shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 10 October 2016

WAYE SANADI? 3

WAYE SANADI? 3 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Na zauna a gida har tsawon wata daya sannan ciki ya bayyana mamata ne ta tsare ni da tambaya rakiya cikin naki wata nawa ne? wallahi vaba ban sani ba "watan ki nawa baki ga Al'adarki ba? in wannan watan ya fita wata uku shi kenam na sami mallam mado yaje ya gayawa mijin naki kina da ciki ai ran
da yaje ya gaya masa rakiya nada ciki sun kwashe bbu dadi wanda hakan yasa vaba magajiya zuwa da kanta sai dai ita ma taga ruwan ba'a'i zuwanta uku har yau da taje na hudu ina cikin daki a kwance na rasa me yake min dadi wannan abin kunyar da Dr,mukhtar yake nema ya likan baba ta shigo sannu da zuwa.yauwa rakiya ta nemi waje ta zauna rakiya abinda mijinki yayi mana sai dai mu barshi da Allah shine kawai zai mana sakayya yau har cewa yayi zai sa yan sanda su kamani dan haka na taho kuma naje wajen malam mado na gaya masa yace karmu kara zuwa Allah zai miki sakayya yace da kin haihu in kin yayeta shi zai sa akaita gongola tayi girma acan saboda gudun magana ina kuka na daga kaina yanzu vaba haka zai min,yasa a dinga kallona Allah zai saka min kiyi hakuri damu Allah zai miki sakayya bayan wata shida yau na tashi da ciwon nakuda tun karfe uku nake ciwon har gari ya waye ina abu daya sai karfe takwas na haihu yarinyar kamar mu daya kamar an tsaga kara kyau kamar balarabiya jajir,vaba kuma ta gyara ni bayan anyi wanka vaba ta mikon yar na karba ina hawaye nasa hannu na karbeta meye kuma abin kuka Allah ya raba ku lafiya "vaba ina tsoron ran da yarinyar zata tambayen mahaifinta kada wannan ya dame ki ai da kin yayeta za'a kaita gongola,wallahi vaba tunda na haifi yar nan naji ina kaunarta,kaunar da bana yiwa karan kaina,gaskiya bana jin zan iya rabuwa da ita ko dai dai da minti daya dan Allah vaba ki barta basai an kaita wani waje ba ba sai ke daya a gabana kuma ni ina yi miki kaunar da bana yiwa karan kaina dan haka duk abin da kike so inaso Allah ya raya ta"malam madone ya shigo dan ganin jaririyar,malam mado aminin babana ne*kai masha Allahu rakiya kamar kinyi kaki kin ajje wannan yarinyar bbu abinda ya raba ku na sunkuyar da kaina ina murmushi to magajiya da wane suna za'a mata huduba? malam kasa mata duk wanda kake so a,a rakiya wane suna kike so? malam kasa mata vaba bayan yayi mata huduba na nana safiyyah yace ni kuma gudumawata na bada ragon da za'a yanka Allah ya raya Mana ita""AMEEN" Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).