WAYE SANADI?
36
MUH'D*ABBA*GANA
www.abbagana.pun.bz
shi kenan safiyya na dai kusa dawowa nazo na ga nana safiyya. baka da hankali kan yayi magana na katse wayar.
yau ya rage saura kwan biyu mu tafi umma kuma gobe zasu dawo duk wani kayana dazan bukata na hada su har ma na zubasu a boot.
yau tsakar dare zasu sauka gobe da safe suna gida na gama duk wani shirina zan kwanta dauki nake gari ya waye naga ummata rediyo na na kunna ina sauraran karatun alkur,ani har bacci ya daukeni cikin barci naji kamar mutum a bayana hannu na kai na taba bayana nayi ba komai dan haka naci gaba da barci na can kuma sai naji kamar ana shafan jikina firgit na tashi na hau dube dube banga komai ba, tsoro na ya kamani, da sauri na nufu kofa zan fita ji nayi an dauke ni cak an cilla gado kan nayi ihu naji an toshe bakina kan na dago naji an danne ni, cikin wata siririyar mury naji magana'yau zanyi maganin rashin mutuncin da kike na keta abinda kike tinkaho karfina na saka na shiga ture shi na kasa ganin yana neman yi min babbar illah naji wani irin karfi yazo mun yunkurawa nayi iya karfina na tureshi nayi saurin mikewa jikina yana rawa kokarin fita nake naji an rungume ni iya karfina na kama naman wuyarsa na ciza ba shiri ya saken, ji nayi ka fata ta bugi cup din glass ba wani bata lokaci na dauka yan kara matsow na buga masa har sanda ya pashe, wata mahaukaciyar kara ya saka bashiyi ya zare sakata ya fita a guje, da sauri na kunna fitila nayi saurin rufe kofar gani nayi bakin kofar ya bachi duk da jini, a wajen na tsugunna ina kuka waye wannan? wake shirin cutardani? burina gari ya waye umma ta dawo wallahi sai mun bar gidan nan ta gama auren.
ina zaune har gari ya waye buga kofa nakeyi kamar za a balla na tashi da sauri na bude, ji nayk an zabgan wani mugun mari a gigice na dago ina kallonta. hajiy ce babar alhaji nasiru zo ki bar gidan nan karuwa Allah ya tona asirinki. a razane na dago kai tsawa ta dakan zo ki bar gidannan yau Allah ya tono asirinki shegiya karunwan ban.......kan ta karasa na daga hannu iya karfina na zabga mata mari tare da hankada kofar na mayar na rufe naci gaba da kukana
umma naji tana kiran sunana nayi saurin budewa ina ganinta na fada jikinta ina kuka umma kizo mu bar gidan nan Allah kin gama auren, tunda kin kashe auren dole ki fadi haka nana baki kyauta min ba meyasa kika fadi haka? nana kin kawo saurayi gidan nan har kuka kwana da abba ya ganki shine kika dau abu kika fasa masa a kai safiyya me yasa kika mari babar alhaji?? karon farko da umma ta ba kiran sunana kai na shiga girgiza mata nama kasa magana dakyar na iya furta umma karki min haka kin fi kowa sanin halina, wallahi sharrin abba ne shi ya shigo dakin da da..... maganar hajiyar mukaji kuzo ku bar gidan baya sake ki ba? kuma ki saurari kiran kotu keda karuwar yarki yunkurawa nayi na kanga dady ya rikeni a hankaki naji muryarsa kiyi hakuri safiyya nasan shari abba yayi miki, zuciyata tana gayan ba zaki taba aikata haka ba komawa nayi daki na dauko jakata hannun umma naja muka fita tunda muka shiga mota nake kukan bakin cikin sharrin da abba ya kullamin..
a bangaren umma tunanin ya zasu kwashe da kaka take, har kofar gida ya kaimu na zaro dari biyar na mika masa kana na zaune a zaure taga shigowar umma da murta ta tashi rakiya saukar yaushe ganim hawaye na bin fuskarta yasa tayi shiru lafiya kike ku..... bata karashe ba taga shigowa na ina jan akwatun umma sai yanzu umma taji kuka yazo mata haka zaki zo kina kuka farar takarda ta mika mata babah alhaji ya sake ni. jawaf tayi ta zauna yanzu rakiya sai da shaidaniyar yarki ta kashe auren nan. inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, na shiga uku ni safiyya wannan yarinyan kin gama asara ai wallahi gara da alhaji muntari bai karbi cikinki ba in da ya karbeki a matsayin yarsa da bakin cikin kine zai kashe shi. umma ce ta taho da gudu zata rufe mata baki tayi saurin dokw hannunta taci gaba da cewa kuma wallahi ba zaki zauna a gidan nan ba sai dai ki nemi wajen zama inda kika raba yata da gidan aurenta to wallahi ki tafi waje ki nemi ubanki kalmar da ta dinga yawo cikin kunne na kenan ji nayi numfashi na yana neman daukewa kan umma na nufa da gudu.......
TO BE CONTINUE SOON!!!!
MUHD ABBA GANA
09039016969
Abbagana hausa novels @ facebook.
[9/30, 11:48 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI?
MUH'D*ABBA*GANA
www.abbagana.pun.bz
Kan na karasa babata tareni wani irin mari ta sabgan nan take wajen yayi ja iya karfinta baya baya naji nake nayi saurin dafe bango cikin wata irin murya na furta umma gayan gaskiya me maganar babah take nufi akaina ban da uba sai yanzu naji wani marayan kuka ya zomin umma tambayarki nake gayan gaskiya ni din shegiyace ban da uba? tana kuka tace nana kina da mahaifi wallahi ke ba shigiya bace nana matsala aka samu har mahaifinki ya ki kar.........karki karasan labarin bakin ciki na yarda ni din shegiya ce, wayyo Allah na umma na barki har abada ba zaki kara ganina ba cikin kuka umma tace nana karki guje ni ki tsaya ki saurari maganar da zan gaya miki wallahi kina da ub.....kuka yaci karfinta ta kasa karasawa na juyo ina kallon babah dakyar na iya bude bakina na furta na gode babah da wannan mummunan labarin na kuma ji dadi gayan matsayina da kika yi yanzu nasan wacece ni din ina fadar haka na juya har nakai bakin kofa naji muryar babah zonan safiyya.
nayi saurin juyowa ina girgiza kai wallahi babah bazan kara shigo miki gida ba zanje nayi rayuwata ni daya ina fatan ubangiji yayi gaggawar daukar raina na huta da wannan bakin cikin na juya ina kallon umma wanda take tsugunne tana ta faman sharman kuka kan babah ta kara magana har na fice koh ganin gabana ba nayi kawai saka kafata nake ba tare dana duba ba ji nayi an taka birki zuro kai akayi daga cikin adaidaita sahu haba baiwar Allah tunanin me kike har kika hau titi sai lokacin na kula kan titi nake karasawa wajensa nayi tare da cewa malam tafiya zakayi yace ehh ina zaki B.U.K shigo muje tunda nashiga na hada kai da gwiwa nayi gaba da kukana. hajiya ciki za,a shiga? naji maganarsa muje ciki har bakin dakinsu farida ya kaini na zaro kudinsa na basa, ita daya ce a dakin tana duba kittafi taji shigowata tayi saurin dago kai suppy daga ina da san.... hawaye data gani a fuskata shi ya hanata karasawa.
karasawa nayi na zauna akan katifarta safiyya lafiya kike kuka?? babu irin magiyar da farida ba tayi ba akan nayi shiru nayi mata bayani, har ta gaji cikin fushi tace tun dazun nake lallabaki kiyi shiru ki min bayani meye yake faruwa kin ki kigayamin kin fi rabin awa kina kuka tunda ba zaki gayan ba bara na kira ruky ki gaya mata ta dau wayarta ta fita.
ba,a fi minti talatin ba suka shigo tare da momy gatanan ruky tun dazun nake lallabata tayi shiru taki momy tayi saurin dagoni ganin yadda fuskata ta kumbura yasata gigice safiyya dukanki akayi na girgiza kai ina kuka to mota ne ya bigeki na kara girgiza mata kai hannuna ta kama muka fita motarta muka shiga baby kin fa tayar min da hankali ki gayan meyake faruwa.
A fusace farida tace me kika dauke mu maciya amana tun dazun muke miki magiya ki gaya mana meye yake faruwa kin ki ki zauna ki tayi ta bude motar ta fita.
momy ta juyo tana kallona baby yau na ga matsayina ashe duk momy da ake gayamim a bakine zan tafi gida ganin ina kokarin bude motar zan fita tayi saurin rike hannuna zauna safiyya bana son ki gayamin damuwarki bara muje na sauke ki a gida, cikin dashewar murya tace momy bazan koma gida ba na bar gida har abada baki ta rike tana murmushi baby har yanzu ke din yarinya ce to yanzu ina zaki kwana kan gobe mu tafi? nima ban sani ba muje gidan mu momy ki bar....karkice komai nasan wannan kukan bai barki kinyi break ba taja muka tafi Al'amin restauranta muka nufa ita daya ta ta dawo da take away shigowa tayi to bude maza cinye mu wuce momy bazan iya ciba hannunta tasa ta debo bara nayi miki ta yara haaaaa babyna" cikin dabara naci abinci sosai🙄.
baby har yanzu baki min magana ba sai ajiyar zuciya kike kin tayar min da hankali har farida tayi fushi bara muje chemis su dubaki.
school muka koma ta samu waje tayi fakin baby bara naje wajen prof adam. na daga mata kai dai da taga nasha maganin sannan ta fita bayan na koma nan take barci ya dauke ni dab da magariba na farka, momy na hanga a gabana tana waya tayi saurin juyowa tana murmushi baby kin tashi na daga mata kai tun dazun nake jiranki kitashi momy me yasa baki tasheni ba? gara ki tashi da kanki ruwa ta mikomin na fita na yi alwala nashi sallah tare muka kwanta ina jin munsharin momy tunda na kwanta na fada duniyar tunani🤔.
abbagana hausa novels @ faceebook.
[10/1, 10:53 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI?
MUH'D*ABBA*GANA
www.abbagana.pun.bz
me yasa umma ta min haka taje ta hanyar banza ta samu cikina ya zanyi da raina meyasa ban bari abba ya aikata abinda yaga dama dani ba, na rama abinda umma ta min ji nayi kaina yayi wata irin sarawa nayi saurin dafe kaina tare da kiran sunan Allah,me yasa tun da ban taba tunanin ina dangin babana suke ba tabbas maganar babah gaskiyace inda da uba duk daya mutu ai yan uwansa zasu iya zuwa su ganni ko ita ta kaini in gansu meye dalilin boye min gaskiya umma koh Alhaji muntari shine wanda suka hadu da umma ta haifeni? wani irin kukane ya kamani momy tayi saurin tashi lafiya safiyya kike kuka? kai kawai na girgiza mata ta matso kusa dani tare dafa kafadata cikin sanyin murya tace haba safiyya kina abu kamar ba musulma ba duk wani tsanani yana tare da sauki kiyi hakuri ki tashi ki kaiwa ubangiji kukanki wallahi na tabbata in har kika mika wuya kika gaya masa abinda yake damunki na tabbata zaki ga komai yazo miki da sauki ki tashi kiyi sallah ki kai kukanki wajen ubangiji kai kawai na daga mata na shiga toilet na dauro alwala kwana nayi ina kaiwa ubangiji kukana.
karfe takwas muka fito dakin hajiya muka shiga bayan mun gaisa tace har kun shirya?? mun shirya kin san takwas da rabi zamu tafi ai tun dazun Alhaji ya fito baku tashi ba kuyi maza ku karya kan ya kara saukowa tunda muka zauna na shiga rijiyan tunani.
abbagana hausa novels @ facebook.
[10/1, 11:17 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI?
MUH'D*ABBA*GANA
www.abbagana.pun.bz
momy tace maza ki ci abinci kan abba ya sauko momy bana jin yunwa bakin ciki ya cika zuciyarta okey kin jawa kanki hajiya tace sai kin gaya mata meye yake damunki haka na dinga turawa kamar madaci
saukowa yayi yana kiran rukayy tayi saurin amsawa da cewa tunda zun abba muke jiranka au abun ya koma karya saukowata uku baku tashi ba.
dakin hajiya muka shiga ta jima tana yi mana nasiha tare da bamu addu'o'i sannan muka kama hanyan makaranta.
mun jima yana yi mana nasiha a cikin motarsa sannan muka fito dakin farida muka shiga bamu jima da shiga ba wata yarinya rashida ta shigo ana kiran safiyya muktar nayi saurin dago kai rashida wa yake kirana? alhaji nas...' karki karasa sunansa rashida kince masa ina nan? ta girgiza kai cewa nayi bara na duba toh kice masa bana nan cikin mamaki momy tace saboda me? momy bana son ganinsa kwata kwata in kika matsayan naje wajensa Allah kema zaki rasani, bazaki kara ganina ba. shi kenan ya isa ta juyo tana kallon sadiya fita kice bata nan rabuwarku da ita tun ranar jumma'a . yana tsaye a jikin motarsa ta karasa dady an tashi lafiya? ina safiyya? cikin mamaki me hade da tashin hankali yace bata zo nan ba? au dady na zata ita ka kawo rabona da ita tun friday. ba ita na kawo ba nemanta nake tun jiya ido ta zaro dady me yayi zafi nema a jalloh haka. babu amma don Allah yanzu ina kike ganin za,a sameta? gaskiya dady ban sani ba saboda ita safiyya bata da kawaye ni daya ce kawarta sai rukayya kuma muna tare da rukayya toh kina ganin zata iya tafiya lagos da kanta? nima yanzu nayi tunanin hakan tun jiya wasu suka fara tafiya yafi minti biyar bai yi magana ba can ya numfasa tare da cewa sadiya ga wannan in har kin jeh kun sameta ki bata kuma ki ban lambarki in kin sameta kin min waya dan Allah ya miko mata karamar farar jaka toh dady insha Allah da mun hadu zan bata.
dakin ta shigo tare da mikamim leda gashi a fusace na dago sadiya ce masa ki kayi ina nan? auntyn masifa cewa yayi in mun hadu a can na baki farida mikomin ledar karba tayi tasa a jakarta tare da zabgan harara.
karfe goma mota ta daukemu a bangaren umma kuma.........
abbagana hausa novels @ facebook.
[10/3, 8:15 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI?
MUH'D*ABBA*GANA
www.abbagana.pun.bz
magajiya kin kyauta kinyi yanda ranki yake so kin kori jikarki kin kuma jefa yarki cikin bakin ciki me ki kayi kan wani dalili naki na banza waya gaya miki saffiya ce ta kashewa rukayya aure daman can Allah yayi aurenta zai mutu baki tsaya kinji abinda ya faru ba kika bata yarki a idon yarta cewar mallam mado, mallam kayi hakuri raina ne ya bacu dan ranki ya baci sai hankalinki ya gushe, ke yanzu zaki iya rantsewa safiyya bata da uba? kin bata yarki kan zigar shaidan kinga kin nunawa safiyya uwarta tayi yawon duniya to har sunanki kika bata ke din ina uban rakiyar ta taba ganinsa? ko ta taba ganin danginsa to kinga kema zata dinga miki ayar tambaya. ya juyo wajen umma wadda take ta faman share hawaye rakiya ki kwantar da hankalinki ki mikawa ubangiji lamarinki na tabbata safi....' sallamar alhaji nasir ce ta katse masa maganar bayan sun gaisa da mallam ya juyo wajen umma rukayya har yanzu baki bar kukan nan ba baki ji maganar da likita ya gaya miki ba? tayi saurin goge fuskarta babah tace me likitan yace mata? lokacin da muna makkah tayi zazzabi har ta kwanta shine muka je asibiti likita yake gaya mata tana dauke da juna biyu.
a razabe babah ta dago kai tana sallati yanzu kaima sai dai kaga tana da ciki shine ka saketa wato kai ma kana so ka mata sharri kace ba naka bane?? cikin mamaki ya dago kai babah wani ya tabawa rukayya sharri?? kar kimin mumunar fassara ki kaddara aure na da rukayya Allah ne ya kawo rabuwarmu rabuwarmu ba zata hanamu karbar kyautar ubangiji da yayi mana ba ina so...... maganar maganar mallam ta katse masa abinda yake so ya fada Alhaji har yanzu babu labarin safiyya?? wallahi mallam duk inda nasan zan sameta naje nasa an duba amma shiru ita kanta kawarta sun sauka a lagos din tace babu irin nemanta da ba tayi ba har wasu makarantun taje bata ganta ba. umma ce ta kara fashewa da kuka.
sallama tayi har wajen sau uku taji shiru dan haka ta shiga daki ina zaune nayi nisa cikin tunani har ban san lokacin da hawaye yake bin fuskata ba har ta karaso kusa dani hmmm saffiya Allah ya kyauta miki wallahi in wata cutar ta kamake ke kika saiwa kanki kin zauna kina tunanin banza momy ta fada cikin fishi nayi saurin dago kai na ta cigaba da cewa mutum baya jin nasiha tunda muka zo garin nan yau sati daya kullum kina daki baki da aiki daga kuka sai tunani damarki ta karshe in kinki ki mayar da hankalinki kiyi karatunki wai ma me kika dauki kanki?? da ubangiji ba zai saukar miki da kaddara ba? wallahi kinji na rantse in har baki cire wannan halin ba zamu yi fada ta mike zata fita nayi saurin riketa momy kiyi hakuri ta juyo tana hararata me kika min da sanyi hakuri sakarmin hannu na fita momy kiyi hakuri zan gaya miki abinda yake damuna amma bisa alkawarin zaki boye min sirrina ina zuwa tace kofar ta rufe ta dawo kusa dani ina sauraronki.
abbagana hausa novels @ facebook.
[10/3, 3:59 PM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI?
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
nan take na bata labarin abin da ya faru tunda ga shigowar Abba dakina har kawo sakin da Alhaji nasir ya yiwa umma muka dawo gida har karshen maganar. yanzu baby kan wannan yar matsalar kike tada hankalinki? cikin kuka nace momy wannan ce yar matsala rashin ubane karamar matsala? safiyya ke din baki da shedar da zaki gaskata haka umma tana ki tsaya ki saurareta kawai shedan yana ingizaki kika tawo kika bar mahaifiyarki cikin wani hali me yasa baki tsaya sauraran maganar babah din ba, fuskanta cike da hawaye na dago kaina momy me zan tsaya naji daga wajensu momy a lokacin nan in har na tsaya na cigaba da sauraran maganar babah zuciyata zata iya bugawa wallahi a yanzu nafi bukatar mutuwa momy bana fatan na kara ganin ummata momy ina ji cikin zuciyata kamar na shiga duniya na rama abinda umma ta min.
saffiya har yanzu ke din yarinya ce ke yanzu kina ganin in kin shiga duniya umma kika cuta? toh ina kina tunanin haka ki daina wallahi kanki kika cuta ke baki tsaya kin saurari maganansu ba. kina ganin Allah ba zai kamaki da laifin tayar mata da hankali da ki kai ba ki duba irin sonki da umma take miki amma....nayi saurin kaste ta momy ai don tasan bata da gaskiya ne shi yasa ta nuna min so da kauna kuma wallahi duk ranar dana gama karatuna saina shigar da umma kara ta nuna min ubana na ganshi ko waye ne s....kan na karasa momy ta dakan tsawa waike baki da hankali ne in kin kai umma kara wa kika tonawa asiri ki, zaki zo kiyi na dama ta cillo farar leda ga sakonki da dady ya bayar a kawo miki kuma wallahi in baki shiga hankalinki ba zanyi waya na gaya masa muna tare naga mutum ne kamar kafiri baijin lallashi 🙄 kuma ki dauka kiga meye a ciki. akan dole na karba na bude kudine rafa biyu yan dubu-dubu sai kuwa wasika ta dada daure fuskarta karanta mana cikin kuka nace momy bana son jin bayaninsa don Allah ki rabu dani bazan karanta ba.
wallahi sai kin karanta in kuma har baki karanta ba karki kara tunanin kinsan wata rukayya ta mike zata fita na riketa momy karki gujen dan Allah bari na karanta da kanta ta warware ta miko min dole na dora idona kan rubutun nasa.
"safiyya me yasa kika yankewa kanki irin wannan hukunci da zaki zo kina nadama wallahi safiyya nasan sharri abba yayi miki please safiyya ki dawo kin daga mana hankali ummanki tana cikin damuwa don Allah ki dawo garemu ki rungumi ummanki da yan biyu da zata haifa miki " wata irin zabura nayi umma zata haifa min kanne? wani cikin shegen tayi umma kin cucen kin cuci abinda zaki..... bakina naji an buge shi yasa ban karasa abinda nake son fadaba ta mike a fusace banza mara hankali tana fadar haka ta juyo zata fita kai na naji yayi wata irin sarawa wata irin kara na saka wadda ta dawo da momy da gudu dai dai lokacin sadiya ta shigo tare suka karasa kaina momy ta hau kiran sunana a gigice safiyya!! safiyya!!. safiyya!! sadiya sai faman jijjigani take nan take na saki ajiyar zuciya maganar momy na dinga ji sama- sama.
bude idona da zanyi zafi nakeji kamar an zuba borkono kin tashi naji muryar sadiya na daga mata kai dakyar na iya bude baki nace sadiya ruwa nake so momy ce ta mikon ruwan nayi kokari na tashi na zauna momy kirjina ciwo yake min sosai ina magana ina dafe kirjina wanda kamar zai fashe sannu baby gobe maje asibiti sadiya ta mike rukayya bari naje daki tana fita momy ta dawo kusa dani baby sannu na daga mata kai baby fushi kikeyi dani?? a,a momy tunani nake yaushe nayi barci ta hau dariya muna hira na juyo naga baby tayi barci sai munshari take. nan take na tuno wasikar Alhaji nasir momy ina tausayawa alhaji nasir umma ta cece......tayi saurin katseni kibar maganan na dago idona wanda ke cike da hawaye momy bazan iya cire maganar nan daga zuciyata ba, baby waye muhammad?? ya bugo miki waya yayi daga nace baki da lafiya duk ya tashi hankalinsa sai kira yake tayi baby shine sirrikin nawa?? momy banfa sanshi ba kawai kirana kawai yakeyi a waya to koma dai waye ni dai na yaba da hankalinsa harma kuma nace na bashi keh' ido na zaro waje momy ban san shiba fa ban taba ganinsa ba momy tunda kika min haka bazan kara daga wayar saba, ta mike kinga abar maganar taso muje kici abinci ba wani musu na mike dan yunwane ya timermireni wanda zai iya kashe ni. wani restaurant muka shiga bayan mun gama muna fitowa momy ta mikomin wayata kirashi yaji muryarki ko hankalinsa zai kwanta zan bude baki hannu ta dora kan lebeta karba nayi tare da kiransa" hello safiyya muryarsa ce ta doki zuciyata ya jikin naki na amsa tare da cewa naji sauki ganin zamu tafi nace masa in na koma daki zan kira kasamin karatu sai anjima. yayi saurin cewa safiyya karki katse a hasalce nace a kanme baran katse ba ina fadar haka na katse muna shigowa cikin makaranta muka hadu da saifullahi momy tace saifu saukar yaushe rukayya jiya muka tawo yanzu muka rabu da sadiya take gayamin safiyya bata ji dadi ba ya juyo wajena sannu safiyya ya jikin naki ko kallonsa banyi ba balle na amsa masa nayi gaba momy kamar zata nutse don kunya.
ina sallah ta shigo bayan na idar na juyo ina kallonta momy ya naga kina hararata laifi nayi?? baki min laifin komai ba kawai burgeni kika yi da kika iya rashin kunya tana fadar haka ta mike ta fita.
washegari na tashi babu wata damuwa a tattare dani tasowa nayi nazo wajen momy . momy fishi kike dani na gaisheki kinyi shiru ta dago fuskarta a hade wato baki san abinda kika min ba koh? momy gaya min Allah zan gyara ta dan saki fuskarta baby kowa yazo yace yana sonki sai kin wulakanta shi haka zaki zauna ba zakiyi aure ba tun muna kano ki kewa saifullahi rashin mutunci me kika fishi ina kallon wayarki an kira yafi a irga kinki dagawa kina abu kamar baki da ilimi ki gayamin me......kukan da taji nasane yasa bata karasa abinda yake bakinta ba.
abbagana hausa novels @ facebook.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.