shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 4 October 2016

TANA TARE DA NI... PAGE 95&96

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI... PAGE 95 BY MIEMIEBEE “A yinin ranan da nabar gidan Ya Ibraheem nabar yarana abin muradina Anas da Shettima badan komai ba sedan bak’in talaucin daya addabemu sau dayawa muna tashi ba abinchi bayan gashi a waje Alhajin Yola ya nuna yana sona yana kashe min kud’i ba tare da na kawo wani tunani a raina ba na tattara kayakina nabar gidan Ya Ibraheem dukda erin kuka da roqana dasu Anas suka rik’ayi hakan be hanani tafiya ba saboda alokacin kwad’ayi ya riga ya rufemin ido”. “Bayan nabi Alhajin Yola yawuce danu Yola a ranan inda muka sauk’a awani had’ad’d’en hotel, seperate d’aki yakama mana acewarsa bamuyi aure ba tukuna be dace mu had’a d’aki ba washegari ya tinkareni ya fad’amin abinda ke zuciyarsa na aurena dayakeson yi dukda nasan haramun ne aure akan aure hakan be hanani amincewa da k’udirinsa ba, achan Yola aka d’aura mana aure acikin sati yamana processing visa inda muka wuce tsarkacacciyar k’asa Saudi yin honey moon sede wani gudu ba hanzari ba tun isar mu chan nake fama da zazzab’i, zuwan mu asibiti aka tabbatar mana juna biyu ne d’auke dani cikin Amal kenan, barin b’oye muku amman a lokacin cewa ma nayi azubar da cikin kasancewar chan gari ne me tsarki basu aikata haramun aka k’i biya min buk’ata koda muka dawo gida hankalina a tashe yake tsoro na kar Alhajin Yola yace ya fasa zama dani tunda na taho masa da cikin wani gidansa, alokacin banida wata burin data fi in kasance dashi saboda yadda yake kashe min kud’i. Shi ya kwantar min da hankali yakuma tabbatar min da cewa in kwantar da hankalina inyi rainon cikin kar na zubar yaso in na haife se na dawo muku da abunku, without a second thought na amince da hakan, haka nata rainon cikin Amal daya bani wuya har fiye da na Anas cikin fari dalilin haka yasa natsani abinda ke cikin ko ante-natal d’ina ba regularly nake zuwa ba fata na Allah rabani da abinda ke cikin nawa lafiya.” “Munyi tsawon watanni 7 a Saudi ba tare da mun samu sab’ani da Alhajlin Yola ba tarerayata yake kamar ‘yar baby abinda nakeso shi yakemin alokaci d’aya na mulmule tunda nafita daga first trimester. A wannan watan ne muka dawo Nigeria inda muka sauk’a a Maiduguri nacigaba da rainon cikina dana tsanesa fiye da mutuwa, kwatsam da daren wata rana nak’uda ya taho min wanda nad’au mutuwa zanyi bayan kusan awa shida danayi a labour room nasamu Amal ko k’are mata kallo banyi ba, in tambayi nurse d’in mace ce ko na miji ma banba saboda jin dad’in da nake na rabani da ita ko shi da Allah yayi, naso barin ta ta kwana a asibiti amman sunka k’i dole na taho da ita gida anan ne na gano mace ce na haifa duk erin kukan da Amal take a lokacin dan yunwa besa na shayar da ita ba yaron dake mana d’an hidima ne yabata ruwa ta rik’a sha kafin garin Allah ya waye Alhajin Yola yasa sa a mota da Amal tare da letter dana rubuta aka kawo muku ita”. d’ago kai tayi ta kalli Amal dake ta kuka jikin Anas kamar ba gobe taji ta k’ara tsanan kanta na wulaqanta wannan kyauta da Allah yayi mata. “Se a wannan lokaci nakai Alhajin Yola gun iyayena basu ko damu taya nayi auren ba tambayar da suka min d’aya ne shin yanada kud’i? siyayyan da Alhajin Yola ya musu ne yazame masu amsa, k’arya namusu nace ka saken ne Ya Ibraheem shiyasa na sake aure, please kayi hak’uri ka yafemin na sharrin dana maka”... “Ko kad’an baki min sharri ba Aysha saboda aranan da kikayi stepping foot kika bar gidana a ranan na miki saki d’aya saboda nasan duk inda zakije aure zakiyi nikuma ina sonki barin iya jure fushin Allah akanki ba shiyasa na sauwak’e miki kinga ko bakiyi aure akan aure ba.” wani sabon kukan ya sake rufe Ummimi she can’t ever forgive herself. “Tabbas babu kaman ka acikin mazaje Ya Ibraheem nagode k’warai Allah yima sakayya. “Daga nan muka wuce New York kamar yadda yamin alk’awari, rayuwa bata tab’amin dad’i kamar a wannan lokaci ba sede abin mamaki koda na tambayi Alhajin Yola wani aiki yake seyace min he is self employed niko da dama kud’insa ne ya damen ban kawo wani abu a raina ba haka muka d’au tsawon shekara muna soyayya dashi ba tare da mun samu wani matsala ba iyayena kuwa kullum yana cikin musu alkhairi daban daban a shekara na biyu da aurenmu ne nasamu cikin Barrah da Basmah wanda suka kasance twins kyawawa wane Amal shekarunsu uku nasamu Yusuf wanda yake sak Anas shi kuma, harta blue eyes nasu iri d’aya” ta d’ago kai tana kallon Anas da take ya kawar da kallonsa daga gareta, hawayen ta ta share sannan ta cigaba; “Alhajin Yola ya kasance yana matuqar son ‘ya‘yansa becika tsawata masu ba koda sunyi laifi ne, haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jin dad’i alokaci kad’an ne nake tunawa dasu Anas da Shettima amman kuwa in na tuna da talaucin daya fitini gidan Ya Ibraheem sema inji na tsanesu tun daga kan Yusuf haihuwa ya tsaya min. Su Barrah suna da 12 years aduniya nasoma fuskantan chanji daga mahaifinsu mutumin da baida magana baida masifa yamiyar da masifa abinyi abu kad’an kayi seya tsigale ka, akwai lokacinda har mari na yayi saboda yana ma Yusuf fad’a nashiga toh tun daga wannan lokaci ban sake gane kan mahaifinsu ba, yadena sonmu kullum cikin k’untata mana yake school fees na makaranta ma seya ga dama yake biya musu nayi nayi ya gayamin inhar laifi na masa ya fad’a mani in basa hak’uri amman ina inya watsa min wani mugun kallo ni dakaina nake tashi masa agun a 13th birthday’n su Barrah yayi suprising namu duka, birthday cakes biyu ya siyo musu mukayi celebrating birthday nasu washegari yasa duka yaran cikin mota cewa ze kaisu park su shaqata yatambayeni ko zani nace mai a’a bansani ba ashe wannan rana shine rana na k’arshe da zan sake sa yara na a idanu na ba. Kuka ne yafi k’arfinta hankalin kowa ya tashi wajen banda Anas, duk sun k’osa suji meya faru, Ummie da Fannah ne ke bata hak’uri. Picture’n taciro ta miqa ma Ummie “yau watanni bakwai kenan da rasuwansu.” Salati kukeji a d’akin bayan Ummie tagani ta miqa wa Abuu se Shettima lastly Amal then back to Ummimi again, anan duk sukayi mata ta’aziya shima Anas badan yanaso ba yayi mata. “Tun safe ya fita min da yara har La’asr basu dawo ba kodana kira wayansa kuwa har ta tsinke be d’aga ba wayoyin su Barrah kuwa switched off yake cemin, anan fa hankalina ya tashi daman tun tafiyarsu nake ji ajikina something bad will happen to them nakasa zama gu d’aya fatana Allah dawo min dasu lafiya se bayan Isha’i naji k’aran bud’ewan gate a guje na fita waje bayan yayi parking na tsaya gun ina jiran fitowan farin cikina yara na, sede basu ba alamansu, mahaifinsu kad’ai nagani cike da tashin hankali na tambayesa ina yaran suke kallo na yayi a raunane sannan yace min wai an sacesu, bansan a lokacin dana sume wajen ba next abinda nasani shine gani na danayi kwance akan gadon asibiti se a washegari muka dawo gida ba kalan tambayan duniyan da banma Alhaji Isma’il ba ya fad’amin ina ‘ya‘yana, amsar nasa d’aya ne an sacesu jiya a park cike da tashin hankali na d’ago mayafina zan kai report station ganin haka munafikin ya dakatar dani yamin qaryan wai tun jiya yakai report yanzu haka police sunakan investigation haka har wani sati ya zagayo ba labarin yarana, ban sake sanin meke min dad’i ba akullum ina sa ran za’a samu su Barrah amman inaa adaren wata rana na fito daga d’akina zan wuce dining space dan shan ruwa naji Alhaji Isma’il akan waya har na wuce se wani abu ya dawo dani baya nakasa kunne ina sauraron meyake fad’i a wayan. Hankalina ya matuqar tashi jin da bakinsa yake fad’in “ran yara na uku dana baku be isheku ba yanzu na mata ta kukeso?” Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un” “Mutuwan tsaye nayi a wajen totally speechless ban hankara ba naga Alhaji tsaye a gabana fuska nakad’ai ya zame masa amsa ga tambayan daya s min. Ina kuka na mai maganar, “Alhaji? Dagaske ne?” Na tambayesa. Kame kame yasoma bansan a lokacin dana fara kai masa bugi ba, ba kalan zagin da ban masa ba a daren nace zan kai k’aransa station nan ya kukkule duka k’ofofin gidan da dambe da fad’a yakaini wani d’aki ya rufeni, ina jinsa yayi waya da d’aya daga cikin ‘yan k’ungiyan nasu yana cemai ya yarda ze sihar dani nima acewarsa tunda nasan sirrinsa yanzu ba amfani na again, ba waya akusani dani koda akwai ma bansan wa zan kira ba kwana nayi ina Sallah Allah ya kub’utar dani daga sharrin sa, washegari nasome neman abinda ze taimaka min in b’alla lock na k’ofan, da cokalin da nasamu na b’ab’alle screws d’in k’ofan na fito a lokacin bayi gida yafita, kayaki kad’an na d’auko da sauran essential things da zan buk’ata, na nemi wayana sama da k’asa na rasa, a gurguje nabar gidan nakai report police station ko ya akayi maganan yaje kunnensa oho next abinda naji shine wai yagudu yabar k’asan kwata kwata tun daga wannan rana ban sake sa shi a idanu na ba 3 months ago na ganshi awani super market tundaga wannan lokaci na shiga b’uya saboda nasan aduk lokacin da ya ganni tabbas nima siyar danayi zeyi, aiki na samu awani restaurant as a cleaner dashi na dogara har izuwa lokacin dana had’u da Anas da Fannah, kunji takaicaccen labari na.” Tausayinta ne yakama kowa a d’akin harta Anas, seda Ummie ta zubar da hawaye. “A gaskia kinsha gwagwarmaya a rayuwanki Aysha ba abinda zamuce se Allah ya kare aukuwan na gaba ya tsaremu daga sharrin mutane da aljanu gabad’aya...” dadda’d’un kalamu Ummie tariga gaya wa Ummimi shi kansa Abuu ya mugun tausaya mata yasani alhak’in sune yakama ta tunda har a duniya taga sakayya yaci ace sun yafe mata suma. “Aysha ni na yafe miki na yafe miki har abada abinda ya faru dake kuma Allah takaita” cewar Abuu. “Ya Ibraheem nagode, Allah ya saka da alkhairi, Shettima, Shettima dan Allah ka yafemin abinda na maka.” Shiru yayi bece komai ba ba irin rok’an da bata mai ba seya bud’e baki zece ya yafe mata seya kasa haka ta dawo kan Amal ma duk ba wanda ya iya ya yafe mata Anas kam ba magana Abuu be sa baki ba saboda yasan ba’a shiga tsakanin uwa da yara yasani with time duk zasu yafe mata. * Abuu ne tsaye da Ummie a dining ayayinda Ummimi ke zaune da Fannah a parlour su kad’ai Anas da qannensa duka sunyi d’aki. “Ya Ibraheem yanzu ya zakayi da Aysha?” “Ni kaina bansani ba Nafeesa, bansan me zanyi da ita ba.” “Agani na mubarta ta zauna damu anan tunda ba inda zata iya zuwa batada kowa banda mu.” “Me kike nufi Nafeesa?” “Ina nufin ka dawo da ita d’akinta ai akwai aure a tsakaninku.” “Barin iya dawowa da Aysha ba ina sonta amman barin iya dawo da ita ba.” “Zaka iya Ya Ibraheem kayi hak’uri mukoma parlon.” Bayan sun dawo suka zauna Ummie tayi gyaran murya “Aysha kinje kinga iyayenki kuwa?” “Banje ba tukuna bansani ko iyayen nawa ma suna raye ba.” “Kinada masauk’i yanzu?” “Banida Nafeesa.” “Toh yanzu wani mataki kika d’aukar?” “Ba abinda nakeso kaman in kasance da ‘ya‘yana Ya Ibraheem dan Allah kayi hak’uri ka dawo dani d’aki na badan halina ba dan Allah.” “Aysha na soki kuma zan cigaba da sonki amman ban tsammanin zan iya dawo dake.” “Ya Ibraheem please karka min haka dan Allah karka hanani daman kasancewa da yarana again nayi kuskure amman wallahi na tuba barin sake aikata abinda nayi da a baya ba, ka taimaka please” “Aysha kiyi hak’uri amman barin iya dawo dake ba” yana kaiwa nan ya miqe. Hak’uri sosai su Fannah suka rik’a bata. Da k’yar Ummie ta samu tayi convincing Abuu ya yarda aka bawa Ummimi d’aki d’aya a gidan Anas najin haka yasa Amal ta had’a akwatinta suka koma gida tare yasan muddin Amal tacigaba da zama da Ummimi toh eventually Amal zata yafe mata abinda baiso kenan. ** Tun isar su Fannah gida bata ma Anas magana ba a d’akinta Amal ta sauqa daidai da Azahar Anas yatura Amal dataje ta kira Fannah suyi Sallah a d’akin Hanan ta tarar da ita bayan tayi sallama tace, “Ya Fannah wai kifio muyi Sallah inji Ya Anas.” “Kice masa yajaku ku biyu zanyi nawa da kaina” da “toh” Amal taje ta isar wa Anas da saqon Fannah, daman yau yasan da akwai drama shida kansa ya miqe yaje yasamu Fannar, agefenta ya zauna “Flower tashi muje muyi Sallah.” “Bakaji meh Amal tace maka bane? Nace kajaku zanyi nawa ni kad’ai.” “Mesa toh?” kafin yakai hannunsa kan cikinta taja da baya. “Mara na namin ciwo se anjima zanyi.” “Toh zamu jiraki.” “Ni ina ma ace yadda kakemin haka kake ma Ummimi wallahi Habeebi ko kad’an banji dad’in abinda kama Ummimi ba yau, uwa uwa ce fa you are not being just inhar kai baraka yafe mata ba then don’t drag Amal into it, I know ba tsakani da Allah kasa Amal had’a akwati ta biyomu ba gudun kar ka barta achan eventually tayi forgiving Ummimi ne koba haka ba?” “Ke kikaji wajen zaki tashi muyi Sallah ne kokuwa?” “Bansani ba nima” tana kaiwa nan tabar masa d’akin binta yayi da kallo yana cizen lips nasa, d’akinsa takoma haka tak’i binsu Sallah ita kad’anta tayi nata bayan nan suka soma jin yunwa sarai zata iya musu girki tace barata iya ba Amal ‘yar gata kam dama ba abinda ta iya yi koda Anas yace ze musu girkin Fannah ta b’ullo da dabara tace ita yau tuwo takeson chi tasan sarai ba iyawa yayi ba. “Flower tuwo kuma yau?” “Eh tuwo nakeso.” “Toh Mom Hanan Amal jeki d’au mayafinki muje musiyo mata.” “A’a Amal is staying with me akwai aikin danakeson ta tayani bayan tafiyan mu cleaners d’in ba kullum suke zuwa aiki ba d’akina duk yayi k’ura zamuyi dusting.” “Flower bakida lafiya kibari gobe sukazo se suyi.” “Don’t worry ai bawani aiki bane zaki tayani koh Amal?” “Why not Ya Fannah.” “Good muna jiranka kefa barakichi tuwon ba asiyo dake?” “A’a banachi banaso.” “Ya muku kyau keda wannan yayan naki wato bakiya chin tuwo kema? Seku nemi abinda zakuchi nide aje asiyo min tuwo da miyan yakuwa I’m hungry.” “Toh Mom Hanan” yayi maganan tare da rufe gab dake tsakaninsu daidai zeyi pecking goshinta kenan taja baya sakamakon haka Amal ta k’yalk’yale da dariya “wai! Wai! Su Ya Anas ansha boncy, an kwashi shoki” itama Fannar bata san lokacinda ta qyalqyale da dariya ba. “Wato ni kikayi shunning a idan Amal ko Flower?” “Ni kaje ka siyo min abinci abeg yunwa nakeji.” “Kin kyauta kekuma Amal ina dariya kikemin nafasa bada iphone 7 d’in ma Shettima zan bada.” “A’a Ya Anas please I’m sorry”*** Bayan tafiyan Anas Amal ta d’auko bucket da towel dan fara goge-gogen da Fannah tace zasuyi sede ta tarar da Fannah zaune a parlour. “Ya Fannah kince akwai goge-gogen da zamuyi.” “Wasa nake babu zo nan ki zauna” tayi mata nuni da space dake gefenta “zamuyi wata magana” ba gardama taje ta zauna. “Amal ke ba yarinya bace yanzu you are 15 years old kinsan whats right and wrong koba haka ba?” Ta gyad’a kai “good” Fannah ta cigaba “inason ki saurari abinda nakeson fad’a miki da kunnen masu hankali ki ajiye duk wani abinda Ya Anas naki ya fad’a miki a gefe do you get me?” “Yes Ya Fannah.” “Mesa kika k’i ma Ummimi magana? Baki tausaya mata ne she lost 3 of her children, three fa Amal how does it feels ke lokacin da classmate naki nema yarasu ya kikaji balle ace ‘yan daka haifa har guda uku kana ji kana gani aka siyar dasu, just how bad does that feels?” shiru Amal tayi bata iya tace komai ba. “Magana nake miki Amal.” “It feels bad.” “Good then meya kamata kiyi dan sata feeling better kuma?” “Inyi condoling nata in bata hak’uri.” “Exactly amman mesa bakiyi ba?” “Ya Fannah ni kin manta abinda tamin ne danake baby? She hated me batare dana mata komai ba ko shayar dani batayi ba, to cut the crap har cewa tayi zata zubar da cikina kuma ga ciwon dataji ma Ya Anas nifa bana sonta.” “Kai kai ya isa haka ya isa karki sake fad’in bakiya son Ummimi, kema Anas ya koya miki wannan banzan halin nasa ko? Ya cusa maki tsanan mahaifiyarki, waya gaya miki ana k’in uwa ne?” “Ya Fannah nifa ba k’inta nayi ba ita ta k’ini, ita mesa baraki mata magana ba.” “Ai na mata Amal we humans we are prone to make mistakes ko ke nan akwai mistakes da kikayi kuma akwai dayawan da zakiyi a gaba haka Allah ya hallice mu we aiint perfect amman kuma the best amongst us shine wanda yayi laifi yayi realising yakuma tuba kamar yadda Ummimi tayi kiga kukan data tayi mana d’azu akan yaran data haifa kinsan da zata bud’e baki ayau tace ta tsine muku gabad’aya bameyin albarka cikin ku kin sani?” Amal ta kad’a kai. “Kinga shiyasa, Amal duk abinda zakiyi ma Ummimi aduniyan inma duniya zaki siya mata wallahi barekai kwatankwacin d’aukan cikin ki datayi ta reneshi har ta haifeki ba, kinsan azaban haihuwa kuwa? Ba zafin daya fishi se mutuwa fah shiyasa akace duk wacce ta mutu ta hanyan mutuwa ‘yar aljanna ce tayi mutuwan shahada, uwa uwa ce komin rashin dad’inta koda cikin shege tayi ta haifeku wallahi shima abu ne our mothers are priceless ba abinda zamu iya musu in return of abinda suka mana.” © MIEMIEBEE

TANA TARE DA NI... PAGE 96 BY MIEMIEBEE “Toh ni yanzu me kikeso in mata Ya Fannah?” “Kema ai kinsani Amal kidena biyewa Ya Anas kibata chance da take nema to hold you and be your mother bawai nace kiyafe mata bane amman kibata wannan chance da takeso dakanki zaki yafe mata in kikaji dad’inta ke bakison kisan mamanki ne?” “Ai nasan Ummie.” “Ummie ba itace mahaifiyarki ba Ummimi ce mahaifiyarki...” haka Fannah tariga ma Amal nasiha seda ta kashe mata jiki. Dawowan Anas ya taho ma Fannah da tuwonta nan tasamu ta kora yunwa shikuma da Amal suka wuce kitchen dan dafa nasu kamar Anas yasani ya tambayi Amal ko Fannah tamata maganan Ummimi bayan fitansa, bata b’oye masa ba ta fad’a masa zahirin gaskia. “Ya Anas don’t you think is about time mu bawa Ummimi chance to be our mother? Wallahi wa’azin da Ya Fannah tamin ya mugun tsorata ni.” “Ai dama nasani, nasan hakan ze faru kinaji na ba bawani chance da zakibawa Ummimi am I clear?” Baki na rawa tace “yy.. Yes.” Washegari... Da sassafe Ummimi ta tashi tayi wanka sannan ta rok’i Ummie data rakata kitchen dan nuna mata inda postions na plates da sauran utensils suke hakan kuwa akayi breakfast me rai da lafiya favorite na Abuu ta had’a wato doya me k’wai a jiki bayan tagama ta had’a kan dining. 8:30AM Abuu yafito daga d’akinsa cike da ladabi da biyayya ta sauk’a har k’asa ta gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa. “Ya Ibraheem ga breakfast chan na had’a maka dan Allah kar kace bara kaci ba kayi hak’uri please” kai ya gyad’a mata sannan yabita dining d’in taja masa kujera ya zauna sannan tasoma serving nasa tana bud’e flask d’in k’amshin girkinta wanda he can’t tell how he missed it ya buga masa hanci bayan tayi serving nasa ta had’a masa tea sannan ta koma gefe tana kallonsa a hankali yasoma chin abincin har ya k’are. “In k’ara maka ne?” Ya gyad’a mata kai dad’i sosai taji a ranta “ashe har a yanzu baka dena son doya me k’wai ba.” “Mesa zan dena so bayan kin riga kin saba min dashi, kefa barakiyi breakfast d’inba?” “Zanyi amman nafison duk ku karya tukuna, Shettima fah? Har yanzu yana kai goman safe kafin ya tashi kokuwa ya rage bacci?” “Keda d’anki kuma kina iya zuwa kiduba d’akin sa ai shine first room by your right.” “Toh nagode sosai Ya Ibraheem.” Seda yagama chi ta masa Allah kare ya fice office sannan ta dawo ta d’iba wa Shettima nasa a plate da tea nasa ta nufa d’akinsa a hankali tayi knocking. “Waye ne” ya tambaya. Da k’yar bakinta ya iya cewa “Ummimi ce Shettima.” Daga nan be sake cewa komai ba. “Shettima yi hak’uri ka bud’en kaji? Yi hak’uri please.” Nanma shiru “Shettima barin bar nan ba har se in ka bud’en k’ofan nan.” Tafi minti goma tsaye a wajen sannan Shettima ya tashi ya bud’e mata ba tare da yace mata komai ba, bayansa tabi ta ajiye masa breakfast d’in akan centre table dake d’akin. “Ina kwana Shettima?” Nanma be amsata ba gefensa ta nufa ta zauna kan gado. “Shettima barin iya forcing naka kayimin magana ba saboda na kasance me laifi amman kayi hak’uri ka tashi ka karya kaji Babana?” “Ummimi why are you doing this?” “Saboda inason ka Shettima, ina sonka fiye da yadda nakeson kaina.” “Shine kika tafi kika barmu alokacin da muke buk’atanki?” “Barin ku danayi shine babban kuskuren dana tafka kuwa Baba na shiyasa nakeson inyi making up for the last 15years da mukayi ba a tare ba, yi hak’uri ka karya kaji?” Hannunsa taja ta zaunar dashi sannan da kansa ta soma basa abincin yana karb’a har yagama chi. “Thank you so much Shettima na wannan dama da kabani Allah ya saka maka da alheri yakuma maka albarka.” “Ameen” ya amsa. Daidai nan wayarsa yasoma ringing kasancewar wayar na kusa da Ummimi tasamu daman ganin wake kira ‘honey boo’ taga rubuce kan screen d’in. Da sauri ya d’aga wayar daga dubanta sede yakasa amsawa ganin Afrah ke kira, d’an murmushi ta saki “haka Baban nawa ya girma? D’aga wayar mana to ko se surikar tawa tayi zuciya ne?” Besan alokacinda ya murmusa ba. “Ko kunyan Ummiminsa yake ne?” “Ummimi fa ba budurwa ta bace.” “Awww shine akayi saving lambarta da honey boo, d’aga mana kose ya tsinke ne.” “Zan kirata anjima.” “Toh wace ita? Wata lucky girl d’in ne ta sace min zuciyan one in town son d’ina?” Murmushi sosai Shettima ke “sunanta Afrah k’anwar Fannah.” “Wow aiko ina da tabbacin itama tana da hankali kamar Fannah, Allah tabbatar mana da alkhairi yabar ku tare.” “Ameen Ummimi” “I will love to know you better Shettima” “Don’t worry” yayi maganar yanasa shirt nasa. “Toh Babana ya naga kamar kana shirin fita?” “Eh makaranta zani inada lectures.” “Oh okay me kakeso kaci da rana?” “Babu ba sekin dafamin komai ba zan siya a school.” “A’a mahaifiyarka na raye bara ka chi abincin waje ba fad’a min meh kakeso.” “Ina irin macronin da kike dafa mana? Irinshi nakeso.” “Toh angama son Allah kiyaye kaji? I love you.” So yake yace mata he loves her too amman kuma yakasa dan haka ya gyad’a mata kai zallah. Bayan tafiyan Shettima ta share masa d’aki tayi mopping tsatsaf haka d’akin Abuu ma sannan tasake yin sabon breakfast masu Anas tare da Ummie suka fita dankai musu sede Ummie tak’i shiga tabar Ummimi ita kad’ai, securities suna ganin Ummie suka bar Ummimi tashiga door bell ta danna alokacin Anas na aka kitchen shida Amal suna had’a musu breakfast ita ya tura da taje ta bud’e ganin Ummimi ce ta bud’e tare da gaisheta kamar yadda Fannah ta buk’ace ta. Dad’i sosai Ummimi taji “Amal my princess ya kike?” “Lafiya.” “In shigo?” Daidai nan Anas yafito “waye ne Angel?” “Ummimi ce Ya Anas” apron d’in jikinsa yacire sannan ya k’ariso “ina kwana Anas” kamar wanda bare amsaba ya amsa “lafiya” tare da sake tare k’ofan dan kar ta samu daman shiga “wani abu ne?” “Breakfast na kawo muku.” “Ai da baki b’ata lokacinki ba we are making breakfast already zaki iya tafiya.” Hannu tasa ta taresa daga rufe k’ofan “Anas please karka min haka dan Allah” tayi maganan hawaye na ciko mata a ido daidai nan Fannah tafito daga d’akin sanye take da kayan bacci iya guiwarta, ganin alaman baquwa bakin k’ofan yasa takoma ta sanya hijabi sannan tafito “Habeebi meke faruwa anan?” “Ya Fannah Ummimi ce tazo.” Amal ta amsata. “Shine baku shigo da ita ba?” tayi maganan alokacin datake tsaye gefen Anas. “Ummimi please kishigo” wani kallo ta watsa wa Anas sannan tashigo da Ummimi ciki anan suka gaisa. “Waya miki kwatancen gidan namu?” “Tare da Ummie muka taho tana waje tana kuma gaisheku duka, dama breakfast na kawo muku.” “Allah sarki Ummimi da gajiya haka ai da baki wahalar da kanki haka ba, Anas d’an karb’i mana” yi yayi kaman be jita ba “Amal karb’i flask d’in kinji?” Ba gardama ta amsa takai kitchen hira kad’an suka tab’a wanda ciki ko uffan Anas be furta ba haka Amal ma kasancewar taga idon Anas daga k’arshe ma kitchen ya koma ya cigaba da abinda ke gabansa da Ummimi tazo tafiya takira Amal tare da miqa mata wasu hada’d’d’en porches na iphone 7s. “Gashi Habibti wannan naki ne naji Ya Anas ya siya miki iphone 7 koh?” Ta gyad’a kai “toh gashi bansani ba ko kinason maroon and red colour? best colorn Basmah da Barrah kenan I was thinking ko kema haka kinaso” amsa Amal tayi tana k’are musu kallo “sosai inason red and maroon colour Ummimi thank you.” “Always Habibti” ta bud’e mata hannu da nufin hug ba gardama Amal taje tayi hugging nata wani erin yanayin da bata tab’a tsintan kanta ciki ba tayi yau, tunda take bata tab’a jin dad’in hug ba kamar na yau gaskiyan Fannah our mothers are priceless sunjima a haka se kallonsu Fannah ke cike da jin dad’i ina ma Anas zebawa Ummimi chance d’innan ta zame masa uwa kamar yadda take buqata. “Toh zan tafi seko gobe in dawo kinji?” Amal ta gyad’a kai. “In na dawo gobe zaki bani labarin ki, kinga yanzu nasan favorite colors naki inason insan komai about you zaki min?” Shiru tayi chan ta gyad’a kai “thank you so much Amal Allah miki albarka yamuku albarka gabad’aya zan tafi” ahaka sukayi sallama. Dawowan Amal ta wuce kitchen “Ya Anas kalli porches da Ummimi ta kawo min na wayan daka sayamin amazing how tasan favorite colors d’ina koda shike tace favorite colors na step sisters namu Allah jik’an rai Barrah da Basmah ma kenan, Ya Anas Ummimi isn’t bad.” “Mesa kika karb’a?” “Ya Anas I’m sorry.” “Bance karki mata magana ba?” “Ya Anas she is our mother.” “Naji zan karb’i iphone d’ina se muga aina zaki sa porche d’in.” “Ya Anas I’m sorry.”*** ★★★★ Haka nan tun daga ranan Ummimi tacigaba da musu girki, da sauran ayyukan gida dukda abinda Anas ke mata hakan be hanata ja da baya ba saboda tasan dalilin dayake hakan alokacin data tafi shine me wayon chan dole abin yafi affecting nasa, addu’arta a kullum baifin Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting nata as his mother ba, duk yadda yayi dan hana Amal alak’a da Ummimi yakasa as the saying goes ba a shiga tsakanin uwa da d’a, shak’uwa me k’arfi ne yashiga tsakanin Ummimi da Amal har fiye da nata da Shettima koda Amal takoma gida d’akin Ummimi ta tare, atare suke kwana da Ummimi, tamata tsifa tamata kitso har wanki haka ma Shettima tuni suka daidaita a tsakaninsu daman Abuu abinda yake jira kenan bayan ya tabbata everything is cool tsakanin Ummimi da yaranta ya dawo da ita d’akinta dad’i sosai Ummimi taji harda kukan murna her biggest dream is now a reality su Ummie da Fannah duk sunji dad’in wannan re union d’in har small party suka had’a inda Fannah tayi introducing Ummimi wa Maminta anan Ummimi taga Afrah in-law to be nata abinde se wanda yagani they turn out into a one big happy family banda Anas da duk wannan abubuwa da akeyi baima zuwa bale yaga kayan bak’in ciki har a yau bayajin ze iya yafewa Ummimi yariga ya dawo daga rakiyarta gabad’aya sede hakan be hana Ummimi fita daga harkansa ba ita ba. Musamman Abuu ya kira Fannah yamata godiya in person in da badan ita ba yasani da bare sake had’uwa da Ayshan sa ba, dabadan Fannah ba da Amal won’t get the chance to see her mother again, da badan Fannah ba da Ummimi won’t get the chance to see her family ever again har ta nemi gafararsu dan haka yayi mata godiya sosai tare sanya mata albarka ba iyaka. Shak’uwa na haqiqa ne ya cigaba da shigewa tsakanin Fannah da Ummimi, yadda Ummimi tad’au Amal haka tad’au Fannah tamkar ‘yar data haifa saboda irin ladabi da biyayyan da Fannah ke mata itama sekace wa Mami. Ummimi da Abuu dasu Shettima ne duk sukaje gidan iyayenta, alhamdulillah iyayen nata na nan da rai dakuma lafiya anan duk suka nemi gafarar Abuu akan abinda suka yi masa shekaru da dama da suka shud’e. Tun daga wannan rana rayuwa tayi turing perfect ma wannan family kan Ummimi da Ummie a had’e sekace ba in laws ba sosai Ummie kebawa Ummimi girma bata kuma dena yiwa Anas wa’azi ba itama fatanta Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting Ummimi. Cikin Fannah se girma yake masha Allah a yanzu haka cikin nata ya tsufa yanada 8 months da sati d’aya, sosai cikin nata yayi girma yazamo ko k’wararren motsi zatayi setayi dagaske, ga wani erin tsoron haihuwan datake cikin yi a kullum ko asibiti bata son zuwa, Anas, Mami da Ummimi ke cikin kula da ita kullum, Amal tadawo zama dasu ma tak’i dan yadda batason rabuwa da Ummiminta bata tab’a sanin dad’in uwa ba se a yanzu. ** Yau ranar ta kasance Saturday zaune Fannah ke a garden tana d’an ciye ciyenta, gefenta Anas ne da laptop a gabansa yayi focusing sosai yana aiki akai. “Habeebi” takira sunansa. “Nagaji” “Yes Mom Hanan, Hanan na damunki ne?” Kai ta gyad’a a shagwab’ance. Laptop nasan ya rufe tare da ajiyewa kan table sannan ya matso kusa da ita yana shafa gashin kanta a hankali, “hak’uri kad’an zaki k’ara Sweetheart nan da 3 weeks in shaa Allah Hanan namu zata fito tadena damun min Flower” yayi pecking goshinta. “Yau zaki iya fita walk?” Kai ta girgiza mai da wuri “banajin zan iya fita yau Habeebi.” “Flower haka jiya mafa kika k’i fita kin tuna me Dr tace? Yi hak’uri kinji?” A hankali ya miqar da ita suka fita walk tafiya kad’an Fannah tayi tace ita su dawo gida hakan kuwa akayi.*** 3 weeks later 2 days later, exactly 9:43AM... Kamar yadda suka saba kwanciya manne da juna haka ma suke a yau sede Fannah ta kasa bacci tun bayan Sallan Asuba da sukayi, da k’yar ta miqe ta zauna dan girman cikin nata. Bayanta ke mata wani erin zafin azaba kamar tacire ta ajiye a gefe da na bayan ya lafa sekuma cikinta yahau juyi ta k’asa k’asa tun tana iya jure zafin takasa ta k’wala wa Anas kira a firgice ya tashi ganinta yayi miqe a k’asa tana hawaye tana juyi. “Omg! Flower what is happening?” kafin tayi magana ruwanta yayi breaking. “Anas I’m in labour please do something arrggh!” Ta saki k’ara hannunta na a k’asan mararta bayi yashige yayi brushing yafito da wuri da k’yar ya iya d’agata yakaita mota sannan ya d’ago maternity bag nata se asibiti, hankalinsa ya matuqar tashi ganin yadda Fannah ke kuka kamar ba gobe da k’yar ya iya tattara hankalinsa gu d’aya ya kira Mami ya sanar da ita, Mami ce ta sanar dasu Ummimi kusan a lokaci d’aya suka iso asibitin duka. Alokacin Anas na a d’akin da Fannah ke ya riqe hannunta gagam cikin nasa yana kissing kanta assuring her _YANA TARE DA ITA_ sede sam its not helping sekaceba Flowersa ba gabad’aya tafita daga hayyacinta tana kuka tana ihu abin tausayi wane mutuwa zatayi, tana zufa yana share mata shima besan a lokacinda ya soma kukan ba sunfi minti talatin ana abu d’aya tun yana iya jure kukan nata har yakasa besan a lokacinda yafito ba he can’t take it anymore, bare iya jure pain da wahalan da Fannah ke fuskanta ba. Ummie, Ummimi da Mami ya tarar tsaye bakin k’ofan da gudu yayi kan Ummimi yayi hugging nata batayi tammanin hakan ba tsabagen yadda mamaki ya rufeta kasa hugging nasa back ma tayi. Kuka yake wane d’an yaro ya matseta gagam ajikinsa. “Ummimi I’m sorry, I’m so sorry please dan Allah kiyi hak’uri, please forgive me I never knew you went through this kafin kika haifeni nima dan Allah kiyi hak’uri for all that I’ve done to you, forgive me please mother.” © MIEMIEBEE

Share:

11 comments:

  1. Nabilahshuaib55 @ gmail.com4 October 2016 at 11:12

    wowww great plz a turo karashin

    ReplyDelete
  2. Pls akarasa mana tana tare dani dawaye sanadi

    ReplyDelete
  3. dan allah aturo karshen

    ReplyDelete
  4. Acigaba Dan Allah

    ReplyDelete
  5. Khadijah Salim MHD11 October 2016 at 13:41

    Pls pls aciga bah mana

    ReplyDelete
  6. Wow Lovely, Its D Best Novel

    ReplyDelete
  7. Tans Dan Allah A Karasa Mana Tana Tare Dani

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).