shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 22 October 2016

waye sanadi? 41---45

WAYE SANADI? 42 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz cikin kuka nace momy kinyi niyar cimun mutunci waye zai aure shegiya momy karkisa zuciyata ta buga please karki kara min maganar aure babu tunanin aure a raina ballantana yanzu da nasan matsayina nasan waccece ni koda ina son saifullahi ko muhammad sunfi karfina momy koda yanzi aure sai dai nasamu dan uwana shege na aura umma ta cuceni ta cuci rayuwata kullum ina jin haushin kaina me yasa ban bari abba ya cimma burinsa a kaina ba......kuka ne yaci karfina jikin momy yayi sanyi sosai ta tsunguna a gabana kiyi hakuri kibar kukan nan yau satin mu hudu tunda mukazo kullum kina cikin kuka haba baby kamar ba musulma ba tafi awa tana lallashina tare da nasiha. bayan munyi break muna rufe daki sadiya tazo ina kuma zaku kuke kokarin rufe daki zai kai baby asibiti tako kwashe da dariya wannan uwar zaki kai asibiti to wai ke din ina kika sani da zaki fita wata kawatace zata rakamu. na zaro ido momy kawa kikayi tace kwarai kuwa ko ban isa nayi kawa ba amma musulmace? meye ruwanku kiyi hakuri momy to ya sunan kawartamu muna cikin magana wata shirgegiyar bakar mata mai sa kukan dare ta nufo wajanmu kannan nata yaci karin gashi daga ita sai wani mini siket da farar riga nida sadiya muka bita da kallo har ta karaso muka gaisa na juyo wajen momy' momy wannan ce sabuwar kawar tamu? kai ta daga tana harararta. da sadiya mukaje asibitin karfe biyu mua fito tare da ita muka shiga daki na juyi ina kallonta kawata baki gayamana sunanki ba ta juyo tana murmushi oniya okinwa ke kumafa ina dariya nace nana saffiya mukhtar suna mai dadi ina son irin sunanku amma kin burgeni kina da kyau sosai kuna kama da rukayya sosai amma ke kanwartace? juyiwa nayi ina kallon momy tana waya maganar oniya ce ta dawo dani ina son muyi kawance ina son inga inda kawaye kyawawa duk cikin makarantar nan ban ga me kyanki ba zakiyi samari da dami dariya nasaka oniya kin ban dariya tace me nayi na baki dariya? maganar ni din bana kula samari kuma oniya aikin fini kyau, kina zagina ne kawai dazun da muka fita ake miki magana don ma kar muji me zakice sai ku juya baki, safiyya duk wanda kikaga yayi min magana cewa yake na shigar dashi a wajen ku musamman ma ke. mun jima muna hira sannan ta tafi gida na juyo ina kallon momy nace momy yunwa nakeji a hasalce ta dago sai na zama abinci ki cinye kwanciyar ta tayi ta shareni. har wajen karfe uku tana barci wayarta ce ta tasheta tana tashi ta juyo tana kallona na kwantar da kaina daya bari, bayan ta gama wayar ta shiga toilet tayi wanka ta dauro alwala bayan ta idar ta mike kizo muje wajen abincin ban ko kulata ba na mike muka fita. ban garen umma kuma...... sallama tayi yafi sau uku amma shiru don haka ta shigo gidan tana zaune tsakar gida fuskanta shakaf da ruwan hawaye. Rakiyya!! Rakiyya!! ta hau kiran sunanta kamar an tasheta daga barci ta juyo babah sannu da zuwa banji shigowarki ba zuciyarta cike da tausayin halin da yar tata ta shiga tace Rakiyya kuka kike? babah wani irin kuka kuma fuskarta cike da mamaki tare da tashin hankali tace ga hawaye nan a kumatuki....(nima can fuskata ne ciki da raunin tausayin rakiyya) TO BE CONTINUE SOON!!.... DON'T FORGET HAVE A LIKE ON MY FACEEBOOK PAGE: Abbagana hausa novels. [10/5, 8:34 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 43 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz kanta karasa umma ta kai hannunta fuskarta wanda kamar an watsa mata ruwa sunkuyar da kanta tayi hakan ya dada tawo da wasu hawaye mazu zafi kan fuskarta har sai da suka taba kasa zama tayi kusa da ita cikin taushin murya babah tace rakiya nayi nadamar korar safiyya daga gidan nan kiyi hakuri duk halin bakin cikin da kike cikii ne yaja miki na rabaki da farin cikinki rakiya ki yafe min dan Allah, baban dan Allah ki daina ban hakuri nice zan baki hakuri in na miki laifi. tana maganar tana goge idanunta wanda ke cike da hawaye rakiya ki rage tunani ki duba halin da kike ciki karki haddasawa kanki wani ciwo munyi magana da mallam ranar laraba zamuje gongola . babah kar muje zasu ce dan muna cikin matsala ne yasa mukazo, sai da mallam ya gayan haka ni kuma nayi tunanin rashin zuwana bazai kwantar da matsalar da take tsakanin ba cikin mamaki nace babah wace irin matsala? hmm rakiya in munje kya gani da idonki mallam yace in munje karmu nuna auranki ya mutu kuma kar muyi maganar batan safiyya zamu nuna tana makarantar kwana, shikenan babah babah bayan fitarki alhaji nasir yazo bai tar da keba yace zai dawo da magariba. karfe takwas alhaji nasir yazo bayan sun gaisa da babah ta mike bara na shiga wajen mallam bayan fitarta ya juyo yana kallon umma rukayya ina so na tambayeki tsakani da Allah ki ban amsa ta daga masa kai bai damu da rashin bashi amsa da tayi ba yace ki gayan tsakani da Allah ina dangin mahaifin safiyya suke a razane ta dago bata taba tunanin tambayar da zai mata kenan ba kantayi magana yaci gaba da cewa karki boyen komai safiyya bata da uba ne?? cikin kuka taxe wallahi da ubanta to yana ina? in kuma ya mutu ina danginsa? karki boye min gaskiya rukayya in safiyya bata da uba kaddara bata wuce kan kowa ba bata tsaya wata wata ba ta bashi labarin auranta da Dr. mukhtar har sakinta da yayi bayan dawowarta gida ciki ya bayyana akaje aka gaya masa sa duk abinda yace ta kara da cewa wallahi alhaji tunda nake a rayuwata ban taba sanin wani da namiji ba sai shi amma yaxe safiyya ba yarsa bace nayi tunanin zuwan wannan ranar da babah zata gayawa safiyya wannan maganar tun farko nina cuci kaina sa ban bawa safiyya tarb.....kanta karasa ya tare numfashinta karki karasa dana sanin a bata da amfani tun farko kika cuci rayuwar safiyya kina nunawa safiyya so mai tsanani wanda haka yasa kika gaza sauke nauyin da Allah ya dora miki tun tashin safiyya duk abinda tayi bakya taba tsawatar mata ko tayi ba dai dai ba ki mata fada kinga soyayyar da kike mata ta zama cuta gashi yanzu cutar ta zama babba kin kasa maganinta ido ta daga wanda ke cike da hawaye alhaji wace iein cuta nayi wa nana? kin cuceta mana tunda baki sauke nauyin da Allah ya dora miki ba baki taba tarbiyya da duk wata uwa take bawa danta ba. Abbagana hausa novels @ facebook. [10/7, 7:51 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 44 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz kiyi tunani safiyya macece duk daran dadewa zatayi aure kina ganin akwai namijin da zai aureta bai isa ya gaya mata magana ba, koh ya bata umarni taki bi kuma su zauna lafiy kin san haka ba zata sabu ba. kema ai babah tana sonki ta tsaya ta baki tarbiyya tun kina karamarki in kika yi ba daidai ba ta nuna miki har kika girma gashi kin haihu ke ma meyasa baki taimaki yarki ki nuna mata gatan da aka nuna miki ba. cikin kuka tace Alhaji Allah ya jarrabeni da kaunar nana wadda kukan ya jawo nayi mata Babban SANADI, tun da safiyya ta tashi ba tasan fada ba balle tsawa ko duka, ko babah bana bari tayi mata fada tun abin yana damun babah har ta gaji ta zuba mana ido akwai lokacin da babah tayi wanki nana tazo ta debi kayan ta wasa cikin rijiya shine ranar da babah tayi niyyar dukanta amma na dauke ta na kaita daki ina bata hakurin tsawar da babah tayi mata wanda hakan ba karamin bakantawa babah yayi ba ta biyo mu tana fada karshen kalmar babah dana dau abin wasa yau gashi ta zama gaskiya kull.....kuka yaci karfinta ta kasa karasawa kiyi hakuri kuka bashi da wani amfani addu'a zaki yi, Allah ya dawo da ita. ya jima yana kwantar mata da hankali har sai da yaga ta daina kuka har ya mike zai fita ta tuna bata gaya masa zancen tafiyarsu zuwa Adamawa ba, tana gaya masa ya juyo Rukayya ki bari in kin haihu sai ku tafi toh saboda me? fuskarta dauke da damuwa yace Rukayya ina tsoron ko bara ku dawo ba dan Allah in wani abin kika kulla kiyi hakuri ki kwance kin san ba a san raina na saki ki ba, ina gudun fushin mahaifiyat in Alllah yayi zaki dawo zaki dawo dakina babu wanda ya isa ya hanaki, kaddara daman lokacin rabuwarmu yayi in kika gujen baki min adalci ba, kar kisa abinda zaki haifa yayi marauci. abin har ya bata dariya wallahi alhaji babu wani abinda na kulla a raina za dai muje muyi zumunci tunda mun jima bamu je ba. shi kenan rukayya na yarda dake yanzu yaushe zaku tafi? ranar lahadi zamu tafi to kwana nawa zakuyi gaskiya ban sani ba yayi saurin dago kai in kun tafi kenan babu ranar dawowa? haba dai ba zamu wuce sati biyu ba Allah ya kaimu zan kawo tsarabar da za a kaiwa yan adamawa. Ana gobe zamu tafi misalin karfe tara Alhaji Nasir ya shigo hannunsa dauke da manyan jakunkuna guda biyu wadda umma zatayi tsara ba tare da kudi masu yawa dan kula da kanta kafin sun dawo. karfe shida yazo ya kaisu tasha sai dayaga tashin motarsu sannan ya tawo ziciyarsa cike da damusa da kuma tunani, tunda umma suka sauka a tasha take kallon yanayin garin cike da sha'awa mallam mado ne ya dauke su ya shigarda su har kauyensu, maganar mallam mado ce ta katsewa umma tunani tajuyo tana kallom wajen da yayi umurni a tsaya, hango wani dirkekiyar darbejiyan yara jingim a zaune bayanta bukkokine da yawa dukkan su suna zagate da karare. Abbagana hausa novels @ facebook. [10/7, 8:30 AM] Äbbå-Gãñâ: WAYE SANADI? 45 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz muka karasa cikin gidan babu kowa a ciki sai wata kyakkyawar yarinyar tmdaga tana kallonmu cikin rashin sani duk da haka tayi saurin mikewa ta dauko tabarma dake cikin wata bukka ta shimfida. babah tace ina mutanen gidan? yarinyar tace sun tafi kasuwa, su baffa kuma suna kiwo mallam ya mike tare da cewa muje ka rakani ya gayawa wani yaron daya tayasu shigar da kaya. tunda suka fita da mallam basu dawo ba muna zaune har wajen karfe biyar sannan matan gidan suka dawo suna ganinmu suka yi shiru da surutansu suka hau yi mata sannu da zuwa wasu tsofaffi biyu ne suka tsurawa babah ido tare da sake baki daya daga cikin su ta furta sufi kene ta daga kai tana murmushi kai kawai ta girgiza sufi kinsha hanya ta juyo tana kallon matar gidan maza ku dura abina sannu ta Rakiya haka kika girma ku taso mu shiga ciki. muda mado ne yaje wajensu baffa kun sha hanya rakiya ina yayan naki? ina murmushi nace guda daya ce tana makarantar kwana ta juyo wajen babah nan take suka juya harshensu zuwa fulatanci abinde ya daure min kai ganin babah tana hawaye, nikam sun saka ni a duhu tunda bana jin fulatanci shigowarsu mallam ce ta katse musu maganar da suke tare da wani mutum wanda naji mallam ya kira da jauro sunde jima suna maganganunsu wansa ban san kome suke tattaunawa ba **** ***** ****** ***** yau watanmu biyu a lagos muna tare da oniya muna duba wani littafi sadiya ta karaso tana dariya mukayi oniya tace ina ruka? (sunan da take gayawa momy kenan) suna tare da saifullahi ina jin ta fadi haka na maida kaina ga littafina safiyya yakikayi shiru?? na dago ina harararta idan bakinkine sai ki matse nayi maganar kan na rufe baki momy ta farida ne suka shigo tare da cewa yan uwa albishirinku sadiya da oniya sukace goro" momy ta dago wato ke bazaki ce goron ba ko? gaskiya momy in har sai safiyya tace goro sai dai su hakura da jin albishirin nikam dana ji da kar naji duk daya ne ina fadar haka na tashi ban karasa dakinmu ba text ya shigo waya ta sai dana shiga nayi sallah sannan na bude "đáñ gírmàñ Àlláh §à₣₣íýà kî gâýàñ wäjéñ đákìkè ñäžõ mùgâî§ā, kî táímákâmîn ñámíkî âlkãwárìñ ìñ đâì ñãzõ mùkã gâì§å §àù đãýâ bá žãmù kãrá hāđùwâ bá hâr ábãđã, kì tãìmâkî rãýúwâ ÑÂÑ ŠÁ₣ÍŸŸÂ đâñ ùwâñkì čìkìñ mùšùlüñčï. muhammad imran Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).