shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 10 October 2016

WAYE SANADI?? 21____29

WAYE SANADI? 21 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz ihun data ji na saki ne ya sata katshe maganar "dole ne sai na gode masa wallahi in dai sai nayi masa ne kar ya ban ni kawai ki mai dani dangin babana,tunda ke bakya kaunata ina maganar ina hada kayana "ki mai dani dangin babana, ita ce kalmar da take yawan yi mata ciwo a cikin kunnenta ganin zan fita daga dakin yasa tayi saurin rike hannuwana "nana yanzu ban isa nayi miki fada ba to tunda haka ne nayi miki alkawarin duk abinda zaki bazan kara yi miki fada ba kiyi hakuri ki zauna tana fadan haka ta fita, washe gari karfe tara da rabi na shirya cikin farar doguwar riga me adon duwatsu tayi min kyau sosai takalmina milk colour high hills na jawo durowa na dau glass dina fari siriri na dora nace yau dai bara na dau wayata. na fita dakin umma na fada cewa zan tafi makaranta gashi inji daddy ya shigo kina barci dubu biyu ta mikon na juya na fita kai tsaye wayen motata na nufa sai daukar ido takeyi me kyau 2007 fara sol maryam na hanga tana jiran direba na shiga na bata wuta na tafi nayiwa maryam bye bye wata uwar harara ta zabgan nayi mata murmushi na fita jina nake cikin nishadi mara misaltuwa in da muka saba daukar sadiya nan na tsaya na san tana hanyar fitowa. waya tace naji tayi kara alamun shigowar message ne suka shigo har guda uku, nana me yasamu wayar taki tsawon kwanaki a kashe dayan kuma akace: nana duk inda kika shiga cikin duniyar nan ba zaki guje min ba mutum baya gujewa kaddararsa muna tare har abada wani kuma yace; ni nasan muna tare gara ki tsaya ki fahimce ni duk inda kika shiga imran mai nemo kine. ganin sadiya a sanyaye na bude na fito zuciyata cike da tunani baki ta saki tana kallona har na karasa "meye haka kin wani saki baki sai kuda ya fada miki sufy kice yau ke kike jan motar to ko ban dace ba no wallahi ban taba ganin macen da take jan mota tayi mata kyau ba sai ke gaskiya kin dade fitowa fa darajarmu a B.U.K kinga kinzo mu tafi lokaci yana tafiya muna shiga kira ya shigo wayata sufy kina jin calling "sady lamarin wannan me kiran nawa yana bani tsoro ban gane ba "wrong number yayi ta kirana nafa gaya masa wrong ya kira amma kullum sai ya kira har kiran sunana yake abinda matukar mamaki kuma yana tsoratani". Abbagana hausa novels @ facebook. WAYE SANADI? 22 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz kin ga message din shi bayan ta gama dubawa ta dago tana girgiza kai gaskiya shawarata kawai karki kara gayawa mutumin nan magana inkina son kanki da arziki dai anyo ko mutum ne kibi a hankali dan ya rabu dake duk lokacin daya kiraki ki daga kuma kar kice zaki masa rashin kunya "sadiya wallahi har tsoron wayar nake ni kawai yarda ita zanyi na huta ke waya gaya miki in kin yar kin huta a yani duk inda kika shiga kuna tare kawai kawai ki dau shawarar dana baki shikenan sadiya na gode tunda muka shiga makaranta ake kallonmu duk inda muka shiga nuna mu ake har mukayi parking muka fito sufy kallo ya dawo kanmu duba ki ga mutumin naki na juya ina kallon ina ta nunan saifu na hange shi zaune da abokinsa duk suna kallonmu muna hada ido ya sakarmin murmushi ya dagan hannu fuska na hade hannuna biyu nayi masa umbola naja hannunta muka tafi muna shiga class sakon m.yusuf ne ya same mu na same shi a office sadiya zaki raka ni gaskiya kawata bbu inda zani kawai kije ki dawo bani wayarki nayi game ban koyi sallama ba na shiga in da kai tsaye nace "gani" nana safiyyya mukhtar ki zauna mana ina da abinyi to nana ina maganar mu ta kwana ban dau maganarka a bakin komai ba tunda ba ita ce a gabana ba ina na riga haba ka amsa bana sonka dan ba soyayya nazo yi ba nana saffiya nima bance muyi soyayya ba aure nake so muyi sannan ina sonki please ki taimaka ki karbi soyayyata kanan......... kan ya karasa nayi ficewata sadiya na tarar akan mota na har kin fito? to kwana zanyi wallahi sadiya zan rufe idona na zabgawa malamin nan rashin mutunci,ki dai bi a sannu tun dazu nake kiran number taki shiga sai yanzu......"Assalamu alaikum sunana sadiya dawa nake magana ke baki san dawa kike magana ba gaskiya ban sani ba a a towa kike nema? ina neman wanda yake kiran kawata nana safiyya inji meye nufin shi a kanta sannan imran salis,ni dan nigeria ne karatu ne ya kaini america zan kira momyna kira wrong number bazan boye miki ba ina son kawarki taki tsayawa muyi magana ta fahimta kullum sai fada sai zagi ki taimaka ki shawo kanta".gaskiya ka dau babban aiki dan kuwa bauddaden hali gareta musamman akan maza amma ya akayi kasan sunanta?? Abbagana hausa novels @ facebook. WAYE SANADI? 23 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz ran da muke waya da ita kanta kashe naji wata ta ambaci sunanta shine naji nana safiyya bata da kawa ni daya ce kawarta nace maka wani irin hali gareta? ita fa yanzu.ta daukeka a matsayin aljani kafa bata tsoro sosai" yauwa sadiya naji dadin wannan labarin kuma zan so ace kin boye mata cewa baki sanni ba karki nuna mata kin yi waya dani kuma dan Allah kici gaba da tsoratar da ita kanni aljanine sannan ina so ki dinga gayan wani abu daya faru akanta wanda kike ganin zata kara tabbatarwa ni aljanine shikenan imran zan yi maka kokarin okey na gode sadiya nafi wata uku ban ji wayar aljani nan ba wanda a wannan lokacin shekara ta biyu a makaranta yau muna zaune da sadiya da kuma sabuwar kawarmu mai suna rukayya wanda nake kira da momy waya ta tayi kara nasa hannu na dauka na shiga uku sadiya aljani ya dawo waye kuma aljani? inji rukayya to kinga ki nutsu ki daga to sadiya ya zance kiyi masa sallama hannu na yana rawa na daga cikin shakewar murya nace salamu alaikum kamar na fashe da kuka ya amsa wa alaikissalamu wata zazzakar muryace ta amsa nana saffiya ya gida ya karatu nasan yanxu kina makaranta ko? sufy kinyi shiru kimin magana Dan Allah ka gayan waye kai kana tayar min da hankali "sunana imran kuma gaskiya ni aljanine kar kuma kice zaki ji tsorona zan dinga kiranki karki tunanin kubuta daga tarkona yana fadan haka ya katse, sadiya naga ta kaina kuna jin maganar da yake fadan wai kr meye haka kiyi abinda nace miki dan ku rabu lafiya ko class ban koma ba nayo gida lafiyar ki nana? umma kaina ke ciwo Allah ya sauwake to kije ki kwanta na shigo miki da abincinki ina shiga na kwanta ina ta tunani naji wayata tana kara cikin dauri na daga nayi sallama. ke baki iya gaisuwa ba ya fada cikin wata katuwar murya kayi hakuri yanzu zan gaisheka daman ke bakya gaida kowa koh hantar cikina ta kada waye ya gaya maka? kina tunanin waye ya gayan ko? karki manta ni fa aljanine karkiyi mamakin ganina zabura nayi na mike ina kallon dakina dan Allah yanzu kana ganina? Abbagana hausa novels @ facebook. WAYE SANADI? 24 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz au kin dauka wasa bara na tabbatar kiga shaida da gudu na kara bakin kofa dan Allah kayi hakuri barrister ki nutsu to na nutsu in kina so mu shirya duk safiya ki dinga gaida ummanki da mijinta da kuma abokiyar zamanta kin ji, naji wallahi zan dinga gaishesu to ki tashi kiyi sallah,nima yanzu zan tafi makka zanyi sallah ban san lokacin da bakina ya furta a hirgi zaka? wane jirgi minti biyar zan isa in kuma zaki mu tafi,zubewa nayi ina bashi hakuri dan Allah kayi hakuri yanzu zanyi sallata to da kin idar kije kiyiwa umma aiki ina kallonki kan nayi magana ya katse wayar da sauri na mike nayi toilet ina idar da sallah na mike na fito umma in kina da aiki ki kawo nayi miki cikin mamaki ta dago kai tana kallona umma kinyi shiru zuba min ido tayi"nana ban da aiki ke da kanki yake ciwo na gama komai kije ki kwanta ki huta kamar na saka kuka na juyo na dawo dakina nasan yanzu yana kallona kuma gashi naje tace bata da aiki haka na yini ranan daidai da wanka ma kasa shiga nayi ina tsoron karya ganni ni gashi fitsari ya cikan mara tunda na dawo nake son na kasa tsungunawa nayi, wata zuciyar tace naje toilet din umma nayi imran kinje yana ganinki haka hawaye ya shiga bin fuskata wayata na dauka na kira sadiya sufy ya gida? sadiya ki taimaka min duk motsin da zan aljanin nan yana gani na me kuma ya faru? fitsari ya cika min mara na kasa zuwa yace yana ganina kan tayi magana kudina ya kare wayar na cilla kan gado tana fadawa aka kira da sani na dauka ina tunanin sadiya ce number shi na gani nan da nan jikina ya hau rawa hannu na yana rawa na dauka sufy kije kiyi abinda zakiyi a bandaki zan rufe idona ba zan ganki ba kuma ina ganin bugawa da kikawa sadiya sannan karki kara kirana da aljani ki kirani da imrana sunan da mahaifina yayi min hudu ba dashi dakyar na iya cewa to karki kashe wayar jeki da ita da gudu na mike nayi toilet dan Allah ka rufe idonka zan tsunguna"bara naje london na kai sako kan kiyi amma karki katse min waya minti uku zan dawo cikim murna nace to na gode. washe gari muna zuwa school na fada jikin sadiya hannuna ta kama muka fito cikin motata muka koma har da momina "sufy wai lafiyarki kuwa??? Abbagana hausa novels @ facebook. [12:10pm, 7/11/2016] Md: WAYE SANADI? 27 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Yana zaune kan bencin sadi na karasa fuskata a hade dai dai lokacin motar daddy ta shigo a,a safiyya ya kuka zauna anan ungo ki bude sit room a dole na karba na bude shiga nayi na samu kujera nayi kwanciyata ganin shiru ban fito ba, ya sa saifu ya shigo, nana kefa yake jira na juyo ina masa irin lalataccen kallo,na zata shima shigowa zayyi bayan ya kai masa ya dawo ya zauna "nana ya jiki? Naji sauki meye kake kirana zuwa nayi na duba ki to kayi kokari na mike zan fita saifu wannan zuwan yazo na karshe a gareka naga kana kokarin shiga min rayuwa ka sauka lafiya. Dan Allah safiyya karki tafi ina son gaya miki wata magana 'saifu na tsane ka sako daya ta hada mu to amma kaci darajar taimakon da kamin jiya ina sauraronka "safiyya kalmar da kika gayan a yanzu ta kara raunana zuciyata amma duk dahaka zan gaya miki ciwon da ke damuna cikin zuciyata,safiyya ina sonki sonki ya dade cikin zuciyata please ki taimakan ki.....' Kan ya karasa na daka masa tsawa baka da tunani saifu me ka dauki kanka dan na baka dama kake so ka wuce goda da iri, to nutsu kaji bana sonka ba kuma zan taba sonka ba na juya zan fita na juyo maganarsa naji bazan daina sonki ba, kuma zaki gane ni din masoyinkine zakiyi nadama sai lokacin da damararki ta kare, ban jima da shiga gida ba sadi ya shigo dauke da manyan ledodi biyu gashi inji bakinki yana kokarin ajiyewa a gabana na daka masa tsawa me yasa ka karbo mayar masa ba,a so, kiyi hakuri ya tafi banza kwadayayye sai kasan yadda zakayi dasu kwashe daga gabana kaine maye kaje kayi taci, sadi yi hakuri ajiye kayan ka tafi bayan fitarsa na juyo ina kallon umma me zaki yi da kayan? Nana kiji tsoron Allah yanzu sadi bai haifeki ba,kike daka masa tsawa. Kan nayi magana kaka ta shigo umma ta mike da sauri ta tarota na juyo ina kallonta na girgiza kai" haka kika kara tsufa dan Allah ki mutu mana" yi min shiru mara kunya bazan mutun ba in raina yana hannunki ki kasheni ina dariya nace bazan zauna a gidan ba kinji abinda ke daya ga kayan dubiya na bar miki tana dariya tace surukin nawa ne ya kawo. in kina sonsa na bar miki bara na tafi islamiya nayi waje. sati banje makaranta ba ina kwance daga ni sai shimi naji shigowar abba kai tsaye cikin dakina nayi saurin mikewa karsowa yayi yana murmushi zama yayi gefen gado my lovely sister kin kara kyau ya kawo hannu zai taban fuska ban san dana doke hannun ba. Abbagana hausa novels @ facebook. [12:10pm, 7/11/2016] Md: WAYE SANADI? 28 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Meye haka kamar ba musulmi ba zaka shigo dakina har kayi kokarin tabamin jiki an gaya maka ni yar iska ce irinka ba....kan na karasa zabgan mari baki da mutunci ni zaki daka har ki kirani da dan iska za kici ubanki sai zaman gidan nan ya gagareki dan kina da kyau shi yasa nake lallabaki tunda na dafe wajen da ya maren na tsaya kamar an kafe ni ya juya ya fita karar mota ce ta dawo dani daga tunani nayi saurin fitowa har ya shiga daki bako sallama na dan na kaina ina kuka a gigicd ya juyo lafiya safiyya? Wani abun akayi miki? Cikin kuka nace dan kane ya mareni kuma Allah bazan yarda ba khalifa ya kwalawa kira ya shigo da sauri a fusace yace kai ka mare ta? Mari kuma daddy? Me ta min da zan mareta sai dai ko abba naga ya fito daga barinsu shi ya mare ki? Na daga kai safiyya meya hada ku? Dakina ya shiga ya kai hannu zai taban fuska ni kuma na doke hannun shi ne ya maren khalifa maza kira min shi tare suka sako kai kai abba me tayi maka ka mareta baiwarka ce? Daddy rashin kunya tayi min kai bakaji kunya ka kai hannu zaka taba jikinta ba? Ido ya zaro daddy sharri..... Mutumin banza yi min shiru ka juya ta rama marin da kayi mata ka kuma bata hakuri dady wannan yarinyar zan bawa hakuri har kuma ta maren daddy kar ka min haka in da ka shiga ka mareta har dakinta haka zata rama kan yayi magana na daga hann na zabga masa mari a fusace ya mike yayo kaina yaji muryar daddy in ka kuskura ka taba ta ranka zaiyi mummunan baci, kiyi tafiyarki safiyya ina shigowa naci karo da umma ina ki kaje? Umma naje dakin mijinki ko bakya so ina zuwa? Ina fadar haka na shige daki a fusace ya shigo dakin momy daman haka daddy ya zama kan wannan agolar maryam tayi karaf yaya abba ka dan ka gani sa,ar daddy kaci ba bai doke ba ni kama har dukana yayi a kanta mommy ta juyo tana kallonsa abba ni kaina sai da yarinyar ta maren sau biyu baice komai ba wata irin zabura yayi momy ta mareki? Kamar ka gani, wallahi momy sai nayi wa yarinyar nan mahaukacin duka sai dai daddy ya kashe ni.yaya abba har mota daddy ya sayi mata mu da umma sai dai direba ya kaimu. Abbagana hausa novels @ facebook. [12:10pm, 7/11/2016] Md: WAYE SANADI? 29 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Ba zan sai muku motar ba in kudinkune na gani kai kuma da kake kawo zaka dake ta to bara kaji na gaya maka wallahi duk ranar da kayi gigin dukanta to kan na dawo ka bar gidan nan kaje ka nemi wani uban, Nafi kwana biyu ban hadu da abba ba dukkan suma ban hadu dasu ba yau ina zaune a falon umma khalifa yayi sallama ya shigo sannu da hutawa kaima sannu ina umma? Tunda ya fara magana ban dago na kalleshi ba sai yanzu tana kicin jin muna magana yasa umma ta leko khalifa ne? Bayan sun gaisa ta juya zubo masa abinci su sadiya ne sukayi sallama nayi saurin mikewa momy kamar a mafarki ummi fito ga sadiya fitowa tayi tana murmushi khalifa ya mike nana na dawo anjima okey khalifa na gode. Budurwar aljani meye labari? Na juyo ina harararta ban san rashin mutunci,saurayi ma n mutum baya gabana wai dan Allah yana ina? Oho masa momy tace ki dai bi a hankali mun jima muna hira sai karfe hudu suka tafi na daga rakasu na hangi abba a garden yana ganin dawowata ya taso kina agola har kika samu damar marin uwata, to wallahi ki shiga taitayinki duk ranar da tsautsayi ya kaiki kika kara karanbanin marin uwata sai kin raina kanki sai kace gidan ubanki ina murmushi na juyo mukayi ido biyj ita agolar da kake magana akanta tafi uwarka matsayi bare kai ina yi maka tuni kan maganar ubanka duk randa hannunka ya taba fatar jikina kasan wani uban gara ka zama ne lallabani dan kusan mi yanci wajen uban naka, ina fadad haka na juya ciki. Ina dakin umma ta shigo da murnarta nana Alhaji ya biya min makka babu wata murna dana nuna nana ki shirya kije ki gayawa baba da malam su zo suyi mass godiya umma meye abun zuwa godiya? Kema in na isa dake kije ki masa godiya tana fada ta fita sai washe gari na shirya da yamma tana falo na fito umma zanje gidan kaka tun jiya sai yanzu ta saki fuska to ki gaisheta kuma ki shiga kiyi masa godiya banyi musu ba na shiga yana cikin daki safiyya unguwa zaki? Fuskata a hade nace zanje na gayawa su kaka biyawa umma makka, ka ban kudi nasha mai dubu goma ya ban a bakin layin mu naga khalifa ina zuwa? Zanje gidan kakarmu ne bude motar yayi muje nayi rakiya. Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).