WAYE SANADI?
17
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
taso muje ki rakani gurin ummanki oh mama ita
ma yanxu ta tahi daga nan zo muje dakin daddy
kinga shima saiku gaisa ta mike ta jawo hannuna
muka nufi wani barin daban shima waje ne mai
kyau yana zaune kan kapet ummansu tana hada
masa tea yana ganina ya hau murmushi safiyya
har kin yi shirin makaranta banyi magana ba har
muka karasa gabansa nace antashi lafiya lafiya
klau ya kan naji sauki yanzu dakyar na danne
zuciyata nace mata sannu da aiki sannan ta dago
fuskarta a daure ta dago kai ke za'a yiwa sannu
ta mai da kanta taci gaba da juya shayi yadda
fuskar maryam da na daddynta sun nuna basu ji
dadi ba, a zuciya ta nace kar ma ki damu ni da
kaina zan yi maganinki duk abinda ta taka nima
shina taka na mike zan tafi makaranta. to safiyya
ungo ki hau mota nasa a nemo miki direban da
zai dinga kai ki da dauko ki tunda muka zauna
zanyi break maryam dasu abba suke ta jana da
hira ban basu wani cikakkiyar amsa ba daga E
sai a'a na mike zan tafi abba ya mike nana bara
na karbo key na kaiki ba dan naso ba na amsa
masa da toh tunda muka tafi yake ta jana da hira
ina kokarin kauce amsa dan dukansu haushinsu
nake ji "nana safiyya tunanin me kikeyi? ina ta
magana kinyi shiru,bbu tunanin da nake kawai dai
maganar ce bana sonyi kamar ance juya naga
sadiya a tsaye a titi ka sauke ni anan ga kawata
can sai kawai mu karasa haba ya za a yi na bar
kanwata a nan bari ita ma na dauke ta sai na
kaiku tana ganin mota ta tsaya a gabanta ta
dauke kai daga wajen ganin an bude yasa ta fara
tafiya ina kuma zaki? jin murya ta yasa ta
juyowa lalala safy kece daman kinga lokacin yana
tafiya kizo mu karasa school ta shiga baya,sannu
ina kwana lafiya klau ya karatu? har muka karasa
bbu wanda ya kara magana yayi parking sadiya
ta fita har na yunkura zan fita naji maganar abba
sufy sunan ya min dadi sosai gashi kya yi break
ka barshi daddynku ya ban nasan ya isheni kan
yayi magana na fice banko tsaya ba rufe masa
murfin ba na karasa wajen sadiya. sufy daman
shine darling din amma gaskiya kun dace ya
sunansa? Allah ke wani lokaci dariya kike ban
kawai daga kinga mutum sai wani surutu kike
nifa duka yau na fara ganinsa kuma wallahi
haushinsa nake ji kamar na kashe shi dama
daurewa kikai kenen 'daina yi min tadin shi"
Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?
18
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
gaskiya sufy baki da mutunci to me yasa kika
shiga motarsa har ma kuma ya akai ya
sanki,kinga bara nayi miki a takaice wannan aban
dan mijin ummatane,dan ni bana kaunar
maganarsa nakeba,kai suffy Allah ya gyara miki
na zaro waya ta kira na gani har guda uku sai
kuma message daya zuciyata ta kasa samun
nutsuwa hankalina ya kasa tattatuwa waje daya
har sai da naji muryar yarinya kin tashi lafiya?
kiransa ne ya shigo ban karasa karantawa ba
nayi saurin dagawa cikin hargagi nace wai kai
baka da hankali kana kiran matar aure banza.na
kashe waya uhum wallahi nana kibi a hankali ba
ayi wa namiji haka"na juyo ina hararanta ke kin
cika abin haushi goya mazan zanyi bara kiji ni a
tsarina dana kula namiji gara na zauna ban
magana da kowa ba saboda me? kai tsaye na
bata amsa saboda bana kaunarsu meye dalilinki?
sadiya ni kaina ba zan iya kawo miki dalili ba illa
dai kullum zuciyata tana gayan namiji bai da wani
buri na gari akan mata shi dai burinsa daya ya
cuceki ya gudu ya barki tsanata ta dada karfi
akan namiji tuna na karanta wani littafi "yaya
sunansa littafi kuwa waye yayi shi? sabon
marubucine, sunan littafin NA DAINA SO wallahi
sadiya naji na tsani duk wani na miji na tsane shi
to an ce miki duka mazan halinsu dayane duk
abin da zaki ji a littafi karya ne kawai dan a
fadakar ni kam ban yarda da abinda na ke gani a
littafi ba.wai wayene yayi? ina jin sunansa muhd
abba"to kinga ni duk cikin marubuta bbu wanda
nake jin dadin littafinta irin "hauwa jabo"
labarinta yana burgeni jiya sai dana karanta
sabon littafinta mai suna"hasken idaniya" yayi
dadi sosai kuma dana koma zan sa a nemo min
wannan din ya sunansa"NA DAINA SO. muna
shiga class na dauko wayata zan kashe naga
wani message nana jiki na yana gayan baki da
aure ki daure muyi magana ta nutsuwa imran S.
gabanane yayi mummunar bugawa waye wannan
yasan sunana na shiga tambayar kaina na shiga
uku kaddai ace aljani ne. lafiyarki kuwa kina
ganin malami ya shigo nayi saurin kashe wayar
na jefa cikin jaka tun dana koma gidan alhaji
nasir naji rayuwata ta sauya kamar lokacin na
fara rayuwa nayi kyau sosai lokacin na san ina da
kyau gaskiya sai yanzu na san ina rayuwa me
kyau kayya kam har bana iya irgawa ni da
ummata duk abinda muka bukata alhaji nasir
yana yi mana daidai da rana daya bai taba nuna
gazawarsa ba,
Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?
19
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
tsakani na da matarsa da yarsa bbu mai shiga
harkar wani tunda muka yi fada da maryam
shikenan babarta ta kafan kagon zuka nima bana
rangawanta mata umma bata taba cemin na bari
ba shima maganarsa daya nayi hakuri. yau ban
shiga school ba misalin karfe sha biyu na tashi na
shiga dakin alhaji nasir yana jin bbc maryam tana
zaune a kusa dashi ban koh yi sallama ba na
shiga na zauna a kan kujera kusa dashi na juya
ina kallon fuskar maryam harara ta zabga min
nayi mata murmushi na juya ina kallonsa sannu
da aiki abinda bai taba jin nayi masa ba cikin
mamaki ya amsan yana tambayata ko da wata
matsalar ce maka zanyi ina son zan shiga
islamiyya shine nake so ka yankan form kuma
yanzu naiya mota da kaina ina so ka sai min
mota mai kyau ta zamani. safiyya duka kwananki
nawa kina koyar motar? wannan ba damuwarka
bace ni dai nace ina bukatar mota shikenan
safiyya zan siya miki sannan maganar islamiyyar
kin taba yin wata koko a nan xaki fara? tun muna
fanshekara har muka koma dorayi ko lokacin da
na daina zuwa izina arba'in. shikenan safiyya in
yamma tayi zan je sai na yanka miki form din.
haba daddy yanzu har agola tafi mu daraja tazo
maka da bukata bbu ladabi sai magan ganu kai
tsaye ta zo ta zauna kusa da kai abinda ko
momy ba tayi maka haka amma ita sabida ba ta
da tarbiyya ta zo ta zauna kusa da kai, sannan
dady nafi shekara ina cewa ka sai min mota
amma baka sai min ba ko su yaya da abba ma
baka sai musu ba sai tsohuwar taka ka basu
amma ita tana tambaya har ka amsa mata
wallahi ba zaki hau motar ba tunda ba
uban.........kan ta karasa ya sakar mata mari
daman baki da kunya safiya ba gaba dake take
ba tashi ki bar min daki mara kunyar banza fita
tayi tana rusa ihu juyowa yayi yana kallona
safiyya kiyi hakuri insha Allahu gobe zan shigo
miki da motarki wai ina wayarki ne ban taba
ganinki da ita ba tana nan kawai dai na ajeta
saboda karatu okey na mike ina zuwa daidai
kofar fita naji an zabgamin mari ina dagowa banyi
wata wata ba na zabge mata mari har sau biyu
kururuwa ta saka da sauri ummata fito tana
tambayarta lafiya zakice lafiya mana munafuka
bada daurin gindinki take komai ba to wallahi
bazan yarda ba agola ta dagar hannu ta mare ni
har sau biyu ta juyo kan ummana nayi saurin
shan gabanta ni nayi miki ba ita ba dan haka
karki kuskura ki taban umma in ki kace zaki taban
umma kina ganin zan rabu dake to gata nan ki
taba ta batun yau nake ganin ta kun ku ke da
yarki wallahi in din gudace banza jaka me kishi
akan namiji.
Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?
20
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
naja hannun ummata mukayi daki wallahi alhaji
kayi kadan ka wulakantani a gabanka yar
matarka ta maren har sau biyu baka yi magana
ba kuma a kanta ka mari yarka to wallahi bazan
zauna ba gara na tafi in kina ganin tafiyar ta fiye
miki alkairi to sai kin dawo in kuma zaki iya
tsayawa ki sauraran to, yana fadar haka ya juya
yayi daki tunda muka shiga daki nida umma
zaune take tayi tagumi umma tun dazun na
tambayeki kinyi shiru ko dan nayi fada da
kishiyarki kike jin haushina' nana ba haushinki
nake jiba jikina kaka nake tunani tun shekaranjiya
take kwance ya kamata kije ki dubata nana tunda
kika dawo gidan nan kusan wata tara kenan baki
taba zuwa kun gaisa ba ya kamata ki jeki ga ya
jikin nata yake. wallahi umma bbu inda zani
kawai kina so kice na bar gidan mijinki saboda
yana da kudi bakya so na zauna naci arziki kuma
yau zan bar.gidan "na mike na shiga dakina bata
koce min kala ba na shiga hada kayana har na
gama na dau jakata na ganshi a tsaye, safiyya
mayar da kayanki kiyi hakuri kuma gobe in zaki
makaranta ki biya ki gaida baba karki min
gardama Allah yayi miki albarka ya juya ya fita
kawai naji yau yaban tausayi dan haka na juya na
mayar da kayana bayan kwana uku ina zaune a
falon umma ina kallo ya shigo ko kallonsa banyi
ba umma ta fito tana yi masa sannu da zuwa,na
mike zan shiga daki naji muryarsa safiyya ga
alkawarinki da nayi miki na juya ina kallonsa
wane alkawari na fada ina hararansa, motarki an
kawo ga key din kuma naje islamiyya na yanka
miki form har an cike gobe zaki fara zuwa. hannu
nasa na karba nayi cikin daki umma ta juya tana
kallonsa an gode Allah ya kara arziki. amin
rukayya na gode da addu'arki na kuma ina adduar
Allah ya barmu tare har karshen rayuwarmu keh
har gidan aljanna. murmushi tayi ta sunkuyar da
kai ya mike ki mikon abincina.
ni kam tunda na shiga daki nake tikar rawa yau
nice nake da mota sabuwar rayuwa tazo yaya
sadiya zatayi in ta ganni da mota Allah Allah
nake gari ya waye na tafi school. umma ce ta
turo kofar ta shiga tana hararata sannu mara
kunya 'umma me kuma nayi? ban sani ba wallahi
nana in baki canja wannan mugun halin naki ba
bazaki taba jin dadin rayuwarki ba ace mijin
mamanki ya zama makiyinki mutumin nan
burinsa ya kyautata miki amma dai dai da rana
daya baki taba masa godiya ba, tsakaninki da shi
sai harara kamar sa'anki."
Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?? 17___20
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.