TANA TARE DANI 97
TANA TARE DA NI... PAGE 97
BY MIEMIEBEE
Hawayen jin dad’i ne suka soma tsiyaya daga idanun Ummimi tana meh godiya wa Allah azuciyarta, mahak’uri mawadaci, ayau ta tabbata wannan zance hak’urin ta be tafi in vein ba tunda finally Anas nata ya dawo gareta. Har a yanzu Anas be raba jikinsa daga nata bekuma bar kukan dayake ba, hannayenta ta aza a bayansa a hankali tare da sake tightening hug d’in “Alhamdulillah, Allah na gode maka daka dawo min da Anas d’ina, kabar bani hak’uri Babna ba abinda kamin is okay kaji? Stop crying.”
“Its not okay Ummimi nasani I’ve been treating you bad har kuka na saki kiyi hak’uri dan Allah if only nasan kwatan abinda kikayi going through kafin kika haifeni believe me wallahi barin tab’a k’untata miki ba” yayi breaking hug d’in tare da riqo hannayenta cikin nasa “I’m truely sorry mother” a hankali ta raba hannunta daga nasa ta sa ta share masa hawayen da yakeyi “bakayi offending d’ina ba Babana, nice ya kamata nan in baka hak’uri. *I love you so much Anas.”*
*“I love you too Ummimi you are the queen of my heart”* ya sake hugging nata dad’i sosai Ummie taji kamar ta cinye su finally! Anas yayi accepting Ummiminsa.
“Babana ya condition na Fannah?” Ummimi tayi maganar cike da damuwa.
“Ya condition nata please Anas” Mami ta mara mata baya wani sabon kukan yasoma musu wajen seda Ummimi tajasa kan kujera ta zaunar dashi “haba na miji dakai kake wannan kukan Anas gaskia beyi ba agaban Mami fah? Me kakeso tace? Surukin nata rago ne komeh? A’a gaskia bana so” tasa hannu ta share mai hawayen. “Kukan ya isa haka” “Ummimi I can’t watch her suffering like this, kuyi wani abu please.”
“Zaka iya komawa ciki?” Da sauri ya girgiza kai “barin iyaba barin iya juran kallon Fannah tana shan wahala haka ba kuma ba abinda zan iya yimata to ease the pain ba, I can’t Ummimi.”
“Shhh! Ya isa in shaa Allah zata sauk’a lafiya.” ta kwanto shi jikinta tana sbubbuga bayansa. Sede hawqyen da Anas yake yanzu ba dan Fannah bane, hawayen dayake na missing d’umin jikin mahaifiyarsa ne wanda ba abinda yakaisa dad’i a fad’in duniyan nan, bare iya tuna when last yajisa comfortable daga anriqe shiba se yau.
*_our mothers are priceless lets respect them ba abinda zamu iya musu wanda zekai koda k’wayan zarrah ne daga cikin abinda suka mana. D’aukan ciki, rainonsa, haifan mu, shayar damu, tarbiyyattar damu d.s they’ve made alot of sacrifices just so to make us happy, they don’t give a damn in abinda zasuyi ze cutar dasu as long as it’ll make us happy toh zasuyi, Allah yabamu ikon kwantata masu so kamar yadda suka somu, Allah musu albarka ya saqa masu da gidan aljannah AMEEN_*
_2 hours later..._
Anas ne tsaye akan Fannah data kasa haihuwa tin tin d’azu yanzu da labourn yad’an sauqa ne tasamu hankalinta, zufan dake akan goshinta yasa hanky ya share yana me mata sannu. “Flower I’m here kinji you can do this” kai kawai ta kad’a mai.
“Habeebi I can’t barin iya ba.”
“Sure you can Sweetheart” yayi pecking goshinta.
“Please karka sake tafiya kabarni Habeebi stay with me please.” ta sake matse hannunsa dake cikin nata tana hawaye. Badan yanaso ba ya gyad’a mata kai alokaci guda labour natan yasake hitting nan aka shiga new chapter again ihu da kukan da take yafi nada data wani damk’o Anas seda ta yayyak’ushe shi da zafin yazo yayi mata over batasan a lokacinda tafara ja mai Allah ya isa ba duk yana ji yasan ba’a cikin hankalinta take ba se sannu yake mata chan ma tace yafita mata daga d’aki batason sake ganinsa haka sukayi spending numerous hours cikin labour room suna abu d’aya.
_3 hours later exactly 3:20PM_
Bayan azaba da wuya da kuka da zagi da yak’ushi Flower tasauk’a lafiya tasamu ‘yarta wacce take nan tubarkallah. Wani irin nunfashi ta saki, seji take kamar an sa mata sabon rai, “Flower you did it, Hanan is finally with us” yayi pecking nata a goshi “thank you so much Sweetheart Alalh miki albarka for this blessing I love you so much.”
“I love you too Daddy’n Hanan, I love you so much” tayi maganan da murmushi kwance akan fuskarta. Daidai nan nurse ta miqo ma Fannah Hanan dake weighing 6 pounds, lullub’e take cikin pink shawul kamar a saceta a gudu. Yarinya k’atuwa tubarkallah, farinta da kamanninta sak na Daddy’nta yanayin gashinta kuwa koba a tambaya ba ansan na Mammynta ne, gashi har kan goshi da kuma kumatu ruwan zamzam da dabino Anas yabata how cute and adorable suna kallon Hanan insu, daga nan Anas ya amshe ta “Flower this is just my carbon copy ana cewa muna kama da Amal but not as we do da Hanan I love our baby Flower most of all I love you.” Murmushi tamasa “you’ve once promised me ni zanyi naming baby’nmu ko?”
“Yes Flower and zan cika promise d’in yau gata kiyi mata hud’uba” amsar ta tayi ta mata wasu maganganu a kunne sannan a fili tace, “Allah raya mana AYSHA.” Cike da rashin fahimta Anas ke kallonta “Aysha kuma Flower? Kin fasa Hanan? Your dream name?” Kai ta kad’a mai ko kad’an “My Lion sunanta Aysha takwaran Ummimi but na mata alkunya da Hanan dashi zamuna kiranta ka gane?”
“Dagaske takwaran Ummimi ce?”
“Yes Sweetheart.”
“Wow! this is great news Allah raya mana mahaifiya ta” duk sukace “ameen” sede wani gudu ba hanzari ba kan Fannah ya d’aure ta d’au Anas will freak out inyaji batun sunan amman kuwa se gani take kamar ma yafita jin dad’in sunan Hanan.
“Habeebi kasani cikin rud’ani, nad’au barakayi accepting asalin sunan Hanan as Aysha ba.”
“Mesa barinyi ba Flower bayan Ummimi mahaifiya ta ce, kamar yadda kika sha wahala kafin kika samu Hanan haka nima tasha kafin ta sameni, I never knew haka mothers namu suke shan wahala da ace inada masaniya akai wallahi da ko na second barin tab’a b’ata wa Ummimi rai ba, kamar yadda barin bari for once Hanan ta miki ba daidai ba nima barin sake yiwa Ummimi ba daidai ba I’ve asked for her forgiveness earlier we are all good.” dad’i sosai taji maras misantuwa.
“Dasgaske Habeebi?” Ya gyad’a mata kai. “Today is indeed the happiest day of my life Habeebi, kai da Ummimi kun shirya ga zuwan Hanan omg! I feel like a queen” daidai nan Hanan tad’an yi miqa tare da bud’e idanunta se gasu nan blue sak erin na Daddy’nta atare sukace “she has blue eyes too.” sekuma suka murmusa.
“Habeebi Hanan nada blue eyes.”
“Yes Sweetheart mena had’a rai kuma Flower?”
“Eh mana ni insha wahala in haifeta kuma ta d’au kominka, farinka, face naka eyes naka ni kawai gashi na ta d’auka.”
“Ohh common Flower nan gaba kika sake haihuwa masu kamanninki zaki haifa in shaa Allah.”
“Wa ze sake haihuwan? Ni? Chab!”
“Eh mana we will have like 10 kids.”
“Engine d’in yara ka miyar dani ko meh?”
“LOL but jokes apart we will have like 4-5 kids ba? Please say yes Flower.”
“Muddin you’ll be the strong Hyena I know we can have like ten kids in kanaso” tayi maganan tare da kashe masa ido daidai nan Ummie dasu Mami suka shigo Ummimi ce a sahun gaba ita ta fara amshe Hanan “wow tubarkallah sannu fa uwata” nan tasa mata albarka sannan ta miqa sauran suma sekuma sannu da sukayi wa Fannah wanda ya biyo baya.
“Ummimi ga Aysha fa.” Cewar Anas.
“Aysha kuma aina?”
“A hannunki” Fannah ta amsata.
“Kai tun ayau na zama kaka kun fara min tsiya wato koh?”
“Am serious Ummimi Fannah named our baby after you sunanta Aysha but za’a na kiranta da Hanan.”
“Ummimi kar kijisa mu biyu mukayi shawaran muka bata sunan kuma ma shi ya fara kawo shawaran.” Hawayen jin dad’i Ummimi ta soma “barin iya muku godiya ba Anas da Fannah, addu’a na d’aya ne Allah ya barku tare, ya k’ara k’arfin soyayyan dake tsakaninku yacigaba da kawo mana zuriah d’ayyyiba yakuma raya mana Aysha me suna na” duk suka amsa da ameen. In next Flower ta samu twins kuma Ummie da Mami zamu sa ko Flower? Ta gyad’a mai kai tana murmushi.
“Wai Anas akwai son baby girls inkuma maza ta samu fah?” cewar Ummie su Mami se dariya suke.
“Fine se asa musu sunan Baba dana Abuu.”
Allah kawo masu albarka Habibti Mami tayi maganan tana shafa kan Fannah. Ameen Mami I love you”
“I love you too” Anas ganin haka yayi gun Ummimi da Ummie shima tare da hugging nasu all “I love you momies. Kin d’au ke kad’ai kike da mama ne anan?” Ya juyo yana kallon Fannah kaman d’an yaro “naki d’aya ne nawa har biyu infact har uku tunda ga Hanan.” Duk suka kwashe da dariya banda Fannah dake dariya kad’an kad’an dan azabah.
_some hours later... A gidan Mr. Fauzi_
“Ummimi wai ina zaku kai kayakin Flower ne?”
“D’akinta chan zata koma da kwana har se ta fita daga arba’in.”
“WTF!” Yayi exclaiming ba tare da yasan lokacin daya fad’a hakan wa mahaifiyar saba.
“Meh kace Anas?” Ta zaro ido cike da mamaki. Kai yasoma sosawa “I mean Where’s The Fork da Amal tashigo dashi d’azu?”
“Zakamin irin na Yusuf kenan kad’au bansan meaning d’in WTF d’in bane koh? What The Fuck ko ba haka ba?” Kallon Ummimi yake cike da mamaki sekuma ya tuna tayi zaman tsawon 14 years a k’asan turawa dole tasan abubuwa irin haka. “Uhmmm” yasoma shafa gemunsa “Ummimi please kubarta anan.”
“Kamar ya abarta ne wai Anas?”
“Muna kwana tare.”
“Chankwad’i!” Tayi maganan tana tafa hannayenta “katab’a jin inda mace ta haihu takuma cigaba da kwana da mijinta? Dan ma Mami batace zata kaita chan gida suyi arba’in ba kenan kake wannan magana.”
“Haba mana Ummimi please kubarta anan” da k’yar d’in k’yar Ummimi ta shawo kan Anas ya yarda Flower takoma d’akinta badan yanaso ba dan Ummimi keso. (Mother’s Love)
Haka nan tun daga ranan da aka samu Hanan akayi limiting tarayyan Anas da Flowersa abin har rashin lafiya yakeson sasa shida ya saba kullum tare da Flowersa yau an rabasu na k’arfi da yaji a wuni befi su had’u na ‘yan mintuna ba, abin damunsa yake sosai ga yadda dangi daga Bama suka rik’a zuwa suna zuba k’auyenchi a gidan. Ahaka har Allah yakaisu ranan suna inda dangi da mutan arziki suka halarci bikin sunan Hanan. True fans na *_TANA TARE DA NI_* dam cikin gidan Mr. Fauzi musamman ma ‘yan *_MIEMIEBEE NOVELS GROUP_* se zuba k’auyenci suke gun security door kowa tace se k’ofa ya kira sunanta haka sukasa Amal agaba tana registering sunansu. Su Mrs Shamsur ne a b’angaren kitchen ansha bidirin suna wane na bikin aure kowa yasan Mr. Fauzi da son kashe kud’i ba sena tsaya lisafo abubuwan da akayi a bikin sunan ba ande ci uwar naira thast all (LOL) anchi, ansha anyi pictures, Fannah da Baby Hanan nata sun ci gifts ba dama.
Tunda Fannah ta haihu Ummimi da Mami ke kanta, Ummie na achan gida dasu Abuu sede in ta wuni musu takoma, su Amal anzama Aunty rawan kai ya k’aru a yau Ummimi ta koma gida itama, ya rage Mami kad’ai ita kanta Fannah missing Habeebinta take ji take kamar taja 40 days d’in yayi ya k’are takoma gun Lion nata. Kamar yadda al’ada ya tanadar seda Fannah tayi 40 days cur! Sannan Mami ta barta takoma d’akin Anas a ranan itama Mamin takoma gida aka ragar da love birds zallah.
_4:25PM_
Daidai dawowan Anas gida daga office kenan meetings hud’u yayi attending yau he is all tired k’ofa na bud’uwa yaga Fannah da Baby Hanan nashi tsaye behind it tasa wani red flow lenth gown me siraran hannu wanda yasha ado sosai, kamar yadda take sanye da jan kaya haka ma tasa wa Baby Hanan jan ‘yar kanti da white socks seda white head band se k’amshi ke tashi a jikinsu take wajen Anas yanemi gajiyan daya tattaro daga office ya rasa ko be tambaya ba yasan Mami ta tafi dalilin dayasa Fannah tafito kenan.
“Welcome home My Lion.” Ta fad’a tana mai murmushi. K’arisawa ciki yayi ya amshe Baby Hanan tare da kissing nata passionately sun d’au tsawon loakci suna abu d’aya sannan a sannu tayi breaking kiss d’in. “I missed you” suka furta wa juna sekuma suka murmusa. “Flower you are looking extra ordinary beautiful I mean you and Baby Hanan.”
“Thank you Honey, muje kachi abinci” tayi maganan tare a karb’e masa jakar laptop nasa sannan suka nufa dining tayi serving nasu, Hanan na a hannunsa har suka gama cin abincin. “Flower amman bake kikayi girkin nan ba.”
“Why do you ask?”
“Sabida I know girkin Ummimi ne wannan.”
Habeebi ba’a iya maka wayo just like Hanan kasan d’azu dana mata wanka na shayar da ita har ta fara bacci fa ina cire maman daga bakinta ta tashi tasoma kuka koda nasa mata sucker nata tak’i sucking sabida tasan ba nono bane, you two ba’a iya muku wayo.”
“Team Blue Eyes kikeji” nan yad’aga Hanan sama yana mata wasa.
“A’a Habeebi a hankali please kasan she is still a baby.”
“Toh Mom Hanan nida bansan zafin haihuwa ba se a fad’amin magana.”
“LOL its the truth ba abinda yakai haihuwa azaba Habeebi.”
“I know Babe tunda har kika jamin Allah ya isa kam ai komai ya b’aci.”
“I said I take it back kaima kasan cikin hayyacina barin tab’a ja maka Allah ya isa ba Daddy’n Hanan.”
“Nima wasa nake gobe tare zamuje office.”
“Kai dawa?”
“Me, you and our Hanan, dama jira nake Mami ta tafi mufara zuwa tare ‘cause I’m missing you guys like hell.”
“In Ummimi ko Mami sukaji na bika office kaima kasan da akwai k’ara’i.”
“Bawani k’ara’in nan you are my wife and this cutie over here” yayi kissing kunatun Hanan “is my daughter whats there? Final discussion gobe zamuje office tare.”
“Yes Sir” ta fad’a tana mai murmushi anan sukayi d’aki.
*© MIEMIEBEE*
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.