WAYE SANADI?
30 MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
Tana zaune tana tsince wake nayi sallama tana ganin shigowata ta saki baki wa nake gani haba kamar a mafarki? Bara na dake ki sai ki tantance na karasa na tsugunna kina lafiya? lafiya klau rakiya tana nan lafiya? Tana lafiya itace ta aikon na gaya miki mijinta ya biya mata makka ki gayawa malam mado yazo yayi masa gosiya wata uwar guda ta tafka naji dadi Allah ya sanya alkairi bara naje na gaya masa nayi saurin mikewa ki bari in na tafi ki shiga sai wani rawar kai kike yar cin uwa ba dole nayi murna ba Allah zai kai yata kasa mai tsarki ki masa godiya kan muzo tare muka fito ta tadda khalifa yayi saurin fitowa suka gaisa ta juyo tana kallona baki da kirki tina tare da mutum kika barshi a waje ko bakya so naga sirikin nawa? Waye surukin naki? Allah ya kiyaye dan ga mijin umma ne kaine abban? Da sauri nace Allah ya kiyaye kiga wannan mugun a motata in naganshi ma zan iya talitseshi baba ta kawo duka. Aike baki da hankali dan Allah ka min godiya wajen alhaji kan muzo.
Tunda muka shiga mota khalifa yayi shiru sai kawai da komawa yake a dakin yafi wata biyar yana kiran wayar a kashe cikin sa,a yau kamar wasa yana kira ta shiga lokaci da aka daga bai san lokacin da ya sauke ajiyar zyciya ba hello wake magana? Da sauri yace sadiya imrana ne cikin rashin sani tace wane imran fah? Wanda yake kiran kawarki safiyya oho na gane imran ya garin? Lafiya sadiya kullum wayarki ke da safiyya a kashe tawa matsala ta samu ta safiyya kuma tana klau kawai kunnawa ne bata yi sadiya dan Allah ko zaki sa ta kunna wayarta, zan maka kokarin haka na gode sadiya muna zaune da sadiya a class ta juyo waike dan Allah ina wayarki? Tana gida to saboda me bakya kunnata?? Kawai bana ra,ayin kunnata dan Allah ki dinga kunnawa ina an na kira muyi hira mana kullum waya a kashe ,zan duba'a a dan Allah kimin alkawarin zaki kunna nifa kin damen da magana na yarda ni dai ki min alkawari zan kunna. Tana komawa gida imran ya kirata kiyi hakuri sadiya na takura miki koh? Ba komai imran tambayarki zanyi me safiyya tafi saurara a fannin kida har yanzu baka fuskana, safiyya ba ita kida bai dameta ba burinta saurari kararun alkurani musamman yanzu da take hadda au tayi sauka? Tun yaushe haddar ma tayi nisa masha Allah ina son mace haka na gode sadiya.
Ina kwance ina duba wani littafi na tuna alkawarin da nayiwa sadiya nayi saurin mikewa na dauko wayata na kunna banfi minti hudu da kunnawa ba naji kira dagawa nayi ba tare da na duba ko waye ba muyar suders naji cikin suratul rahman cikin mamaki nayi sallama naji shiru loudspeaker na karo na ajiye a kusa dani ina saurara a hankali na dinga bin kararun yana gamawa naji an kashe wayar da sauri na duba number na ganta wata iri in kokarin kira kiran sadiya ya shigo wa kika samu kiketa waya haka sai kira nake kina busy, uhum sadiya baki san wani abuba saikin fada yanzu wata number ta kirani nadaga nayi sallama naji shiru sai naji an sakan karatun alkurani har surar ta kare tana karewa wayar ta kaste to kibi kiji wayene shikenan zan bi mun jima muna hira bayan mun gama na duba received call na duba nakira number kira daya ta shiga ana dagawa naji suratul fatiha tun ina sallama har na dawo hello,hello amma shiru dan haka nayi shiru ana gamawa na katse abin ya ban mamaki wannan kuma waye? Bayan na idar da sallah nayi shirin iskamiyya dakin umma na shiga umma zan tafi islamiya to nana Allah ya bada abinda ake je nema ameen umma tun daga bakin get na hango m.idris yana dukan makara na karasa ba tare da tsoro ba na mika masa hannu dago kai yayi yana kallona safiyy ki tafi aji yadda kake dukan kowa nima sai ka daken, hannuna ba zai taba dukan abar da nake so ba kije aji naga mal.ahmad ya shiga harara na doka masa tare da jan dogon tsaki nayi gaba ina zuwa kofar ajinmu na tasda mall ahmad yana dukan wata makarar karasawa nayi na mika masa hannu iya karfinsa ya zabgan bullalar ganin ba a dauke hannu ba yasa ya dago kansa ke saffiyya me ya kawo ki nan wajen? Cikin tsawa nace ban sani ba ka karashe dukana na tafi. Baki da hankali zan kara dukanki kina ganin yadda hannun ya fashe wuce aji.
Abbagana hausa novels @ facebook.
[10/3, 9:00 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 31
MUH'D*ABBA*GANA 09039016969
www.abbagana.pun.bz
Allah mallam ba zan tafi ba sai de karasa ganin
na kafe bazan tafi ba yasa yace duka mu tafi aji.
muna shiga na dauko sunayen Allah ina dubawa
naji an kira sunana nayi saurin dago kai kizo inji
mal ahmad yana office dinsa kan nayi magana ta
fita maida kaina nayi ina duba littafi har sai da
ya kara turo wato jin nayi mata shiru ta hau
masifa ,dan wulakanci a nayi miki magana kinyi
shiru me kika dau kanki me kike ji dashi sai kace
yar gidan uban wani gidam ma da ake takama
dashi ai mun san komai zan agolanci aka zo ake
anaso ana kaiwa kasuwa..." saukar mari da taji
shi ya hanata karasawa ba kiyi karya ba zaman
agolanci nazo gidansu aminiyarki maryam sai
kuma nazo nafisu iko da isa har ma da samun
matsayi shi kuma wanda kike haukan a kansa
baya gabana hasalima ni din nafi karfinsa dan ko
ta gefen zuciyarta bai taba giftawa ba ke da
kawarki kuke hauka akansa duk malaman
makarantar nan nafi karfinsu babu tsoron
maganata karatu nazo nema ba hauka a kan
namiji ba, kiyi hankali dani kadan nayi miki kinyi
sa,a bana hada jiki da kowa bare ke kazama ga
sako ki gaya masa ba zan zo ba, in yana da karfi
yazo ya dauken ko ya koren a makarantan mari
na kara zabga mata sai ki hada ki gaya masa ya
rama miki banza me kishi kan abinda bai san
kina yi ba. baki daya ajin suka rude da ihu suna
cikin ihu ya shigo fuskar nan babu imani nan da
nan suka gigice tsawa ya dakawa nadiya meya
kawoki wato kun mai da ajin kasuwa koh?
dukkan ku ku fita daga ajin juyowa yayi ya dakan
tsawa ba zaki fito ba? banyi kifi ba akan me zan
fita ke rashin kunyar daki kewa sauran malamai
zaki min duk wanda na yiwa rashin kunya shiyaja
nikam babu inda zani tashi ki fita wallahi babu
inda zan fita zakici ubanki zanyi maganin taurin
kanki ya juya ya fita a fusace ya dawo na kalli
hannunsa bulala har hudu tashi ki fita na dago
kaina ina malam mun gama magana nace banyi
laifi ba dan haka babu inda zan.... kan na karasa
ya daga iya karfinsa ya zabgan a kaina wata irin
azaba nayi nayi saurin rintse ido ban kuma
motsa daga inda nake ba haka yayi ta zabgana
duk inda ya duken sauri wajen ya dauke duk yan
ajin sun shigo suna bashi hakuri wata irin kara
nayi na mike nayo kansa da hannu daya na
dakeshi ya fadi kan ya mike na karbe bulakar na
hau dukansa da gudu suka fita kiran malamai
dakyar mal. ahmad ya karbe bulalar hannuna a
hankali na bude idona nayi saurin mikewa umma
na gani da daddy sannu safiyya lafiyata klau
umma yaushe na dawo ji nayi duk jikina ciwo
yake, safiyya ki tashi kici abinci gani nayi duk
jikina shedar bulala nan take na tuna da mal.
umar to ya akai naxo gida khalifa ne ya shigo
dake, ki tashi safiyya na daga masa kai daddy
ana kira a fusace waye yake kirana wanda yaxo
Allah daddy duk hakurin da zasu baka kar ka
hakura sai an koya masa hankali shegen
malamai bai san aikinsa ba.
Abbagana hausa novels @ facebook. [10/3, 9:03
AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 32
MUH'D*ABBA*GANA www.abbagana.pun.bz
mikewa yayi ya fita umma ta juyo tana kallon
khalifa kai da zaka bashi hakuri shine kake kara
tunzura shi? haba umma ba kya ganin yadda
yayi mata kice ayi hakuri gara a koya masa
hankali na juyo ina kallon umma me akayi wa
mal. umar? Alhaji ne yasa a kamashi kwana biyu
bana zuwa ko ina kullum sai mal ahmad ya turo
a a kirani na aika masa cewa bazan fito ba.
momy dan Allah meyasa baki leka kin gaida nana
ba, momy ko maryam bata je ba hab..... yi min
shiru ba za muje din ba mara kunya kaja mu ka
kaimu momy kiyi hakuri gani nayi ya kamata kije
ai kasan ni din ban san ya kamata ba, saboda kai
baka da kishina yariny ta mari uwarka amma
kake tunanin naje dubata to ba zanje ba kuma
wallahi ka kara zuwa kamin maganarta sai na
saba maka shashasha mara hankali. daka bakin
kofa taji muryarsa wallahi zahra khalifa ya fiki
hankali kuma in har kina so mu shirya ki tashi
kije ki dubata ya shiga kiran maryam da sauri ta
fito. gani daddy jiya dana tambayeki kinje kin
duba safiyya me kika ce? shiru tayi ya daka mata
tsawa fice waza kije ki mata sannu, yana fita
sukaci karo da abba "daddy sann....." yi min
shiru wato ban isa na saka abu kayi ba ko daddy
yanzu nake shirin shiga to wuce muje tare suka
shigo fuskarsa a hade yace ya jikin? ban ko
kalleshi ba na amsa na wuce cikin dakina. karfe
tara na shirya umma zan tafi karatu to kin
karya? zanyi break a makaranta yau zamu fara
jarabawa to Allah ya bada sa,a dakinsa na shiga
yau zan koma makaranta har kinji sauki safiyya?
naji sauki kasa asaki mal. umar saboda me?
bazan kara zuwa islamiyyan ba kaga ko rike shi
bashi da wata fa'ida. ina shiga na hangi momy
tayi parking tare muka shiga class baby ya jikin
ki naji sauki jiya ina ta kiran wayanki ba,a daga
ba momy na ma mance da ita in na koma zan
duba. ina koma gida na dauko wayar miss call
yafi hamsin nayi saurin dubawa wannan number
ceta min miss call 45, na duba account din naga
akwai raguwar kudi na kira number ana dauk wa
suratul iklas naki shiru nayi ina saurara har aka
gama sai kiran ya katse. wajen wata daya kullum
sai an kirani da number ina dauka wa karatu
kawai nake ji wanda hakan ba karamin farin ciki
yake sani ba, har yau ban san waye yake da
number ba kuma ban samu nasan waye bane.
yau tun da safe nake jiran waya shiru bayan na
idar da sallah na dago wayata na duba saina ga
da raguwar kudi kadan sai na fara rubuta sako
kamar haka *dan Allah waye ne me wannan
number nayi sending ban fi minti biyar da turawa
ba ga reply kamar haka "muhammad. i .salis
Abbagana hausa novels @ facebook. [10/3, 8:12
PM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 33
MUH'D*ABBA*GANA www.abbagana.pun.bz
abun ya bani mamaki kira ne ya shigo kamar kar
na daga can na daga muryar sudeis ta duka
kunnena cikin suratul ma,ida shiru nayi ina
saurara har ta kare nayi sauein cewa dan Allah
waye ne? cikin wata zazzakar murya aka furta
muhammad ne ana fadar hak aka katse na ajiye
wayan na wuce cikin toilet, ina toilet naji kara
wayata bayan na fito na daga hello suppy kin
shirya shirin me kuma? kin mance bikin zulaih oh
nina mance kuje kawai bazan samu zuwa ba
haba suppy karki mana haka kin san motar
rukayya ta samu matsala, ni ai bam sani ba to
yanzu kin sani dan Allah ki shirya gamu nan
zuwa ke sadiya bafa inda zani kinga ga mominki
zata miki magana kan nayi magana naji muryarta
safiyya mekike cewa ? ba magana nayi ba cewa
nayi sai kun karaso okey mu same ki a ciki? zan
fito kafin ki iso ma tunda muka shiga mota babu
wanda yayi wa wani magana ba har muka karasa
wajen party yan mata ne kowa yana harkarsa ,
parking nayi momy in kun fito ina jiranku ba zaki
fito ku gaisa ba Allah momy babu inda zani toh
shikenan wayata ce tayi kara nayi saurin dagawa
naje angwa in na koma gida zan kira ka ina fadar
haka na katse. fitowa nayi ina kiran su sadiya
mu tafi mutum na gani tsungune bayan mota ta
na kunna touching waya na na haskashi da sauri
na koma cikin motana ina zaune har na fara
barci naji karar waya na tashi na dauko yau dai
na kira mu gaisa abunda aka furta kenan dan
Allah waye kai kai tsaye aka ban amsa kiyi hakuri
na takura miki koh? ni dai kawai ka gaya min kai
waye ne ya akayi ka samu numberta? zan gaya
miki gaskiya numberki a jikin kudi na ganta nasai
credit an ban canji to ban duba ba kum lokacin
muna hanyar zuwa filin jirgi zan taho karatu
kasar waje bayan na sauka na duba kayana sai
naga canji ina budewa sai naga number an kum
rubuta suppy tawa ni kuma sai naji ina son jin
muryar me number da fatan kin gamsu da
bayanina.
Abbagana hausa novels @ facebook. [10/3, 9:58
PM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 34
MUH'D*ABBA*GANA www.abbagana.pun.bz
tabbas na tuno ranar da sadiya ta rubuta number
ta a jikin kudi kawar kice? school din mu daya to
baki gaya min sunanki ba? meye ruwanka da
sunana, ina son kawai naji "safiyya mukhtar
shine kawayenki suke kiranki da suppy an ce
maka kawaye ne dani? zan kwanta okey safiyya
na gode sai da safe. ya rage saura sati uku
umma su tafi tun da naje makaranta nake ta
ware ido inda zan hango sadiy ko momy naji an
rufe min ido momy ko sadiya ta bude tana dariya
kallon me kike ku nake nema littafi ta zaro take
karantawa, momy kema kina karatun littafi??
baby labarinsa aka ban momy meye a cikin
littafin uhumm baby bazan iya baki labari ba zan
so ki karanta baby ban taba ganin rayuwa irin
wannan ba zan baki ki karanta momy ya
sunansa? bayan ta juyo tace da ita
"sireenah"baby so nake kawai na karanta na 3
naji karshen matar da yayanta. ya rage saura
kwana uku su umma su tafi ina daki umma ta
shigo nana kizo alhaji yana kiranki tare muka fita
muka tarar dashi yana zaune a falon umma,
safiyya kinga saura kwana uku mu tashi shine
nace zaki zauna ko zaki tafi gidan kaka kan mu
dawo? zan zauna sai a dauko kaka ta tayani
zama kuma muma sauran sati hudu mu tafi
lagos, Allah ya kaimu karatu yazo karshe kudi ya
zaro gashi ki rike a hannunki na karba ranar da
suka tafi ina school ban samu damar raka su ba
ina dawowa na tadda kakz a,a yar tsohuwa kin
sha A/C har kin fara mulmulewa zaki fara halin
naki koh kinga abar magana yanzu ina abinci na
ba wani musu ta nuna min. khalifa ya shigo
muna cikin hira maryam ta shigo yaya kazo inji
momy okey ina zuwa. muka ci gaba da hira ji
mukayi an banko kofar kai dan wulakanci ana
kiranka shine kake zaune wajen wannan
kwadayyayun tare suka fice aiko ranar kaka ta
rantse ba zata kara kwana gidan ba babu irin
magiyar da khalifa bai mata ba amma taki haka
dole ya kaita gida, ina daki naji sallamarsa har
ka dawo daga kai tsohuwa yar rigima babu wani
rigima sai gaskiya kuma wallahi in daddy ya
dawo sai na gaya masa yanzu nana zaki iya
kwana ke kadai to me zai sameni? shikenan
safiyya zanje nayi sallah yana fita momy su ta
shigo kina ina makira? nayi saurin fitowa ta
cigaba da cewa to wallahi abinda zan gaya miki
ki fita daga harkar dan in kina ganin uwarki ta
cinye zuciyar alhaji toke kinyi kadan ki cinye
tasa...........
Abbagana hausa novels @ facebook. [10/3, 9:59
PM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 35
MUH'D*ABBA*GANA www.abbagana.pun.bz
murmushi na saka zahra'u ni safiyya a golar gida
nafi karfin danki kece kike kishi akan danki har
kike tunanin ko auransa zanyi umma kuma da
kike maganar ta cinye zuciyar mijinki ladabi da
biyayya ta fiki ina fadar haka nayi daki. tun da
ga ranar ban kara ganin khalifa ba yau ina
kwance naji shigowar message dagawa nayi tare
da budewa 'please safiyya kin ban dama na
kiraki mu gaisa na rasa ya zanyi bana so na kira
ba tare da amince warki ba. naku muhammad I
salis. muhammad na kara mai mai ta sunan
kwata kwata na manta dashi filashin nayi masa
ba,ayi mintu biyu ba ya kira "Assalamu alaikum
naji sansanyar muryarsa ta doki kunne na safiyya
kin amince na dinga kira muna gaisawa kau nifa
na mance da kai sai ka tuna min waye kai bakin
ciki ne ya tunkare zuciyarsa da kyar ya iya
hadiyewa tare da cewa ni kam kinga bazan taba
iya mancewa dake ba koh? sosai ma kuwa kina
lafiya ya karatu? lafiya klau karatu mun godewa
Allah safiyya ni baki tambayeni ya karatuna ba,
meye ruwana sa karatunka kaga maganar ta isa
haka zan kwanta, bai kamata ki kwanta haka ba
cikin mamaki nace saboda me? ki tashi ki roki
ubangiji bukatunki ko ki daura alwala ki kwanta.'
okey na gode ina cikin sallah naji wayana na kara
bayan na idar nayi addu'o'ina na dauko littafin
da momy ta ban na karanta "MASOYINA HAR
ABADA" na mrs umar. ina cikin karantawa
wayata tayi kara na daga, na zata kinyi barci ga
karatu nan zan sa miki, to na gode ina saurara
muryar sudeis naji cikin suratul rahman tun ina bi
har barci ya dauke ni muryarsa naji safiyya iya
nan kika iya? firgit na bude idona cikin wata
rikitacciyar murya nace ka kashe kar kudinka ya
kare wata irin ajiyar zuciya ya sauke kiyi addua
sai na kashe kan ya kara wata magana na katse
wayar. washe gari umma ta kirani mun jima
muna hira muna cikin waya naji sallama juyawa
na momy ne tare da farida na hango tare muke
karatu da ita yar katsina ce da gudu na taro su.
yanzu baby ke kadai kike kwana momy ya zanyi
umma ta tafi ta barni na juyo wajen farida
yaushe kika dawo ina kuma tsarabata uhum
suppy kin fiya ban haushi kudi kawai na karbo
kin san saura sati daya mutafi. sai bayan isha
suka tafi na gama shirya tsaf zan kwanta naji
karar wayat sai da ta kusa katsewa sannan na
daga' na zata kinyi barci yanzu nake shirin yi dai
okey safiyy wai me kike karantawa ne?? da sauri
nace meye ruwanka da abinda nake karantawa,
laifi ne dan na tambaya?? to ba zan fada ba".
Abbagana hausa novels @ facebook.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.