[3:31PM, 5/15/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?
13
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
na katse na ja tsaki har kin sallami yayan naki
okey ke ba ya yanki bane abin ba kara nao dariya
sorry sahiba gaskiya na fada saboda ni dayace
banda yaya mamana ta haifa ai ko inda kina da
yaya dai sai nace ina a aiki cikin mamaki nace
saboda me? don nasan zai kasance kyakyawa
kamarki kinga ko kasami namiji mai kyanki ko
haye bbu inda baza ka shiga ba ke,wallahi kin
fiye ban dariya karfe biyu da rabi na koma gida
kaka tana zaune tana kada lagwani na shigo ban
ko kalleta ba na shiga ciki sai nayi wanka nayi
sallah sannan na dauko sallaya da jakata na fito
soro madam kaka ina abincina naji gidan kanshi
dambu kike yi,"sai yanzu kika san da mutum a
gidan mara kunya tana maganar tana cigaba da
kada lagwaninta keh kaka me kuma nayi na
rashin kunya na shiga ukuna kullum cikin laifi
nake a wajenki ban taba yi miki gwaninta
ba,amma shi kenan inna gudu na barku kwa
nemin wata rana.in kin gudu sai me baki ji wani
tsohon mawaki ba yace yawon duniya mafarki
kowa yayi shi dole ya farka,kaka sharrin da zaki
min kenan koh? ina batun sharri ko gaskiya ni
kinga rabu dani in kuma yanzu ma kashe ni zaki
yi to baki na bude kamar me hamma.wane ni na
kashe kaka mu rayu dawa? oho miki sakarya
kawai okey kakas magana ta wuce "wai wani
rashin mutunci kike ji kike batan suna saboda
wuyanki ya isa yanka to wallahi ki bi duniya a
hankali "wai kakas meye haka ina ta binki ta
lallami in kuma kin fiso muyo fada to ki ban
abincin kin tsaya wani wa'azinki sai kace
malamar gaske nan ko karatun sallah sai anci
gyaranki inda bani nake koya miki karatu komai
ba 'kin wa rakiya ita ce bata iya komai ba
shegiya mara kunya wallahi indai haka ki kace
zaki ringayi kinyi asara kuma in kinci dambun nan
kinci hantar uwarki dan ba ubanki ne ya ban
kudin ba.can ta matse miki dambun kuma kici ke
daya kashen sa zakiyi.....wani yaro ne ya shigo
shigan lagwani kai zo ka karbon lemon kwalba na
shiga na dauko safayar kwalba na bashi bayan ya
dawo ya cillan bakar leda a fuskata gashi nan inji
kado (Dan malam mado ne shege kado har ya
hado yaji kudin yaji banza ta wadi to ni kaka me
zanyi da kudin kya kara jari ki kuma rike a
hannunki.au ni zaki tsokana tana magana tana
hararata "Allah vaba bada wasa nake ba in kuma
ba kya so na fita na bayar sadaka kinga kin hutar
da kanki"
Abbagana hausa novels @ faceebook.
[3:33PM, 5/15/2016] Ábbā-Gãñå WAYE SANADI?
14
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
ai shedanne mai maida alkairi bazan so na zama
shedaniya ba,na gode Allah yayi miki albarka" wai
yau wace rana kaka ta samun albarka haba
takwarata ai ke kike jawo abinda zamuyi
fada,wallahi duk abinda zan fada miki gaskiya ne
nake gaya miki,nana yau ko namiji anayi mishi
fada ballantana ke mace duk abinki wata rana
gidan wani zaki je,in kuma ki kaje da wannan
halin wallahi ba zaki taba jin dadin rayuwa ba
son......" kinga abar maganar yanzu zaki ban
dambun ko na hakura? ya za ayi na hanaki
dazumma ke kika bata min rai wallahi nana dan
muna kaunarki ne shi yasa muke miki fada
kum....."ringing din wata ne ya sata tayi shiru
tana kallona na zaro na daga in ka kara kirana
ban yafe maka ba ina fadan haka na katse.ke
kuma da wa? kaka take tambayata wallahi kaka
wani ne yake neman ya takuran haka kawai yake
ta kiran wayata.to ki dai a sannu tana maganar
ta mikon plate ta juya tayi ciki ina cikin ci text
message ya shigo"wallahi ba zan taba daina
kiranki ba,har sai kin tsaya mun yi magana ta
nutsuwa na san wrong number na kira to amma
kuma sai naji zuciyata tana ban sha'awarar ci
gaba da kiranki,banza wahalalle sai kai tayi can
ta matse ma.bayan sati daya yau tun safe nake
ta hada kaya kaka sai dariya take to nana ta dan
Allah in kin je karkice zaki gwada musu halin naki
ki tausayawa uwarki karki sata magana tun da
zaman aure ne ya kai mahaifiyarki ciki.dabara
tayi min saboda tayi min nasiha amma saboda
zumudi sai amsa mata nake da to_to karfe
takwas muka ji sallamar alhaji nasir kaka ta fito
tayi masa shinfda lokacin ina sallah a tsakar
gida,bayan sun gaisa ta debo masa ruwa Alhaji
ya iyalin? vaba lafiya klau da tare da rukayya
zamu taho kan na koma gida ka ta shirya mutaho
sai naga lokaci yana kara kurewa dan haka na
taho ni daya,daukar ta nazo yi dan munyi kewarta
ya juyo yana kallona lokacin ina addu'a ina
juyowa naga yana kallona na harareshi naci gaba
da addu a kaka ina kayan nata nasa a bot,ai gasu
a gabanta nana yau tun safe ake faman zumudin
hada kaya za a ga umma ita ma umman tayi
kewarta kullum hiranta daya nana"yana fitar da
kayan na hau kan kaka da masifa meye zaki wani
ce ina ta zumudin sai kace zani wani gidan gwal
ni bana son irin haka mutum sai wani rawar jiki
yake yaga mai kudi na mike na fita bbu ko
sallama zuwa nayi na jingina da motar yana
gama gyaran kayan ya ganni a tsaye "ah safiya
har kin fito? ban ko kalle shi ba na amsa a
dakile.
Abbagana hausa novel@ facebook.
WAYE SANADI?? 13&14
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.