[9:15PM, 5/7/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?
8
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
ko kalon kayan banyi ba na mike na tafi washe
gari ina zaune a soron gidanmu ina cin wake da
shinkafa wani yaro bai fi shekara sha uku ba ya
leko yana gani na ya hau dariya yana
tsokanata.nana a daki maza nana a daki aiko na
taso muka zuba gudu Allah ya ban sa'a ina
fitowa na rike shi na hau dukansa,yana ihu yana
zagina ni kuma ban fasa dukansa ba wani
mahaukacin zagi ya lallayo mun kan ya rufe
bakinsa na gwara kansa da kofar gidanmu wata
gigitacciyar kara ya saki karar da yayi ne yasa
kaka da umma lekowa da gudu,salati suka hau yi
kaka ta karaso."baki da hankali kina gani kin fasa
masa kai amma ba zaki sake shi ba,watau dan
haka kika zo soron ci abinci to wallahi bbu
ruwana ba zaki sake shi ba tana magana ta
kowan duka,mota tayi parking ya fito da sauri
haba nana me yasa kike san jawo magana (haka
kawai yau yayi min kwarjini) sake musu yaro ban
ce kala ba na sake shi nayi cikin gida ban san ya
suka yi da yaron ba.umma ta shigo "kizo yana
son ganinki.har zan ce ba zani ba sai kuma ba
mike na zauna a soro na zo bbu sallama ya ganni
kawai a tsaye meye kake kirana? bai damu da
yadda na tsaya masa ba yana murmushi yace
"rukayya a tace kina son magana dani oh ce
maka zanyi tunda kace sai ka aureta to in dai
zaka aureta sai dai ka aureta da yarta bbu me
rabamu sannan in kana so na amince ka aureta
sai ka samomin admission a B.U.K nayi candy
kuma takarduna sunyi kyau karka auri babata ka
ganmu a karkashinka kayi tunanin zaka juyani ko
zaka ban umarni ko kuma kace zakai min fada
bbu ruwanka da rayuwata,magana nida kai bata
zama dole ba duk abinda na shiryawa kaina baka
isa ka hanani ba in har ka amince,to na amince
ka aureta.nana zan samo miki admission a B.U.K
zan kuma dau nauyin har ki gama karatunki nana
kina gani inna rabu dake kina duk abinda kika ga
dama Allah ba zai kamani da laifin haka ba a
matsayina na mijin mahaifiyarki wanda inda kara
zaki iya bani matsayin mahaifinki to in kuma bbu
sai ki ban matsayin duk da kika ga dama."baka
da matsayin da zan baka ko takalmina ya fika...'
karar wayarsa ce ta katse maganar yana gama
wayar ya juyo yana kallona yafi ki shiru kinyi
shuru ina jinki ci gaba "bazan cigaba ba kuma
wallahi bazan yarda a ka aureta ba,sai ka kawon
sabuwar waya black berry da kuma nokia original
one sim oh daughter kawai rigima nima nayi
niyyar zan sai miki wayar nana irin son da nake
wa rukayya zan iya yi miki komai in kika kwantar
da hankalinki har mota zan sai miki kinga daman
mace bata hawa machine fatana nana ki nutsu ki
daina sa mahaifiyarki bakin ciki,
Abbagana hausa novels @facebook.
[8:13AM, 5/8/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?
9
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
Kinga kuma macece zaki aure ki haihu ki so yarki
ta dinga yi miki abinda ki kewa ummanki a yanxu
ba please my daughter ki tausayawa ummanki
kar kisa wata cutar ta kamata ummanki tana
masifar sonki karki samata ciwon zuciya inta
m........." kaga malam ya isheka meye ruwanka
da rayuwata wai kaga mallam zakai min wa'azi
ka wani bude baki kamar kofar gar......." marin
daya sauka a fuskanta na daga kaina ina mai
kuma ya kawo mallam mado "ke dai wallahi kinyi
asarar hankalinki shegiya mara kunya kaini
wallahi tunda nake a duniya ban taba ganin
shedaniyar yarinya irin ki ba,wadda bata dau
iyayenta da mutunci ba, kai kuma Alhaji ka zauna
yarinya tana zaginka kana lallabata in anzo
daurin aurenta ki hana ko ki tsine mata "baba
kayi hakuri kasan har yanzu nana yarinya ce
komai zai daidaita a hankali dole sai an dinga
binta a hankali" wannan shedaniyar yarinyae ce
ta san abi ta a hankali,to wallahi in baka ci
ubanta ba ba zata saurara maka ba dan...."sai
dai aci naka uban,banza munafiki kuma wannan
marin kayi na farko kayi na karshe dan wallahi
duk ran da hannunka ya kara karanbanin mari na
sai na rama banza anga mai kudi ana rawar kafa
Allah yasa dan yankan kaine." na juya cikin gida
da gudu sun jima suna tattaunawa da
malam,sannan ya shigo zayi kiran vaba ina zaune
ta shigo nana na dago ido ina kallonta.me ya
same ki a fuska? ba ke ki kasa mallam ya mare
ni ba ido ta zazzaro haba nana ya za'ayi nasa
malam ya dake ki wallahi ban san ya dake ki
ba,me kika yi mini da zansa ya dakeki dan Allah
nana kiyi hakuri yanzu yace ki kai masa takardun
nawa zai tafi dasu kuma dan Allah nanan k dinga
sanin maganar da zaki dinga gaya masa kin ga
koni ya girman bare ke kar ma dai ta dan in Allah
ya yarda sai ta hadu da aljanu.tayi masu rashin
kunyar taga in zatayi nasara' na mike ina
harararta.ina Allah ya yarda kene zaki hadu da
aljannu su shanye miki kafa da hannu'yana tsaye
yana dan yin waya na tura masa takardun suka
rufe wayar murmushu yayi yana duba ya dago
yana kallona nayi mamakin dana ga takardunki
haka banyi tunanin ganinsu haka ba,kwarai kin
ban mamaki kuma naji dadi Allah yasa ki dore
haka am....'" kan ya karasa nayi shigewata.
BAYAN WATA UKU
yau alhaji nasiru yazo ya shaidan gobe zan fara
zuwa makaranta dan fara karatuna, to nana gobe
zaki fara zuwa makaranta kuma kin san
makarantar nan ba irin makarantar da kika saba
bace,wannan ta hada maza da mata kuma yare
kala-kala dan haka ki tsaya ki nutsu kiyi abinda
ya kaiki.
Abbagana hausa novels @ facebook.
[8:15AM, 5/8/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?
10
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
ba ruwanki da kowa karatu yana bukatar
nutsuwa,nana zanyi farin ciki ace yau kin zama
barrister fatana ki maida hankalinki Allah ya
taimake ki ki kammala karatunki lafiya" sannan
ga alkawarinmu na waya kuma duk wasu kudi da
makaranta take bukata na riga na biya na gama
komai Allah ya taimaka ya baki sa'a ya mikon
wayar "ki turon ummanki" na gode na juya nayi
ciki washe gari aka daura auren umma da alhaji
nasiru ranar kuwa na fara zuwa makaranta.tun
tara na safe na tafi sai biyar na dawo na tarar da
gidan cike da mutane,bbu wanda nayi magana na
shige dakinmu umma na tarar tana kwalliya"
sannu nana yan jami'a ya karatu? karatu gashi
mun fara,umma kwalliyar me ki keyi? kaka ce ta
shigo tambayar me kike mata?? harara na zabga
mata sannan tace. kwalliyar me take? kwalliya
za'a kaita gidan mijinta ko zaki hana? ba zan
hana ba,amma kin san kafata kafarta ke ma baki
isa ki hana ba vaba dan Allah kiyi hakuri karki
haka saboda maganar mutane to wannan
bankaddaddiyar yarinyar ce take gudun maganar
mutane shegiya.
"ni ba shegiya bace kije can ki nemi shegiyarki
mutum ko baka saka magana da shi ba sai ya
saka dan gulma an girma ba asan an gir........."
bugun da ya sauka a bakina ne yasa nayi shiru
da ban shirya ba umma tayi saurin shiga
tsakaninmu tana bawa vaba hakuri sannan ta vita
umma ta juyo wajena,"haba nana ke kullum kin
fison ki sani cikin bakin ciki,baba kakarkice amma
kin maida ita kamar yar aikin gidanku bakya
rangonta mata,kuma maganar ta fiya kin san da
bakin ki kukayi magana da shi kice sai nayi sati
daya zaki tawo ba sannan kuma yanzu ki zo da
wata maganar, kawai umma kice ba kya son nazo
gidanki,saboda kin auri mai kudi' haba nana har
akwai wani arziki da zan samu wanda ya fiki
naba saboda irin son da nake miki yasa vaba
take jin haushina,nana ki tausaya mu rabu da
vaba cikin farin ciki,kin ga yanzu in nace na
amince zan tafi dake yau vaba ranta zai baci kar
kiyi fushi dani ni nayi miki alkawarin rana ita yau
da kaina zan zo in dauke ki kiyi hakuri"tana
magana tana shafa kaina haka yasa zuciyata ta
sauko. shi kenan umma Allah ya kaimu kuma kin
san babba ba abincin ta take ba ni ba in kuma so
kike inyi iskanci na samo to"
Abbagana hausa novels@ facebook.
WAYE SANADI? 8-9 & 10
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.