Assalamu alaikum! Zuwa ga daukacin ma'abota wannan shafin na abbagana hausa novels.
Bisa ga dukkan alamu wannan shi ne rubutu na na karshe a shafin bulog na MyWapBlog. Domin kuwa, a safiyar shekaran-jiya alhamis ne, 6 ga wannan watan na oktoba, shugaba kuma wanda ya kirkiri MyWapBlog din, Arvind Gupta, ya fitar da sanarwar rufe ayyukan MyWapBlog a ranar 15 ga watan Nuwamba mai zuwa. Idan har hakan ta kasance, wannan na nufin karshen dukkan shafukan bulog na MyWapBlog ya zo kenan.
Shafin MyWapBlog dai ya kasance wajen da aka kyankyashe wannan shafi na abbagana hausa novels tun a watan Yunin shekara 2012. Wato kenan, zuwa wannan lokaci da mu ke bankwana da MyWapBlog, shafin abbagana hausa novels ya shafe shekaru hudu da watanni uku a bisa manhajar yanar gizon na MyWapBlog. Tsakanin wannan lokaci ne, bisa ikon Allah, na samu daman wallafa kasidu (posts) sama da 800 wanda na ke kayautata zaton dubban jama'a sun amfana da su a wannan shafin, duk ta hanyar amfani da MyWapBlog. Don haka, ba za mu manta da rawar da MyWapBlog ya taka ba, a game da wannan shafin. Haka kuma, ba zan manta da duk wadanda su ka aiko da sakonni ko 'comment' na fatan alheri da nuna jin dadin rubuce-rubuce na a wannan shafi na bulog ba. Godiya ta musamman a gareku.
mu hadu a sabon blog na mai take kamar haka: www.muhdabbagana.blogspot.com
Bissalam, ku huta lafiya.
AGASKIYA BAMUJI DADIBA ALLAH YASA HAKASHI MAFIALKAIRI
ReplyDeletekayya amma nayi matukar bakin ciki muna tare da kai a sabon blog naka
ReplyDeleteGaskiya dai ba dadi
ReplyDeleteThis was loovely to read
ReplyDelete