shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 4 October 2016

TANA TARE DA NI... PAGE 93&94

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI... PAGE 93 BY MIEMIEBEE washegari... Da safe Anas ya tashi yayi wanka sannan ya had’a wa Fannah ruwan ta itama tayi, dakansa ya shafa mata mai ya cire mata d’aya daga cikin had’ad’d’un maternity gowns nata tasa sannan suka karya. “Habeebi ya naga kana zipping mana akwati?” “Yes Baby zamu wuce Maiduguri yau ina zaki iya ko mu bari se gobe?” “No its okay with me toh baka sanar dani ba bale in fad’awa Ummimi, barinje in ce mata ta shirya.” Hannunta ya riqo da wuri “no Mom Hanan baramu tafi Maiduguri da Ummimi ba anan Abuja zan barta zan mata renting gida tayi zamata anan we don’t need her again.” “Haba My Lion wani erin magana kake haka? Ita da wa zaka barta anan?” “Ita kad’anta kamar yadda muka sameta ita kad’ai a NY ai dama cemin kikayi zamu dawo da ita 9ja bawai zata bimu gida ba.” “Oh Habeebi wallahi banajin dad’in abinda kakeyi ko kad’an banaso haba mana Ummimi fa mahaifiyarka ce ko kak’i ko kaso itace mother’nka baka iya canzawa.” “I know ba abinda zan iya thats why I need her out of my life.” “Wai meke damunka ne Baby? Nifa ba haka nasanka ba Ummimi is following us home.” “Sede in ke zaki biya mata kud’in jirgi which I’m not allowing you.’ “Fine karka bari zan kira Abuu in sanar dashi I’m sure shi ze biya mata.” “No Flower you are not doing that I forbid you to call him wai mesa kikeson muna fad’a ne? I’m your husband amman ko kad’an bakiya jin magana na, Ummimi is not following us and that stays that period!” Ya fad’a a tsawace tare da matsawa yakoma kan kujera ya zauna. Kuka ta tsaya tanayi a wajen chan takoma kan gado ta zauna se kuka take wanda ke mugun tayar wa Anas da hankali gani yayi kamar ze iya jure sautin kukan nata amman ina he can’t. “Flower wai baraki bar kukan ba?” K’ara k’arfin kukan nata tayi cike da tashin hankali ya matso kusa da ita yana aza hannunsa ajikinta taja da baya. “Flower kibar kukan mana wai ke bakisan its bad for your condition bane?” “Kai da kasani kuma kake sani kukan fah? Ni ka tashi min akai” ta juya masa baya. Gadon ya haye yadawo ta inda take fuskanta. “Ya isa toh I’m sorry Flower ke kike sani miki masifa nace miki banason zancen Ummimi amman bakiya ji sekita min maganarta. Kiyi hak’uri kinji? Kidena min magananta se baramuna samun midunderstanding ba.” Baki ta murgud’a mai “ni katashi min kuma barin iya tafiyan ba yau mara na naciwo.” “Toh naji sannu, se gobe zamu tafin kenan.” Ta gyad’a mai kai “kuma ni barin tafi ba seda Ummimi.” “Kingani koh?” “Toh Habeebi wani erin magana kake please?” Ta tashi ta zauna “taya zamu taho da ita 9ja kuma semu barta anan ita kad’ai ai gwara ma ace tun farko mun barta achan NY, ni gaskia in bada Ummimi ba barin bika ba.” “Se mu gani ai” daidai ze juya kenan tariqo hannunsa “Habeebi please dan Allah kayi hak’uri mu koma da Ummimi please Habeebi kamin wannan ka gama min komai Habeebi please don’t say no please please sweetheart, the father to my children please say yes kaji Baby? Say yes please.” Shiru yayi bece komai ba dawowa tayi ta zauna kan cinyansa “please Habeebi say yes kaji my Baby?” Nanma shiru “Sweetheart please...” “Toh inta bimun aina zamu ajiyeta?” “A gidan mu zata sauk’a for the meantime.” “A gidanmu? No barin kaita gidana ba never.” “Toh naji ba’a gidanmu ba, a gidanku nasan Abuu ze bata d’aki inbe bata ba ko gun Mami zan kaita please say yes Habeebi.” “Naji” amsar daya bata kenan. Hannayenta ta zagaye a wuyansa tare da pressing masa hot kiss “I love you Habeebi, I love you so much” tayi pecking nasa a kumatun damansa sannan a na hagu se tip na hancinsa “mufita sight seeing (ganin gari) yau kasan bansan cikin Abuja ba.” “As you wish Mom Hanan” yayi pecking lips nata “sa hijabinki muje.” “Yauwa Abu Hanan zamuje da Ummimi?” “Bansani ba in zaki tashi muje toh fine inkuma a’a muyi zaman mu.” “Dama wasa nake nasan ba yarda zakayi ba” daidai zata mik’e kenan Hanan tayi kicking. “Habeebi Habeebi! Hanan moved tayi motsi!” tasa hannunta daidai inda tajiyo motsin, shima hannun nasa yasa wajen kad’an kad’an sukejin motsinta nan da nan suka fita basu suka dawo ba se kusan Maghrib Sallah sukayi Fannah ta wuce d’akin Ummimi inda ta sanar da ita zasu wuce Maiduguri gobe. Hira kad’an suka tab’a Fannah tamata seda safe ta dawo d’akinsu anan suka kwanta da wuri kasancewar zasu hau hanya gobe. ** K’arfe 10:30AM su Fannah suka isa Maiduguri already driver na jiransu a airport, anan ma sam Anas yak’i barin Ummimi shiga motansa haka ta shiga taxi gidansu suka fara wucewa inda shida Fannah suka shiga suka watsa ruwa aka bar Ummimi cikin taxi tana jira, Fannah tayi tayi da Anas yabar Ummimi ta shigo ta watsa ruwa itama amman yak’i ba yadda ta iya haka ta hak’ura bayan sun sake shiri suka fito suka wuce gidansu Anas. Daidai gaban gate Anas ya tsaya bayan me gadi ya bud’e gate ya shiga, itako Ummimi a waje driver ya ajiyeta da kud’in da Fannah ta bata ta biya sa. Fitowar Fannah daga mota ta kama hanyan waje dan shigo da Ummimi ta soma tafiya kenan Anas ya tsayar da ita. “Flower where to?” “Zan shigo da Ummimi ne kafara shiga we will follow afterwards.” “Mschw! Wai ita batasan hanyan ciki bane da sekin shigo da ita? Ni kidena wahalar min da Hanan akan Ummimi.” “I’m sorry Babe yanzu zan shigo da ita ko zaka jira ni neh mu shiga tare?” “Mschw! You are trying me koh?” D’an murmushi ta sakar masa sannan ta fice a waje ta samu Ummimi. “Bismillah mushiga daga ciki Ummimi.” “ ‘Yata nace gidan da muka baro d’azu shine naku dana Anas?” “Eh Ummimi.” “Masha Allah gidan naku yayi kyau sosai kamar a ture wallahi.” “Kai Ummimi mungode Anas ne yayi desinging gidan da kansa kinsan architecture ne ayanzu haka shine CEO na Flames Enterprises one of the biggest Emterprise a Nigeria in whole, he is being referred to as Nigerias youngest billonaire, Ummimi ki godewa Allah Anas naki is very bright.” Hawayen jin dad’i ne suka soma gangaro wa Ummimi “Alhamdulillah! Oh! Allah sarki Anas Allah ya cigaba da mai bud’i ya kare shi daga sharrin maqiya, ameen.” “Ameen Ummimi mu shiga.” “A’a Fannah tukuna, ina ne nan?” “Nan gidansu Anas ne mushiga Abuu na ciki.” “Kina nufin wannan babban gidan na Abuun su Anas ne?” “Eh Ummimi” “Allah mai iko, me azirtawa dakuma talautarwa, Allah sarki ban kyauta wa kaina ba wallahi ko kad’an, da ace na k’ara hak’uri na cigaba da zama da Ya Ibraheem da atare zamuyi wannan arziki, Allah cigaba da masa bud’i yakuma rabamu da sharrin shaid’an gabad’aya.” “Ameen Ummimi mushiga.” “Fannah banida courage na shiga, ina tsoro nasan cikinsu ba wanda zeyi accepting d’ina sabida abinda na musu da ciwo zasu ce ban tashi dawowa ba sedana ga Ya Ibraheem yayi arziki, please ki kaini wani gun daban kokuma in zan iya tuna hanya in je gidanmu that is in iyayena suna raye.” “Ummimi just trust me kinji? Mushiga ciki please na tabbata idan duk sukaji labarin ki zasu yafe miki musamman ma Shettima I know him shi ze fara accepting naki” Hannu tasa ta share hawayen nata sannan tabi bayan Fannah hannunta riqe cikin na Fannah. Amal na bud’e k’ofa taga Anas ne tsaye jikinsa ta d’ale tana mai oyoyo! “Ya Anas I missed you so much, shine zaku dawo baku sanar dani ba tun shekaran jiya nake trying numban ka dana Ya Fannah basu shiga.” “Sorry Angel we wanted suprising you su Abuu suna ciki?” “Yes kowa na gida ina Ya Fannah da Hanan d’ina?” “Gata chan!” yayi mata nuni da yatsa. Tafe Fannah ke da Ummimi behind her. “Ya Anas ita da wa wancan?” “Nima bansan taba kinsan me nakeso dake Angel?” “A’a” ta girgiza mai kai. “Karki kuskura kimata magana kinji? Koda ta miki karki mata magana she is a bad person.” “Really Ya Anas? Mesa toh?” “Trust me kinji Angel? Karki kuskura kimata magana” Yayi pecking nata a goshi. Alokacin da su Ummimi suka gama k’arisowa Amal ta ruga tayi hugging Fannah har agarin haka ta bige mata ciki. “Amal kinason kijiwa Hanan naki ciwo ne?” “A’a Ya Fannah barin k’ara ba its just that I missed you wallahi gashi munyi hutu ba gun zuwa Ya Shettima kullum na cikin bullying d’ina.” duk maganganun nan datake bata kalli Ummimin da tayi mutuwan tsaye tana kallonta ba ko kyaftawan ido ba. “Aiko ga Ya Anas naki ya dawo seki kai masa k’orafi.” “Haha! Ai kibari Ya Anas yace ze rama min ko Ya Anas?” Tayi maganar tana k’ok’arin maida kallonta kan Anas a garin haka idanunta suka sauk’a kan Ummimi da idanunta suka ciko dam da hawaye ganin ‘yar data bari a cikin tsumma ne ta girma haka tazama babbar budurwa kuma kyakkyawa. Kallon cikin ido suka tsaya sunayi wa juna na kusan minti biyu, wani erin yanayin da Amal bata tab’a tsintan kanta ciki ba tasoma yau. Aina na santa? tambayar data ke tayi wa kanta kenan. “Amal” cewar Ummimi tana mata murmushin daya zame mata dole. Ta bud’e baki zata mata magana kenan seta tuna abinda Anas yace mata sekuma tayi shiru. “Amal barakiyi mata magana bane? Bakiji ta kira sunan kiba?” Cewar Fannah. “Baruwanki, bata santa ba taya zata mata magana zo Angel d’ina na siya miki iphone 7s ma taho kinji?” “Dagaske Ya Anas yeyy!” Taje tayi hugging nasa. “Ina yake Ya Anas?” “Nachan gida tare zamu koma yau zaki kwana mana ba?” “Yeyyy!!! Mushiga ciki toh” dake hankalin ta har a yanzu na yara ne anan ta mance da chapter’n Ummimi taja hannun Anas suka shige ciki. “Ummimi please karkiyi kuka dan Allah, nasan da akwai k’wararren dalilin dayasa Amal tak’i miki magana Anas ne ya hanata kuma jin maganansa take har fiye da yadda takejin na Abuu, duk abinda yace mata yi take but karki damu with time zaku saba she is fun to be with mushiga daga ciki.” Da k’yar tayi convincing Ummimi data kariya da reaction na Amal tabita suka shige ciki bakowa a parlourn illa Anas dake a dining space yana shan ruwa bayan ta zaunar da Ummimi kan kujera ta nufa inda Anas yake. K’asa k’asa take maganar ta yadda Ummimi barata jisu ba. “Habeebi yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?” “Menayi kuma yanzu?” ya bud’e goran ruwan ze kai baki tasa hannu ta k’wace. “Ma tambaya na kake ko? Mena hana Amal yima mahaifiyarta magana?” “Haka Amal tace miki ni na hanata? Ma in ni na hanatan toh ina ruwanki? Tsakaninsu su biyu bata santa ba taya zata mata magana bani ruwana insha.” “Barin bayar ba.” “Ki riqe akwai wani cikin fridge d’in ai” daidai zebud’e kenan tasa hannu ta taresa. Murmushi ya saki “I will excuse you Flower saboda dama mata masu ciki sunada taurin kai.” pecking nata yayi a goshi wanda tuni ta tunkud’esa, killer smile nasa ya kashe mata “Shettima! Shettima!” Yau hau k’wala masa kira. Daidai nan Ummie da Abuu suke fitowa har Amal taje ta sanar dasu dawowan su Anas dawata mata me kama da ita da Anas harma da Shettima kad’an kad’an. “Oyoyo! Mutanen New York ne a gidan namu, maraba lale!” cewar Ummie alokacin data ga Fannah, hugging nata tayi ahankali gudun karta jimata ciwo anan sukayi exchanging greetings. Ummimi dake a parlour ba abinda take se kallonsu hawaye na bin k’uncinta. “Me kuke tsaye anan?” Abuu ya tambayesu. “Uhm ruwa nazo d’aukawa Anas” Fannah tamai qarya “gashi Anas” murmushi ya saki sannan ya karb’a. “Toh mu k’arasa parl-” be samu daman k’arisa maganan ba kasancewan ido hud’u da sukayi da Ummimi kwata kwata ya kasa amincewa da abinda idanunsa ke gane masa cewa ma yayi ko imagination nasa ne kawai, Ummie ma was at shock alokacin data ga Ummimi she couldn’t believe it either. Cike da rashin yarda Abuu ya juyo yana kallon Anas fuskarsa d’auke da son k’arin bayani har b’ari bakinsa ke. “A.. An.. Annas wac..wacce wancan?” yana nuna Ummimi da yatsa, shida Ummie suka kasa kunne suna jiran amsar sa. Daidai nan Amal ta falfalo da gudu, Shettima na biye da ita yana huci sanadin d’aukar masa cookies dayayi niyyan kaiwa Afrah da tayi. “Ai wallahi yau se jikinki yayi tsami, sa’an kine ni da zan ajiye abu ki d’auka har kichi?!”” Yayi maganar se binta yake a yayinda take ta gudu tana kiran sunan Anas “Ya Anas! Ya Anas! Shettima ze min duka.” Suna isowa dining area’n duka suka sa full stop tuni Amal tayi bayan Anas. Ganin Abuu Shettima ya dakata kaman ance ka juya ya juya idanunsa se akan crying Ummimi. Idanunsa ya zaro sosai kamar ze ciresu sam shima ya kasa yarda da abinda idanun nasa ke gane masa. “Abuu wace wancan?” Abinda ya iya tambaya kenan. “Ya Anas meke faruwa haka? Ya naga su Abuu sunyi shiru.” Amal ta tambaya. “Anas magana nake maka wacece wancan?” cewar Abuu. “Abuu Nima bansanta ba Flower keda kika kawo ta seki musu bayani” anan duk suka maido da kallonsu kan Fannah suna jiran amsarta seda ta kalli Ummimi sannan ta kallesu bakinta ya bud’u “Abuu wancan Ummimi ce, Ummimin ku.” © MIEMIEBEE

TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 94 BY MIEMIEBEE “Um... Waye?!”Abuu yayi maganar cike da k’in yardan abinda Fannah tace. “Eh Abuu Ummimi ce” ta sake tabbatar masa, juyawa yayi ya miyar da kallonsa a gareta “Aysha?” Yayi questioning nata hawaye ne ke ambaliya kan fuskarta “nn..na’am Ya Ibraheem” “Ummimi?” Cewar Shettima disebelievingly. “Na’am Shettima.” “Noo this can’t be wannan ba Aysha bace ko Nafeesa?” Abuu yayi maganar har yanzu be yarda ba. “Ya Ibraheem ka kwantar da hankalinka please ba shakka zahiri wannan Aysha ce.” “Meta kemin a gida? kice mata ta tashi tabar min gida tun kafin nakira mata securities banida wani alaqa da ita” yana kaiwa nan yayi ciki. “Ya Ibraheem ka tsaya please” Ummie tabi bayansa. Wani erin matsanancin kuka Ummimi ketayi abin tausayi ayayinda su Shettima suke kallonta kamar TV har a yanzu yakasa motsawa dan yadda mamaki ya ziyarce sa gabad’aya ashe dama ze sake sa mahaifiyarsa a ido? “Ya Anas wace ita? Dagaske kake she is a bad person shiyasa Abuu yace tafita mana daga gida?” “Yes Angel mushiga ciki in ta tafi se mu fito” Fannah ce ta dakatar dasu. “Anas baka gani is about time Amal tasan gaskia itama?” “Flower don’t you ever tell her a thing about it, am not asking you am ordering you banason kifad’a mata wani abu I hope am clear” yana kaiwa nan suka fice. “Shettima” Fannah ta kira sunansa a nitse. “Shettima nasanka kai kam I know baraka yi shunning Ummimi ba dan Allah ka mata magana kama mahaifiyarka magana” kai kawai ya girgiza sannan shima ya koma d’akinsa. Wajenta Fannah ta nufa tana bubbuga bayanta tana bata hak’uri tana me tabbatar mata da cewa evrything will be okay. ** A d’akin Abuu. Zaune yake a bakin gado ya had’a uwa uba tagumi yayi shiru ko kad’an yakasa comprehending abinda ke faruwa gani yake wane a mafarki wai Aysha ce ta dawo matar da har a ayau yakasa son wata mace bayan ita, matar da har a yau yakasa maye gurbin ta da wata, Aysha his first and last love, toh me tazo yi? Ina mijinta dakuma ‘ya‘yanta? shekara goma shabiyar dole ace ta haihu. “Ya Ibraheem bekamata ba kace ta fita maka daga gida nasan yadda abin yake da ciwo da zafi amman hak’uri yazama dole, dole kayi hak’uri kaje kaji dame ta taho meya kawota? Dakuma me takeso” “No Nafeesa kije ki sameta kice mata ta fita min daga gida, banason sake ganin fuskarta.” “A’a Ya Ibraheem nasan you don’t mean what you said, Aysha cefah matarka daka fiso fiye da komai, cool down kaje ka sameta muji dame take tafe please.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin Shettima inda ta samesa miqe kan gado yayi jugum se hawaye yake zubarwa. “Ahhhh namiji dakai kake wannan hawaye Shettima gaskia ka badani yanzu in Afrah taganka haka me makeso tace? Saurayinta rago ne saboda yaga mahaifiyarsa yake wannan kuka?” Tashi yayi a lokaci d’aya yayi hugging Ummie gagam yana fad’in “kece mahaifiyata Ummie, ke kika raineni ke nasani ba itaba, she gave birth to me but you played the role as my mother, ta tafi ta barmu alokacin da muke tsantsan buqatar ta kece mahaifiyata ba itaba Ummie.” Bayansa ta hau bubbugawa a hankali “shhh! is okay Shettima inhar kamar yadda kace nice mahaifiyarka inaso kamin wannan abu guda d’aya yau kaje ka zauna a parlour ka jirani, kamata yayi kabawa Ummimi chance ko explaining kanta ne tayi muji menene amfanin dawowanta kaji son?” “Noo Ummie I don’t want to banason sake ganinta, Ummimi bata sonmu bata tab’a sonmu ba ta tafi kawai.” Breaking hug d’in tayi ta riqo fuskarsa “banason suratan banza kaji ko? Man up! Haba na Afrah ba haka fa na sanka ba tashi kaje parlour kajirani kaji? Don’t say no tashi! Tashi! ina ganinka” ba gardama ya share hawayensa sannan yafice izuwa parlon inda ya tarar da Ummimi se kuka take da Fannah a agefenta ba tare da yace dasu komai ba yanemi waje ya zauna. ** “Anas ka bud’en k’ofan nan kaji koh?” Ummie tayi maganar tana buga k’ofan d’akin Anas dayasa lock ya rufesu da Amal ciki. “Amal tashi ki bud’e.” Ido yamata nufin karta tashi aiko ta maqe tayi shiru. “Anas wai baraka bud’e ba? Sa’arka ceni nace ka bud’e!” “Toh Ummie ki fad’i me kikeso inhar maganan Ummimi zaki mana save it bamuwa so.” “Anas abinda kake be dace ba ka bud’en please.” Badan yana so ba ya tashi ya bud’e tashigo. A kan gado a gefen Amal dake kusa da Anas ta zauna tare da riqo hannayen Amal cikin nata tana mirzawa a hankali. “Amal d’ita.” “Na’am Ummie.” Kafin Ummie ta sake magana Anas ya dakatar da ita “Ummie please don’t tell her karki fad’a mata komai banason wannan yazamo silan lalacewar rayuwar Amal I can’t afford it.” “Ya Anas meke faruwa ne please ku sanar dani, meneh Ummie?” “Amal sweetie kinga matan data shigon nan ko wacce Abuu yakira da Aysha?” “Eh naganta.” “Ummie please don’t” Anas yayi pleading. “Bakiga kuna kama da ita ba? Dukanku da Ya Anas naki harma da Shettima?” “Nagani Ummie wacece ita?” “Ummiminku ce.” “Ummimin mu? Meaning?” Juyo da ita Anas yayi “listen to me carefully kinji Angel?” Kai ta gyad’a. “Good kinga Ummie nan ko?” Nan ma ta gyad’a kai “who is she to you?” “My mother mana Ya Anas, she is all our mother, Ummie mamanmu ne dukan mu koba hakaba Ummie?” Shiru Ummie tayi takasa amsa Amal tsantsan tausayi yau shekarun ta goma shabiyar amman ace batasan wace asalin mahaifiyarta ba, batasan ta ina zata fara mata bayani ba. Kanta ya karkato zuwa direction nasa. “I’m sorry Amal.” abinda ta iya cewa kenan. “Ummie ba mahaifiyarmu bace Angel, ba ita ta haifemu ba she just played the role as our mother amman ba ita bace asalin mahaifiyar mu Ummie is our foster mother Ummimi wanda Abuu yakira da Aysha a while ago itace mahaifiyarmu ita ta haifemu kingane?” Hawaye tasoma zubarwa alokaci d’aya sam k’wak’walwarta yakasa comprehending abinda ke faruwa kamar ya Ummie ba mahaifiyar ta bace. “Ya Anas bangane ba, bangane me kake nufi ba? Taya zakace Ummie ba mahaifiyata bace, ba mahaifiyarmu bace duka? Taya zakace wancan matan datazo wanda ban tab’a ganinta ba se yau itace mahaifiyata? Why Ya Anas?” Hannu yasa ya share mata hawayen. “Angel banason ganinki kina kuka.” “Then tell me you are not telling the truth” cike da tashin hankali ta juyo tayi hugging Ummie. “Ummie you are my real mother right? Kece mahaifiyata bawata daban ba Ummie you are my mother please say yes, Ya Anas be gane bane you are my mother and no one else” itama Ummien kuka take sosai na sosai da k’yar ta d’aga Amal daga jikinta tasa hannu ta share mata hawayen. “Amal I’m so sorry kinji? Ban tab’a sanar dake gaskiya ba, na tauye miki hak’k’inki na sanin asalin mahaifiyarki amman kisani nayi hakan ne for your sake, wanki Anas ne yahana a fad’a miki gaskia sabida yadda yakeson ki bayanson abinda ze lalata miki rayuwa, bani bace mahaifiyarki Amal Ummimi ce ta haifeki itace mamanki na asali.” “Noo Ummie ni kece mahaifiyata and no one else kece ba ita ba she is a bad person banasonta ban santaba.” Ta rushe da kuka, hugging nata Anas yayi yana bubbuga bayanta har seda tayi shiru. “Ya Anas inhar ba Ummie ce mahaifiyata ba then wacece ita? Mesa take zama damu kullum?” “Ummie sister’n Abuu ne bakiji Abuu na kiranta Nafeesa ba? Asalin sunanta kenan but ana cemata Ummie shiyasa time da ta dawo zama damu tun kafin a haifeki muke kiranta Ummie, dalilin daya sa ta dawo zama damu kuwa shine sanadin barin mu da Ummimi tayi” “Toh in haka ne mesa ban tab’a sanin Ummimi ce mahaifiyata ba? Inhar dagaske kai da Ummie kuke wancan matar itace mamanmu mesa bata zaune damu?” “Kinason kisan dalilin Angel?” Ta gyad’a mai kai. “Saboda batada imani Angel, bata da tausayi bata sonmu.” “Anas don’t talk about your mother like that” Ummie ta katsesa “uwa uwa ce komin rashin dad’inta.” “No Ummie kibari in sanar da ita dukkannin abinda Ummimi tayi mana sabida kar ta tausaya mata.” “Anas I said no.” “I’m sorry Ummie amman ya kamata Amal tasan abinda mahaifiyarta ta mata” nan ya cigaba “Amal Ummimi bata tab’a sonmu ba zaki iya tuna ciwon dake a hannu na wanda nace miki agarin ball aka jimin?” Nanma ta gyad’a kai. “Its a lie kinga matar dake parlourn, Ummimi ita tajimin ciwon, she left us for another man 15 years ago...” nan ya kwashe labarin komai yabata ba tare da yabar komi a baya ba. Kuka sosai Amal take Ummie takwantar da ita a jikinta. “Ummie mena mata? Mesa ta tsaneni? Mesa bata bari naji d’uminta ba?” “Shhh! is okay sweetheart ya isa kinji? Bar kukan haka, duk abinda ta miki she is still your mother-” katseta Amal tayi tare da d’agowa daga jikinta “No Ummie you are wrong Ummimi ba mahaifiyata bace, ita ta haifeni amman ke nasani as mahaifiyata saboda haka you are my mother right Ya Anas?” “Yes Angel come here” nan ta matso jikinsa yayi hugging nata “is okay bar kuka kinji?” “Ya Anas promise me Ummimi batazo dan tafiya dani bae, bana sonta kamar yadda tak’i ni tun ina baby, Ya Anas karka barta ta tafi dani please.” “That will never happen Angel.” “Anas ya isa please be kamata kasawa Amal tsanan mahaifiyar ta haka ba koda meh Ummimi tayi she is still your mother yanzu ku tashi muje mu sameta a parlour banason jin no ku tashi.” ** A parlour. “Shettima, Shettima d’ana dan Allah kamin magana I’m sorry for what I did to you dan Allah kayi hak’uri.” Anan ta miqe ta nufo inda yake zaune ta dafe kafad’ansa, hannunsa yasa yacire nata shima yana hawaye “Shettima please kayi hak’uri.” “Ummimi why? Mesa zaki dawo bayan mun mance dake? Why do you have to mess up our lives always? Why Ummimi?” Ya rushe da kuka tsugunawa tayi gabansa tare da hugging nasa sam be hanata ba sede beyi hugging nata back ba, yana kuka tanayi Fannah na kallonsu sun kusan minti biyu a haka sannan ya raba jikinsa daga nata. “Shettima wallahi ba’a son raina na tafi na barku ba I love you guys so much” ta yi maganan hannunta dafe akan fuskarsa tana shafawa a hankali. “Sharrin shaid’an ne ba komai ba Shettima dan Allah don’t stop me from being a mother to you kabani dama in biya wannan shekaru goma shabiyar da mukayi ba’a tare ba please this is all I ask nasan barin iya tambayan gafarar ka ba saboda ban cancanci hakan ba ni kawai kabani dama in zame maka mahaifiya again please Shettima.” Shiru yayi bece komai ba. “Shettima kayi shiru” Fannah tayi maganar tana d’ago Ummimi daga k’asa. Daidai nan Abuu yafito idanunsa sun mugun kad’awa bayanshi Ummie ne da Amal sekuma Anas. Bayan sun zazzauna Abuu yayi gyaran murya; “Aysha meke tafe dake? Me kika zo yimin a gida? Ko ban tambaya ba nasan sharri ne tattare dake saboda haka in kinayi wa Allah kitashi kifita min daga gida, nida yarana bamu k’aunan ganinki, bak’in cikin da kika bamu da abaya kad’ai ya ishemu basekin k’ara mana.” “Ya Ibraheem please ya isa kayi hak’uri” cewar Ummie. “Amal taho nan” Abuu yakirata seda ta kalli Anas yabata nod tukuna taje tasamu Abuu, a gefe dashi ya zaunar da ita. “Zaki iya tuna wannan?” Ya tambayi Ummimi da tuni kuka yafi k’arfinta. “Zaki iya tuna ‘yar da kika k’yamata kika turo ta kamar shegiyar da batada uba acikin basket? Zaki iya tunawa?” Har k’asa ta sauqa kan guiwanta tana roqan Abuu. “Ya Ibraheem dan darajan ubangiji kayi hak’uri, kayi hak’uri dan Allah wallahi baroku danayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa na, d’an Adam ajizi ne we all make mistakes nasani kuskuren danayi babba ne wanda se me imani da tausayi ze iya yafemin, Ya Ibraheem wallahi nayi nadaman abinda na muku musamman ma abinda nayi ma Amal.” Nan ta dawo da kallonta kan Amal. “Amal dan Allah kiyi hak’uri kiyafewa mahaifiyarki I’m so sorry Amal please forgive me, give me the chance to hold you in my arms Amal tunda na haifeki ko k’are miki kallo banba nasa aka nad’eki cikin tsumma aka turoki ban tab’a riqeki ba Amal wannan abu har a yau yana damuna barin tab’a samin sukuni ba a rayuwa na har se in na riqeki as mothers do dan Allah karki hanani please my Amal.” Hannu Amal tasa ta share hawayenta sannan ta miyar da kallonta kan Abuu. “Abuu mena tab’a mata ta tsaneni haka? Mesa baka tab’a fad’amin inada wata mahaifiya ba bayan Ummie? ” “Amal kiyi hak’uri kinji? Nasan mun miki laifi wanda yake babba na hanaki sanin asalin ki, kisani nayi hakan ne saboda ina sonki Amal banason ki tashi kina kewar mahaifiyarki, I’m sorry kinji? Bar kuka” yasa hannu ya share mata hawaye. “Angel zo abinki” Anas ya kirata ba gardama taje ta samesa. “Abuu nida Angel zamu d’an fita in kun gama abinda kukeyi call me se in d’au Fannah.” “Anas dan Allah karka tafi kabari in nemi gafarar Amal please.” “Amal zaki iya yafe mata tauye miki hak’k’in datayi? Zaki iya yafe mata wulak’antaki da tayi since you were a baby?” Kafin Amal ta amsa yacigaba “no that the answer daga ni har Amal bame yafe miki sede ko Abuu da Shettima kina iya hak’uri in maganganun dana fad’a miki are a bit harsh to your ears, hakan na nuni da tsantsan tsanan da nake miki ne Ummimi dukda cewa kina mahaifiyata.” “Anas enough!” Ummie ta daka masa tsawa “kai bakasan wannan mahaifiyarka bace kake gasa mata bak’k’en kalamu haka iya son ranka? Ya Ibraheem kamishi fad’a.” “Anas yayi laifi Nafeesa, amman kuma in kika lura Aysha itace sila da ace bata aikata abinda tayi 15 years back ba da Anas bare tab’a gaya mata munanan kalamu haka ba, I’m not saying Anas is right what am saying is he has a point mukad’ai muka san kalan hell da mukayi witnessing da wannan marar imanin ta tafi ta barmu. Aysha me muka tab’a miki? Talaucin da kika tafi kika barmu danshi kisani bamu muka d’aura wa kanmu ba, gashi nan kinzo kin gani da idanunki Allah ya yaye mana shi saboda haka me kika zo min a gida?” “Tabbas ba k’arya ko kuskure a magananka Ya Ibraheem Allah shike azritawa aduk sanda yaga dama, inda zan iya bayyana muku how sorry I am da nayi, inda kunsan kalan tashin hankalin dana shiga bayan barinku danayi, wallahi tun a duniya anan naga sakayyan butulcin dana muku shiyasa nake barar gafararku Ya Ibraheem inhar baku yafemin ba bansan a’ina zan sa kaina ba bansan ya zaman kabari ze zame min ba ku agaza please. Ya Ibraheem inhar kai baka yafemin ba ba yadda yaran nan zasu yafemin please ka taimaka, Ummie dan Allah kisa baki ko zejeki.” “Ya Ibraheem kayi magana please godiya yakamata muyi tunda har Aysha tagano kuskurenta kuma tayi repenting se ku kuma kuyi hak’uri ku tausaya ku yafe mata, Aysha ko zaki bamu labarin ya rayuwarki ta kasance cikin wannan shekaru goma shabiyar dasuka shud’e ba tare da kowa yaji ko ya ganki ba? Ko ban tambaya ba nasan kina cikin babban tashin hankali jikinki kad’ai amsa ce game tambaya in shaa Allah, in family’nki sukaji labarinki zuqatansu zasu kariya su yafe miki.” “Nagode Ummie” tayi maganan tare da komawa kan kujera ta zauna. “LABARI NA bashida dad’in sauraro, ba komai bane aciki banda k’uncin rayuwa wanda ni dakaina na d’aura wa kaina saboda kwad’ayin kayan duniya dana sa a gaba, kwad’ayi ya kasance halin mata dayawa a rayuwarmu na yau. A gaskia duk wacce tad’au kwad’ayi abinyi toh wallahi tana tattare da gwagwarmayar rayuwa saboda kwad’ayi ba abar yi bace. Labari na wanda yasamu asali tun daga ranan dana bar gidan Ya Ibraheem nabi Alhajin Yola shine mafi mumunan labarin da na jima banji ban kuma gani a real life ba sede a labarai.” Taja numfashi sannan ta cigaba... © MIEMIEBEE

Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).