[7:58AM, 5/20/2016]
Ábbā-Gãñå WAYE SANADI?
15
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
tunda muka shiga mota bance kala ba har muka
je kabuga safiya kin yi shiru ko kina kewar baba
ne kaina ke ciwo ban cika son magana ba,nafi
bukatar kwanciya a wannan lokacin,na juyar da
kaina.wani tafkeken gate naga mun nufa bayan
mun shiga layin runfar shehu gidan horn din da
yayine ya dawo dani daga duniyar tunani ina
kallon wani yazo ya bude gate din tunda muka
shiga nake kallon aljanar duniya sannu da zuwa
alhaji yauwa magaji ya aikin.safiya fito mu shiga
sai a samo miki maganin ciwon kan,a sanyaye na
fito ina binsa a baya har muka shiga gidan
babban walo ne muka shiga.daddy sannu da
zuwa wata yarinya ta fada tana murmushi,"sannu
maryam ina umma? tana daki,daddy ina
bakuwarmu "safiyya shigo ki zauna ai daddy tana
bayanka aunty sannu da zuwa haka kawai naji
ina jin haushin yarinyar dakyar na taushi zuciyata
nace yawa na juyo ina kallonsa yana ta faman
murmushi ina ummata? safiyyya ki zauna yanzu
zata fito nanunan dakinta sanin halina yasa yace
ta so muje a cikin falon naga mun shiga wani dan
siririn loko sai gamu mun fito wani lafiyayyen
falon ya sha kujeru gefen dakuna guda
biyu.safiyya ga dakin ki wannan kuma na
ummanki da fatan dan gidan nawa ba laifi" na
juya na nufi dakin da yace na umma ta ne bbu ko
sallama na tusa kai tana zaune a kan sallaya
tana gani na ta taso da sauri tana dariya"oyoyo
nanata kwana bakwai kamar shekara dubu na
ganta wajena ina tunaninki sannu" sai da muka
karasa bakin gadonta ta zaunar dani yaushe ya
jeya dauko ki? umma kinyi kyau dan haka kika
nace sai kin aureshi ashe dadi kika gani,amma ni
vaba take min bakin ciki nima nazo na dandali
arziki. shigowarsa ce tasa nayi shiru "rukayya na
cika alkawari ga safiyyar mu nan na dauko mana
tazo gidanmu da fatan zaki zauna da
ummanki,please safiyya duk abinda akai miki ki
gayan zan dau mataki safiyya na dauke ki a
matsayin yata. rukayya baki kawo mata komai ba
kuma tace kanta yana ciwo na bawa khalifa key
yaje ya karbo mata magani in tasha sai ta
kwanta dan ta huta,khalifa da abba sun yi miki
sannu da zuwa sun zo ganin ummanki gobe zaki
koma bakin karatun nagaya musu kanki ke ciwo
gobe zaku hadu gun break bayan fitarsa umma ta
juya tana kallona yanzu abinda kike kin kyauta
mutumin nan yana yi mana hidima amma baki
taba budar bakinki kin masa godiya ba,
Abbagana hausa novels@ facebook.
[8:00AM, 5/20/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?
16
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
in yayi miki magana sai ki nuna kamar ba dake
yake ba,gaskiya in kina so mu shirya to ki gyara
halinki,kai umma har mutumin ya mallake miki
zuciya kin daina sona kuma da ki kace yana ta
hidima damu to ni nasa shi ko kiransa nayi dan
haka bbu abinda ya dame ni da nayi masa
godiya"na mike umma zan tafi tunda bakya
bukatar gani na,mijinki ya fini.haba nana ina
kuma zaki ya riga ya dauko ki kin riga kin dawo
nan kawai dan na fada miki gaskiya sai ki tafi ki
barni
"umma wannan ba gaskiya kika gayan ba,kawai
kin nuna bakya son ganina a gidan nan kuma
wallahi in har na bar gidannan ba gaida zani ba
sai dai na shiga duniya inda har abada ba zaki
kara ganni na ba ina fadar haka na juya zan fita
naji umma ta rike hannuna cikin sanyayar murya
tace kiyi hakiri nana insha Allahu bazan kara miki
fada ba tati ta lallashina har na sauko naci abinci
na sha magani umma tace to kije dakinki kwanta
kyafi sakewa umma kin san tare muke kwanciya
dan haka auranki bazai hanamu kwana tare ba na
juya na kwanta.washe gari bayan na idar da
sallah na koma na kwanta a hankali umma naji
tana bubbuga kafata na bude ido nana ki tashi
lokaci yana kurewa kuma tun dazu su abba suke
shigowa zaku gaisa.umma sai kace gaisuwar dole
ce "haba nana daure ki tashi kin ga zaki
makaranta kada lokaci ya kure sai lokacin na
tuna da makaranta na tashi na shiga toilet
gaskiya rayuwar hutu itace rayuwa Allah kayi
mana arziki,abinda na fadi kenan bayan na shiga
toilet naga umma tana zaune tana kallona a
zuciyarta addu'a take Allah yasa kada na bata
kunya.nana in kin shirya kizo muje mu gaisa
umma dawa zamu gaisa? nana ai kinsan gidan
bamu kadai bane gaskiya umma ba inda zani dole
ne sai mun gaisa nifa ban cika sonyin
magana,dasu bashi ba na gaya masa bbu ruwana
dasu ba" nana yanzu ban isa na saki abu kiyi ba
ai ko dan darajata kya je ku gaisa dan Allah kar
ki ban kunya ace daga zuwanki har kin fara
haka"Allah umma in dai naje yau bazan kara
zuwa ba na yarda nana Allah yayi miki albarka
taso muje na mike nabi bayanta duk kansu suna
falo muka karasa umma kin fito kanwarmu sannu
ya bakunta murmushi nayi musu na juya ina
kallon maryam aunty an tashi lafiya? lafiya
maryam aunty taso muje muyi break a,a,
Abbagana hausa novels@faceebook.
WAYE SANACI?? 15&16
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.