shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 22 October 2016

TANA TARE DANI 98

TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 98 BY MIEMIEBEE *A/N* *Dear Supporters (fans) barin che dear readers ba dan kuwa dayawa suna karanta wannan littafi nawa suna min hassada akai, wasu kuma suna zagina akanshi ba gaira ba dalili, anyways ina me farin cikin sanar da masu min unnecessary k’orafi akan wannan littafi nawa, wannan shine second to the last page of the story, Allah’n daya had’a mu shi ze rabamu, wataran zaku nemen danku zagen ma baraku sameni ba dama shi had’uwan social media haka yake. Dayawa daga cikin readers harma writers sun b’ullo ta duk inda suka san zasu iya dan hanani cigaba da wannan labari nawa amman dake nasan masoya na sunfi maqiya na yawa sesa ban d’aura kowacce aka ba na cigaba da abinda na fara, true fans kusani ko badan saqonnin alkahirun da kuka riqa mani ba, tsoronku wai kar nayi fushi na katse labari na inason kusani wallahi ba’ayi wacce zata hanani k’arisa abinda na fara ba. I just want you guys to know that no matter what *_INA TARE DA KU kamar yadda kuma kuke TARE DA NI_ Allah shige mana gaba.* *Babban albishir danakeson ma supporters d’ina shine page 98 of *_TANA TARE DA NI_* *is dedicated to each and everyone of you for the love, support and care I recieve anytime I turn on my data* *ina fatan yin hakan ze sanya ku nishad’i dakuma jin dad’i kamar yadda lovely comments naku ke sanya ni jin dad’i nima. MIEMIEBEE loves you so very much!!!* ___________________________________ Washegari suka shirya tsaf suka wuce office, duk meetings da Anas yake dashi dakuma appointment dayake dasu da mutane yayi cancelling ba abinda ya tsinana a office d’in ranan se soyewan da suka tayi da Flowersa dakuma wasa da Hanan, sun d’au selfies ba iyaka bayan sunchi lunch Hanan tayi poopoo aikin da Fannah ta tsana kenan wanke kashi, ko time da Aiman ke baby haka take kwana-kwana in Mami ta sata yi. “Habeebi Hanan tayi ajiya.” “Toh meh aciki? Kowa nayi.” “Nikam...” Ta turo baki wipes na hannun nata ya karb’a cike da mamaki take kallonsa “Habeebi meh zakayi?” “Zan goge mata mana.” “Ka iya ne?” “Zauna kiga.” Akan matress na ta ya kwatar da ita sannn yacire mata pampers d’in yayi disposing sanan yayi using wipes d’in ya gogeta tatas yasake sa mata new pampers kallonsa kawai Fannah ke she can’t be happier than this duk wani abinda tasani Anas nata ya iya she’ve got the best man! Se dariya Hanan ke ma Daddy’nta dayake sa mata new pampers bayan daya gama ya d’agota yana nunata da wa Fannah, “ya kika ga?” “Habeebi kasan ban tab’a ganin amazing person like you ba komai ka iya zamuyi deal kai zaka na wanke mata poopoo in tayi nikuma zannayin sauran.” “Niko duka ma kika ce zan nayi barin damu ba because I love my little Fauzi” yayi pecking Hanan a kumatu daidai nan wayar Fannah yasoma ringing tana kai dubanta taga Mami. “Omg! Habeebi yanzu me zance mata? Nasan definately tana gidanmu ne yanzu haka seda nace maka kar muzo kace se munzo.” “D’aga yanzu muji” ba gardama ta d’aga “hello Mami?” “Eh Fannah gani a gidanku fa ina kika jene?” “Erm.. Erm..” Ta hau kame kame. “Daga tafiya na kin kama yawo koh?” “Mami ba yawo bane fah” ta kare wayan da hannunta “Habeebi meh zance mata?” Amsar wayan yayi “Hello Mami ina wuni?” “Lafiya Babana kuna tare da Fannah ne?” “Eh mun fito asibiti ne d’auka wa Hanan allura.” “Ohh okay toh dama tuwo na kawo wa Fannah zan ajiye mata seka fad’a mata.” “Okay Mami mungode.” “Yawwa ashafa min kan jikata.” “Toh anagama se anjima” karap ya katse. Pecking nasa tayi a gefen idansa “Mr. Fauzi can tell lies ehm!” “LOL ai da nayi shiru ta sissileki.” “Ai cemata zanyi kai kace in biyo ka.” “Haha! Zan qaryata ki ince kekika dameni wai sekin biyoni.” “Allah ko?” ”Yes Baby d’an had’a min coffee kinji I can’t remember when last nasha coffeen Mrs. Fauzi.” “Barin had’a ba” ta murgud’a mai baki. “Flower menayi kuma yanzu?” yana tab’a hannunta taja da baya. “Bansani ba ni miqo min Hanan in bata lunch nata.” “Zo ki bata anan yi hak’uri Mom Hanan” a hankali ya jawota ta zauna agefensa sannan ta amshi Hanan tafara shayar da ita yana zaune gefensu yana kallon su cike da adoration**** ★★★★ Life couldn’t be better, Anas, Fannah da Hanan nasu rayuwa na tafiya masu daidai se girma Hanan take wane kazan agric, tana girma tana kyau tana kuma sake kama da Daddy’nta, a yanzu haka Hanan nada 5 months tafara zama, yarinya son kowa k’in wanda ya rasa sede Fannah bata shiga da ita cikin jama’a ba kowa so yake ya karb’eta. _Mother’s day 8th May 2016 4:10PM A GIDAN MR. FAUZI_ D’an rumfa ne wanda k’ark’ashinsa su Ummie, Ummimi, Mami dasu Afrah da kowa da kowa ke zaune akai. Tun jiya Anas yaketa preparation na wannan babban rana he want to make Ummimi feel special on this special day. Atare Fannah dake riqe da Hanan a hannunta suka fito da Anas tasha wani purple lace wanda yayi fitting nata sosai, purple kaya tasawa Hanan ma, kullum haka suke suna anko. Wajen da Anas ya tanadar mata ta zauna sannan Anas yayi welcoming kowa da kowa wani k’atoton cake aka shigo dashi aka ajiye a tsakyan d’an taron daidai gaban Ummimi kenan da *HAPPY MOTHER’S DAY* rubuce akai. _“Ummimi on this special day I your son Anas, Shettima my brother and Amal our sister will love to show our love for you, thank you for being there for us all the time we love you so very much thank you for being the perfect mother”_ ya miqa hannu ya d’agota daga kan kujeran da take zaune. “And all the other mothers here, Mami, Ummie and my dear wife Fannah Happy Mother’s Day” nan duk suka mimmiqe sukayi cutting cake d’in sannan Anas yayi presenting gift nasa wa Ummimi, se Ummie se Mami haka duk sauran ma sukayi lastly yakai wa Fannah wani d’an medium sized cake da *I LOVE YOU MAMMY (HANAN)* rubuce akai “thank you Habeebi.” “Always Flower this is from Hanan ita tace in baki so thank her not me” murmushi ta saki sannan tayi pecking Hanan a lips. “And this is from me as a token of appreciation da kula mana da Hanan da kikeyi” amsa tayi ta bud’e white diamond ne aciki na d’an kunne d sarqa aciki. “Habeebi this is too much.” tafad’a disbelievingly. “Its not Flower because I love you.” ”I love you too.” Nana suka ci kuma sukayi wasa da cake suka b’ab’b’ata jikinsu, sunyi having fun like never ba k’arami ba yaro duk suka zage suka ta wasa daga k’arshe Ummimi tasamu Anas tamasa godiya sosai in person. *RAYUWAN HANAN* Dan nishad’i. _2 years later..._ Hanan an zama ‘yan mata fa yanzu tana da 2 years 5 months yanzu se uban surutu da rashin kunya kullum suna cikin fad’a da Fannah, Allah Allah Fannah ke asata a school tayi tayi da Anas yasata koda a pre school ne Anas yak’i acewarsa se Hanan takai 3 years tukuna. Badan komai Fannah keson asa Hanan a school ba illa dan ta huta daga headache da Hanan kesa mata, gashi bata san me ba duk abinda Hanan ta mata bata iya dukanta saboda yadda take son ‘yarta. Yau ranar ta kasance Tuesday k’arfe shidan da Fannah ke tashi dan ma Anas breakfast Hanan ke tashi itama sekace me alarm Fannah ta rasa ya hakan ke faruwa na farko bawai a d’aki d’aya suke kwana ba amman sede bata tashi ba Hanan ma seta tashi tana fitowa daga d’akinsu ta tarar da Hanan tsaye bakin k’ofan d’akinta da babban pink teddy bear nata da tsayinsu d’aya riqe a hannunta d’ayan hannun kuwa ribbons na kanta ne wanda da alama pincikesu tayi. “Good morning Mammy.” tace cikin siririyar muryarta me uban sauri. Gabanta Fannah ta nufa ta tsuguna “Good morning baby, Hanan sweetie yanzu kitson dana miki jiya kika warware duka? Ina sauran ribbons d’in?” Baki ta turo tayi nuni da d’akinta. “Sweetie mesa kika tsefe? Bana ce miki karki tsefe ba?” “Banacho! I want a new one.” ”Allah ka rufa min asiri!” Fannah tayi maganan tana kallon sama, “koma d’akinki ki kwanta kokuma kije kisamu Daddy a d’aki” tayi maganan tana kama mata dogon sumanta gu d’aya. Kafad’a Hanan ta buga ”ni jan biki kitchen.” “Saboda ki sake fasa min plates ba? Banaso koma ki kwanta” tana kaiwa nan ta nufa kitchen Hanan na biye da ita. Kaman dagske Hanan ta ajiye teddy nata a gefe ta d’alle kan kujera tana kallon mamanta na aiki chan ta miqa mata wuqa ganin Mammyn nata ta d’au albasa. “Good girl” Fannah tayi praising nata. Sid’ak sid’ak Hanan ta wuce store room taciro bucket da moping stick ta cika da ruwa sannan tajawo shi kitchen, inda ake ajiye morning fresh ta nufa tajuye roba d’aya ciki duk anan Fannah batasan me Hanan keyi ba as she is busy cooking. Yadda Hanan taga cleaners keyi itama ta soma mopping kitchen d’in Fannah na juyawa dan d’auko abu taga Hanan na mopping kafin tace Hanan bari aikin gama ya riga ya gama Hanan ta juye ruwa kusan rabin bucket a k’asa. “Aysha Hanan Fauzi!!! Yau sena zaneki a gidan nan” da gudu ta yi d’akin su taje ta d’ale jikin Anas anan shima ya tashi. “Daddy talk to Mammy wai seta min duka.” “Duka kuma?” ya maido da kallonsa kan Fannah. “Metayi kuma Flower da zaki ce zaki daka min little Fauzi?” “Habeebi ruwa kusan rabin bucket ta zubar a kitchen.” “Toh shine abin tada jijiyan wuya?” “Dama ai nasan haka zakace Hanan ki nutsu tam! Asata a school kak’i an bar yarinya se uban gagara oh ni Fannah zaki kasheni wallahi.” “Oya Hanan say sorry to Mammy.” “But Daddy..” “Shh! And say sorry.” “I’m sorry Mammy” tayi maganan hanneyenta riqe da kunnuwanta “barin sake ba.” “Allah sa Hanan” tana kaiwa nan takoma kitchen. ****_Some minutes afterwards..._ “Habeebi baraka tafi office da Hanan ba yau?” Fannah tayi maganan tana bottling wa Hanan shirt nata. “Inada very important meetings yau bareyi inje da ita ba gobe in shaa Allah zamuje ko little Fauzi?” “Yes Daddy!” ta fad’a tana jin dad’i. “Oh ni wallahi toh kaja mata kunne karta min gagara yau kuma karta shiga harkan cleaners.” “Who is a good girl?” “Aysha Hanan Fauzi!!” Hanan tayi maganan tana jin dad’i. “Good banda disturbing Mami kinji?” “Yes Daddy” Fannah na gama sa mata kaya taje tayi hugging Anas. *** _3:15PM_ Zaune Fannah ke akan gadon d’akinta daidai tagama ciro wa Hanan kayakinta daga drawer kenan. “Hello Habeebi ina jinka kace Moosa zezo?” Tayi maganan wayanta maqale a kunneta. “Eh zezo seki basa files dana bari akan gado earlier d’azu.” “Oka-” bata samu daman k’arisa maganan ba takira sunan Hanan da k’arfi “Haanaaan! Nooo!” Ai bata k’are maganan ba Hanan ta ture duka jeren da Fannah tayi gaban dressing mirron abinda ya kama kan turarukanta man shafawa komai da komai. “Hello Flower what is it?” Anas yayi maganan cike da tashin hankali acewarsa abu ne yasamu Hanan. “Habeebi wallahi yau sena zane Hanan.” “No please don’t metayi?” “Baraki matsa a wajen ba sena iso tukuna koh?!” Fannah ta tsawata mata, jin haka Hanan tabar d’akin ma gabad’aya tasa gudu da wani baby pink overall dake jikinta ta wuce nata sannan taje ta fara sabon b’arna achan, bin pages na story books nata take tana yayyage su one by one tana littering d’akin nata dasu. “Jeren dressing mirror na fa ta ture kap a k’asa.” “Flower please karki tab’ata.” “Wallahi Habeebi kabarni da ita” da k’yar Anas yayi convincing Fannah ta hak’ura. **** Hanan de ba wanda yasan ranan shiryuwanta gagaran yau daban na gobe daban Fannah tayi magana har tagaji batasan kuma me zata sake yima Hanan ba kotace zata bugeta bata iyawa, yanzu sede in Hanan tayi b’arna kawai ta kalleta ta kad’a kai tace Allah shiryeki yarinya kuwa ta amsa da Ameen Mammy tana mata murmushi nan kawai se Fannah taji ta huce. Akwai lokacin da ta kama Hanan da wuqa da albasa a kitchen ita wai a dole zata yanka albasa. Sede in Hanan bataga bayi a bud’e ba se ta saci jiki ta shiga takuma kulle da key sannan ta bud’e tap na jacuzzi ta cikasa dam da ruwa harya fara yoyo a k’asa, ita Fannah tsoronta ranan da Hanan zata fad’a cikin ruwan. Hanan nada shekara uku aka sata makaranta dad’i kaman ya kashe Fannah finally zata huta itama first day of Hanan a school ta koyo rubuta letter A believe me gidan Mr. Fauzi gabad’aya seda aka zana da capital letter A and Small letter a. Anas na dawowa daga office kafin ya shigo gida yaga letter A na masa sallama jikin k’ofa koda ya gwada gogewa kuwa bai goguwa kasancewar da permanent marker tayi rubutun tunanin ina tasamu ya soma chan ya tuna ashe jiya a gabanta ya miyar da markern bayan daya gama rubutu dashi. Bayan k’ofa ya bud’u masa ya shigo yaga a kan marble floor na parlourn ma an rubuta Aa baki ya tab’e sannan ya shiga kiran sunan ta. “Hanan! Daddy is home” alokacin Fannah na a d’akinsu tana baci itako Hanan tana d’akin Fannah taje ta bud’e drawer tacicciro ninkakkun kayakin Fannah tana hargitsa su fuskarta kuwa janbaki ne ko ta ina har akan girarta tana jin muryan Daddy tasoma k’ok’arin cire bangles da sark’ok’in Fannah datasa a wuyanta dakuma hannu sede kafin tagama cirewa Anas yashigo ya kamata. Murmushi ta hau mishi “Daddy!” “Omg Hanan what have you done?” Yayi maganar yana bin d’akin da kallo k’aran zuban ruwan daya keji a bathroom yasa yayi sauri ya bud’e ya duba, jacuzzi ya tarar cike dam da ruwa da sauri ya rufe yafito. “Little Fauzi ban hanaki tab’a kayan Mammy ba?” “Daddy you did” ta had’e rai. “Toh mesa kike b’ata mata kaya?” In kaiki amiki allura ko?” Dagudu ta je takama k’afansa “no Daddy nadena.” *© MIEMIEBEE*
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).