shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 10 October 2016

WAYE SANADI? 5-6 & 7

[6:25PM, 5/6/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI? 5 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Kiyi wa kanwar nan taki magana ta yarda na kaita a duba lafiyarta sai na sai miki sabon lifan ni za kaiwa karya muryar umma naji a fusace ke wai baki da kunya ba haifeki ba amma har ki ke cewa yana karya dan Allah bawan Allah kayi hakuri bbu komai na dauketa a matsayin yata wani wajen sai da babura na gani na juyo ina kallonsa in ba karya kake ba to ga wajen sai da babura muje ka sai min bai ko kallona ba ya karya kwana ya shiga wajen fito ya juyo yana kallon umma amma dai kanwarki ce ko? wallahi nina haifeta to ina babanta? ya mutu Allah ya ji kanshi ta amsa da ameen yanzu kina da aure? mallam me yasa kake ta tambaya ta ban son ki gaza ba yanzu naji wannan amsar iya so sai kiji dalilin tambayar "to tunda babanta ya mutu ban kara aure,yayi magana na bude motar da karfina ka fito ka biyana zaba ka wani tsaya zuba a'a Alhaji nasiru kaine ka dawo Alhaji musa yata nazo sai mata lifan bayan sun gama magana ya biya kudin to ki zo mu tafi sai wani ya hau ya biyo mu da shi a'a aban key din da kaina zan taho da kanki kuma sai dana murguda baki sannan nace eh da kaina din meye ruwanka na fusgo key din na hau na fara tafiya banko bita kan umma na hau kan titi ina zubga uban gudu har na karasa gida.kakarmu na tarar tare da mallam mado bbu wanda na kalla na wuce zan shiga daki naji maganar baba magajiya mara kunya in kika baro uwarta ki kika zo zaki wuce mutane,kafura mai kama da aljana juyawa nayi na zabga mata harara in ke kike xanja halitta sai kizo ki gyara mutum baka kulashi ba amma shi sai ya kula ka dan.....tsawar malam ce ta sa ban karasa ba wato ke rashin kunyar taki ta wuce kanmu har tazo kan wadda ta haifi uwarki to wallahi ki nutsu in ba haka ba zaki ga yadda zamu kare sakarai kai kuma na kula ka kuma naki ja nutsu bazan nutsu ba sai kayi maganin nawa mutum sai sa ido umma ce tayi sallama ta shigo vaba yana ganku a tsaye lafiya? rakiya muda wannan mara kunyar mara mutunci ce daga tambayarta ina ta baroki ta tsaya take zaginmu" Abbagana hausa novels @ facebook. [7:39AM, 5/7/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI? 6 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Dan Allah mama kuyi hakuri ta biyo ni cikin daki nayi dai dai kan gadona tace tashi zamuyi magana umma kunne na yake jafa bata kara kallonta ba ta juya baya wato nana duk fadan da nake miki baya shigarki ke daya ki tada hankalinmu kullum cikin jawowa kanki magan kike bakya tsoron bakin mutane,haba nana wane irin rayuwa ce haka ba kya ganin mutuncin kowa bakya ragawa kowa hatta ni da na haifeki bakya sauraran wa mahaifiyata bakya raga mata bakya kunyar kowa da kowa me ye amfanin haka saboda ke muka bar unguwarmu muka dawo nan amm....'haba umma dan kinga kaka tana fadin haka shi ne kema saki gayan tunda bakya sona bakya kaunata kawai gara na bi duniya'ina maganar ina kuka nan da nan hankalinta ya tashi meye abun kuka kema kin san ina sonki ina kuma gudun bacin ranki amma ke bakya gudun bacin raina shi kenan umma kin dau zigar kaka wallahi wata rana sai na bar muku gidan in yaso ku zauna da wadda kuke kauna yanzu ma ki tashi ki tafi wa ya hanaki sakarya mara kunya.nayi saurin tashi zaune "wai ke kaka dana shigo na kula ki tunda na shigo kike takalata, me ruwanki san ina magana da uwata sai...." kan na karasar kaina tayo zata dake ni nayi saurin direwa ta taga na fice ina dariya.washe gari na yo cefene ina zuwa kofar gidanmu naga mota ajiye tabbas ban mance motar ba data bigeni ce har ma kuma ya maran ya sai min sabon lifan ai kuwa in har gidanmu yazo to sai na rama na duba in dana kurje nayi saurin yin parking,wallahi sai na rama na dau kayan miya na sauka na shiga soron gidanmu ganinsa nayi akan tabarma ummanmu kuma akan kujera har na wuce na dawo me kuma ya kawo ka? gidan ko nan ma kazo ka mare ni.ke kuma me kenan zama a kusa da shi'rankwashi naji ya sauka a sakar kaina shegiya mara mutunci ubanki ya zaunar da ita wadda bata san uwarta da alkhairi" juyawa nayi ina kallon kaka kai kawai na girgiza kai cikin gida tsayawa tayi tana bashi hakuri,haba vaba bbu komai ai yarinya ce ta shigo tana bambami juyowa yayi yana kallonta umma wadda kunya ta rufeta.rukayya baki ban amsa ba kin amince zaki auran? Alhaji kai yanzu zaka iya aurena kana ganin halin yata ko da na amince nasan nana bazata yarda nayi aure na barta ba, a yanzu duk na mijin da zaka aura bazai yarda ka tafi da yarka ba koda ta garice ballantana kaga halin ta kuma gashi ina son yata bana kaunar abinda zai rabamu in har zaka aureni sai dai ka aura nida yata"; Abbagana hausa novels @ facebook. [7:42AM, 5/7/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI? 7 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz rakayya ai irin son da nake miki babu abinda zai hanani auranki yarki ba zata zame min matsala ba matsalata daya da ita zata bari ki auran? in har zata bari ni kuma nayi alkawarin zan rike ki tsakani da Allah zan rike nana kamar yadda nake rike yayana rukayya n mance ban gaya miki kaina ba Alhaji nasiru aliyu sunan kuma asalin iyayena yar rijiyar lemo ne muna da yawan gidan ina da aure mata ta sunanta zahra ya yanmu uku aliyu,nasiru,sai maryam, maryam nasan zatayi sa'a da nana su Aliyu suna abuja suna karatu maryam kuma tayi candy tana jiran sakamakon ina zaune a rijiyar zaki,rukayya zan tafi amma zan dawo gobe dan naji amsa.ya mike ya fita ina zuwa can ya dawo hannunsa dauke da ledar biba,rukayya ga kayan yar dubiya wannan kuma nakine "haba har da kuma wahala banda machide din da ka sai mata "meye abin wahala dan nayiwa abinda nake so hidima zan tafi sai goben naji yadda kuka yi da ita" to madallah na gode meye abin godiya tana daki ta hada kai da gwiwa sai faman kuka take nayi saurin shiga na ajiye kayan yanzu nana dan nayi miki fada shine kike kuka watau ke ba wanda ya isa dake sai dai kiyi ki yi abinda ranki yake so umma cewa nayi baki isa dani ba kawai kece yanzu bakya kaunata,saboda kin sami saurayi gwara kawai na hada kayana na bar gidan na sami wasu iyayen" nana ni kike cewa na sami saurayi bana kaunarki,yanzu bakya ji kunyar ganin haka ba" to karya nayi miki ba gashi kin fara karbar kayansa ba to wallahi in dai kika aure shi sai na gudu kuma har abada ba zaki kara gani na ba tayi saurin dago kai ta kalleni kan tayi magana kaka ta shigo tace "mara mutunci kin sata a gaba kina zaginta kuma wallahi baki isa ki hanata aure ba mutum nawa ne suka fito suna sonta saboda ke bakya kaunar uwarki ta sami ladan aure sai ki hanata ita kuma saboda tana tsaronki sai ta fasa,to wallahi wannan karyan rakiya in har baki amincs kinyi aure ba bani bake kije can ki nemi wata uwar in dai kika daka ta wannan shedaniyar taki sai zuciyarki tayi bindiga"ta juya tana fada umma ta juyo tana kallona.yanzu nana kinfi son na rabu da mahaifiyata saboda na faranta miki kiyi hakuri ki barni nayi auren nan na gaya masa in har zan aureshi zan tafi dake ya amince yanzu yaushe zai dawo? sai gobe" in ya zo akwai maganar da zan masa.meye wannan kaya ne yace a kawo miki na dubiya. Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).