shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 22 October 2016

waye sanadi? 46---50WAYE SANADI? 46 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.muhdabbagana.blogspot.com Ina gama karantawa kiransa ya shigo na daga tare da yin sallama safiyya kinga sakona? Na gani mene ne? ki gayan inda kike nazo mu gaisa wai kai dole sai ka ganni? Babu dole to tunda babu dole in dai kana da zuciya karka ka kirana ina fader haka na katse wayr muryar momy naji daga bayana “gaskiya kina burgeni safiyya tana fadar haka ta shiga toilet ta dauro alwala bayan ta idar da sallah ta juyo tana kallona safiyya meye yake damunki? Wallahi in baki daina yiwa maza rashin mutunci ba zakizo kiyi dana sani” momy bana son naga namiji yana min Magana koda na minti daya ne na gaya masa ya daina kirana yaki yarda shi yasa na sake gaya masa Magana dan yaji haushi ya daina kirana. Ke a ganinki hakan da kikayi shine mafita? Na daga mata kai to wallahi wannan ba zata zame miki mafita ba shawara ta karshe da zan baki in kin dauka kin taimaki kanki kuma wannan itace shawara ta karshe d azan baki, in har baki dauka ba har abadah bazan kara baki shawara ba kin yarda? Momy ki…….tayi saurin katse ta ban nemi wata Magana a wajenki ba kawai ki ban amsa shi kenen momy na yarda kuma insha Allah in har kika gaya min shawararki zan dauka nayi aiki da ita dan nasan bazaki gayamin abinda zai cuce ni ba ‘ safiyya ki bawa Muhammad dama yazo ya ganki, kai ta dago a razane momy bana son na yaudari mutum dan haka bana sauraran samari.” Okey ke haka zaki zauna ba zakiyi aure ba? Momy waye zai auri wadda bata da uba ni kam b azan batawa kaina lokaci ba, nazo na kamu da son mutum daga baya yazo ya guje ni. Ni dai shawara na baki in kinga dama ki dauka in kin ga dama ki barshi, wayar tace tayi kara kallon momy take wadda ta tsare da ido, dole na dago nayi sallama da sauri ya amsa safiyya Dan Allah ki gayan inda kike” zan turo maka da message ina fadar haka na katse wayar tare da juyo ina kallon momy bude bakina keda wuya kan nayi Magana tace’ to tura masa da text din’ momy ya zance? Okk baki san meh zaki gaya masa ba kika ce zaki turo masa? Na daga mata kai tace sai ki rubuta masa kalaman soyayya tare da alkawarin zaki aureshi zaro ido nayi ina dariya kai momy in na rubuta hakan ai naji kunya na zubar da ajina; au har ma aji ne dake? Kai haba momy me kika dauke nine? Kinga karki shiriritar dani ki tura masa yanzun nan. Abbagana hausa novels @ facebook. [10/12, 9:07 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 47 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Ina tura masa ya kira na gode safiyya gobe karfe biyar zan zo toh Allah ya kaimu ina fadar haka na katse kan na mata magana wayarta ce tayi kara ta dauka tare da cewa Salamu alaikum Abba lafiya klau sun jima suna hira sannan ta miko min wayar abba an yini lafiya? Lafiya klau safiyya ya karatu? Alhamdullilah ai gobe zan zo ganinku gayan me zan tawo miki dashi? Ina dariya nace ba komaii zuwanka ya fiye mana komai Abba, ina hajiya? Mun jina muna hira sannan mukayi sallama momy shine baki gayan Abba zaizo ba? Tana hararata tace ce muku nayi albishir kika mike har dace mana in dai sai kince goro ne to abar albashiri din dan haka na bar maganar sorry momyna ina son allbishir din goro goro har sau biyu daman gaya miki zanyi Abba zaizo kuma gashi ya gaya miki da kansa ni ban so ya gaya miki ba naso ya zo yaga yadda kike wulakanta mutane. Baby yau bakya jin yunwa ne? Me kika gani? gani nayi baki fara mitar inzo muje aci abinchi ba ni kam baran kara zuwa restuarant din da muke zuws ba in dai bamu canza ba bazan kara binku muci abinci ba, saboda me? Bana son wannan kafurin yana damuna ke dai Allah ya gyara miki meh ruwanki dashi tun... kan ta karasa saadiya da farida suka shigo ruki yau azumi kuke yine? Farida ta fada tana kallona sarkin korafi da mita ce ta zauna tana aikin nata wai bazata kara zuwa inda muke cin abinci ba saboda me wajen yana zuba mata ido. Mun fito cikin makaranta muka hadu da saifullahi ya shigo, yana ganinmu ya hau murmushi rukayya fita zakuyi? Kan tayi magana farida tace saifu ba rukayya zaka tambaya ba ga mutumiyar taka zaka tambaya tana magana tana nuna ni wata uwar harara na zabga mata ta hau dariya, sadiya tace lallai farida zaki sha mita yau yace au sadiya safiyya bata son ai mata magaba? Nikam in za'a shekara ana min maganarta bazan gaji ba momy tace tana so a mata hirarka wai kunyarka take ji. Yayi saurin natsowa kusa dani har takakminshi ya gogi kafata yana murmushi yace wai haka safiyya kina san ma.... kan ya karasa na matsa kamar a mafarki na daga hannu na zabga masa mari wata irin kamewa su momy sukayi bana sonka! Bana kaunarka!! Ka fita a rayuwata ana son doke ne? Ya girgiza kai hannunsa yana dafe da inda na mareshi naci gaba da cewa ka takurawa rayuwata na gaya maka bazan taba sonka ba meye ruwanka dani wannan maganar ta zama ta karshe a tsakaninmu wannan marin ka da nayi zanyi maka wulakancin da yafi wannan ina fadar haka na juyo yayi saurin shan gabana na gode safiyya yau naga karshen kiyayya na miki alkawarin daga yau bazan kara yi miki magaba ba har abada amma a yanzu ina neman alfarmanki kiga cikin idona ki gayamin abinda kika gani muryarshi da naji tana rawa yasa nayi saurin dagowa ruwan hawaye ne kwance a cikin kuakkyawan idanun nasa ya saki murmushi ya juyo wajensu sadiya duk kansu ji suke kamar zasu nutse dan kunya. Rukayya sai anjima yana fadar haka ya tafi... na juyo wajen momy bude baki nayi zan mata magana tayi saurin katseni cikin tsawa karki kuskura ki fadamin wata kalma muje inda muka nufa in kuma zaki tsaya marin wasu mazan ne to taja wani dogon tsaki tayi gaba a wajen ma hakan ce ta kusa faruwa. Haka muka kwana babu wanda yayi wa wani magana balle kula wani karfe sha daya abban rukayya yazo, keh ki tashi abban rukayya yazo kanta bata amsa ta fita na fito yana zaune cikin motar abokinsa na karasa har kasa na zube muka gaisa safiyya ya karatu? Mun jima muna hira nace abba aunty rukayya ta daina kulani ina maganar hawaye ya fara zubomin cikin bacin rai ya dago yana kallonta daman fada kike da kawarki? A,a abba laifi tayi min to wani irin laifi ne zaki daina yi mata magana abba in na gaya maka abinda tayi zaka iya dukanta.... Abbagana hausa novels@ facebook. [10/13, 8:06 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 48 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Bana son ki gayan safiyya kanwarkice duk abinda tayi a hankali zaki dinga nuna mata tayi ba daidai ba in kika daina mata magana me kikayi? Maza ki bata hakuri bana son na kara jin haka Ta juyo wajena kiyi hakuri tana fadar haka ta fita tana cewa bari na kira su sadiya to ki bude but ki dau sakonku da hajiya tace a kawo muku" Karfe biyar abba ya tafi muna dawowa momy ta bude ledar da hajiya ta aiko mana da shi katuwar cooler ce cike da soyayyar miya, Bayan sati daya Fitowar mu kenan da momy daga class mota tazo tayi fakin a dai kusa damu bayan motar naga an rubuta element sai daukar ido take kalko daya nayiwa motar na dauke kaina a hankali ya sauke glass din barinsa wata zazzakar murya naji ta doki kunneta mai faranta zuciya tabi ta ratsa duk sannan jikina kamar an watsa min ruwan sanyi na dago kai na kalli inda akai mana sallama idanuwa ya sauka akan kyakkyawan fuskarsa me cike da kwarjini zuciyata ta buga sa sauri, dauke kaina nayi dan zan iya mutuwa a wannan lokacin. Momy ta amsa masa sallamar sannunku dan Allah ina tambaya ne kan ta bashi amsa nace mallam bamu sani ba' da sauri ya juyo yana kallona sai yanzu ya kare mata kallo tsarki ya tabbata ga ubangiji tabbas duk inda ake neman kyau akazo wajenta an gama ganinsa tsaki nane ya dawo dashi daga tunanin dayake muna hada ido na aika masa da harara nayi gaba, cikin kunya momy tace ina sauraronka fuskarshi cike da murmushi yace ina neman wata daliba mai suna safiyya mukhtar tazo daga kano cikin mamaki momy tace kaine wa? Nine muhammad imran salis yau satina daya ina zuwanm nemanta amma Allah baisa na sameta ba, toh amma ka kira wayanta mana nan da nan fuskarci ta canza zuwa damuwa tun ranar da mukayi alkawarin zanzo kullum inna kira wayarta a kashe to kai baka san ta a fuska bane saita waya? Gaskiu ban santa ba, hasalima ban taba ganinta ba kullum nazo makaranyar nan sai an nunamin wasu masu suna safiyya amma inna je sai naga ba ita bace amma kai da baka taba ganinta ba ta yaya in an nuna maka wata ka gane ba ita bace? Safiyyar dana zo nema tana da tsiwa da fada ga kuma bata da kawaye sai mutum biyu sadiya da momy duk wadanda ake nunamin ban samesu da irin halin safiyya ba. Me yasa baza ka tsaya ka kalli yan matan da aka nuna maka ba? Na tabbata yan matan da aka nuna maka suna da kyau kar kaje ka hadu da safiyyar dakazo nema ka tarar da ita wata mummuna kamar hadari ba kalar da kake so ba ya saki murmushi ya daya kara fito da kyaunsa karki manta na gaya miki a waya muka hadu da safiyya, na kuma kamu da kaunarta tun kan na ganta bana zakuntar zuciyata, ina son safiyya a kowanne haki take bara nayi miki a takaixe ko dana tarar da safiyya a keken guragu bata ji bata gani zan iya aureta ki taimaka in kin santa kigaya min nasan safiyya Dan Allah da gaske? in baka yarda ba shikenan sai kaje gaba tana fadar haka ta fara tafiya yayi saurin fitilowa ya sha gabanta Dan Allah ki tsaya ki taimakeni, nace maka nasanta kana nema ka karya tani sai kayi gaba koh zaka samu wanda ta santa kiyi hakuri mutane da dama suna cewa sun santa suyi ta wahalar dani wasu suna karban kudina ni kam ban damu da kudin ba burina na ganta koh jiya sai dana bawa wata kudi mai yawa take cemin bara ta kirata shiru har shadaya ina zaune a waje harna hakura wata zuciyar ta kara gayamin da yardan Allah safiyya matar kace kar kayi zuciya dan haka yau yasa na dawo nemanta kiyi hakuri ki taimakeni ki nuna min saffiyar koh zuciyata zata iya samun sukuni tana murmushi tace tare muke da ita zuwanka ne ya koreta ya zaro ido kamar zasu fadi kina nufin wadda kuke tare ce safiyya??........... Abbagana hausa novels @ facebook. [10/15, 8:21 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 49 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Kwarai kuwa ko kanwar tawa ba tayi maka bane no aunty safiyya ta min sosai fatana ta yarda dani amma baki gaya min sunanki ba, sunana rukayya amma safiyya tana kirana da momy sunan umman tane ni kuma in kiranta da baby, ina fatan zaka iya tuna wata ranan da ka kira ta wata ta daga take gaya maka bata da lafiya. Duk abinda safiyya takeso nima ina so ka karaso na kirata ku gaida. Hannunsa ya hade yana murmushi na gode anty bara na gyara parking ina sallah ta shigo tana zaune har na idar baby ki fito ku gaisa da muhammad momy wanni muhammad kuma? Wanda kuke waya kika kuma yi masa alkawarin yazo ku gaisa momy ni......karkice min komaii kije ku gaisa in kin ga dama koh in kin fita shima ki mareshi tana fadar haka ta mike ta fita, yana jingene jikin motarsa ta karaso ga tanan zuwa kayi hakuri muhammad kasan halin kanwartawa kan ya bude baki yayi magana na fito fuskata hade tunda na fito ya ziba min ido kamar zai hadeye ni har na karaso na tsaya a gefen momy, momy tace imran bari naje na dawo da sauri yace to anty a dawo lafiya, sai da ta harareni sannan ta bar wajen a zuciyata nace momy akwai shiga abinda ba ruwanta maganarci ce ya dawo dani daga tunani" yau Allah ya nunamin safiyya farin ciki ya cika zuciyata safiyya kina farin ciki da ganina? Kamar ba dani yake ba naci gaba da kalle kallena please safiyya ki min magana . Wai to dole sai nayi maka magana ne? Ido ya tsura min can kuma ya hau dariya tabbas safiyyata ce sai yanzu na yarda, harara na mayar masa wacce ce safiyyar taka? Wallahi darajar momy da karatun da kake saminne yasa na saurareka' Ina son mace mai tsiwa da fada kinyi daidai da kalar matar da nake so na kuma ji dadi da naci darajar girman alkurani da momy Allah yasa koda yaushe zan dinga cin darajarsu ya dan matse fuskarchi wanfa yakara fito da kyawunsa. Safiyya ya karatu? Meye ruwanka da karatuna ina fadar haka na juya zan tafi naji an rije gefen mayafina a fusace na juyo ina hararansa meye haka? Da zaka kamanine? Ban gama ganinki ba zaki tafi kya bari anty momy ta dawo karta ce nagudu da kanwarta nayi saurin buge hannunsa da sauri ya janye ina kallonsa nayi mamaki da ban maka abinda yafi haka ba ka kiyaye duk lokacin da kayi karanbanin rike wani abu a jikina zan maka abinda yafi haka, ina fadar haka na juya muryarshi na juyo "i love you safiyya ban ko juya ba na koma daki ina mita momy ta shigo hannunta dauke da manyan jakunkuna ta zuba a gabana tana murmushi baby ga tsarabar ki nace tsarabar me? Iman ne ya kawo miki tsarabar america gaskiya baby kun dace da imran nayi miki murna imran yana sonki tsakani da Allah, dan Allah momy me haka ce miki nayi ina sonsa? Wallahi nayi mamaki da dazun ban mareshi ba kanna karasa momy ta katseni ina tunanin safiyya kin samu tabin hankali har na tsaya tunanin kan abinda na fada meye ya hanaki marinshi to wallahi tun wuri ki nutsu ki tattara hankalinki kina wasa da damarki, momy safiyyarki kike cewa bata da hankali nagaya miki inda kina dashi har baki tsaya kin saurari imran ba sai na gayawa dady muna tare dake nayi saurin dago kai ki rufamin asiri; bazan ruka miki ba momy bana son imran kwata-kwata bana so kuma na yaudareshi dan haka bana so na shiga rayuwarsa yaga kamar na yaudareshi ki gane nufina, naji na gane nufinki nima kuma kin gane nufina zaki iya gayawa imran bakya sonsa amma bata wannan sigar ba ki gyara halinki. Shi kenan momy zanyi kokarin naga na gyara ina wayarki? Tana nan wato shine kika kasheta dan kar yazo koh Allah kuma yayi sai kun hadu ai kya tausayawa imran ko da wuyarda yasha na nemanki ki dau wayarki ki kunna ko zai kira kusha hirar soyayya....... Abbagana hausa novels @ faceebook. [10/18, 8:33 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 50 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Kai momy gaskiya kada ki min haka zan kira abba na gaya masa kullum sai kin sani kuka kina daina kulani, oho dan kinga abba yasa na baki hakuri shine zaki kuma kafa da abba koh? Bata ko bata amsa ba sadiya ne ta shigo a,a wannan kayan fah momy tace yau babban bako mukayi waye babban bakon? Muhammad imran ta zaro ido kamar zasu fadi dan Allah ruky da gaske kike imran ne yazo? In de baki yarda ba shikenan yace a gaisheki gaskiya naso ganinsu tare da safiyya yaushe zai dawo? Ina hararanta nace bansani ba meye ruwana da dawowarsa, ke din baki da hankali safiyya baki san kanki ba kina abu kamar wacce bata taba sanin hanyan makaranta ba wallahi in naga saifullahi rasa inda zan sa kaina nake dan kunya harya gane daya ganin sai ya canza hanya. Hmm sadiya baki kaini jin kunyar saifullahi ba, jiya ina kokarin guduwa muka hadu nama rasa ya zance masa wallahi sadiya ga mamaki babu wani abu a fuskarsa muka gaisa har yake nuna min budurwansa yarinya kyakkyawa me hankali da kin ganta babu alamun fada a tattare da ita kai amma ruky naji dadi Allah yasa ya aureta a fusace nace kune wahallalu kuna son shiga abinda bai shafeku ba. **** **** **** **** Tunda mukazo gongola babah take cikin damuwa musamman in ta shiga dakin wata tsohuwa kullum sai ta tambayeta amma saitace bata babu komai yau ma fitowarta kenan daga dakin dattijuwa da babu wata magana a tsakaninmu in ba gaisuwa ba na shigo dakin da muke kwana na tarar da babah zaune babah ki gaya min me yake faruwa yau watanmu daya kullum in kuna magana sai kutayin yaren da bana ji meye yake faruwa ki gayamin gaskiya tun da mukazo kullum kina cikin bacin rai dan Allah ki gaya min gaskiya ta dago fuskarta wanda idanuwanta cike da ruwan hawaye tace babu komai rakiya kawai suna fadamin meyasa bamu zuwa musu haba babah me yasa zaki boye min gaskiya in har wannan hausin sukeji yaci ace sun fada mana tare da harshen da zan fahimta rakiya ki bar shiga abinda babu ruwanki. Muna cikin magana mallam maso ya shigo rakiya ta juyo wajensa dan Allah mallam ka gayamin me yake faruwa, rakiya me kika gani? Ya tambayan yana kallon babah , kullum in babah ta shiga dakin wannan matar sai ta fito tana kuka kuma sai filatanci sukeyi me dalilin? Babu komai rakiya kawai tattaunawa sukeyi. Abbagana hausa novels @ facebook
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).