na shigo kan na karasa wayata ta
soma kara karo na biyu a fusace na dago wai kai
mallam ba nace maka wrong number kakira bane
kake ta damuna please sister ki daure ki sauraran
"kaga mallam kaje can ka nemi yar uwarka karka
kara kiran wayata kayi magana"
abbagana hausa novels@ facebook.
WAYE SANADI?? 11&12
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.