shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 3 January 2017

Waye Sanadi?? 85-- 90


[12/21/2016, 8:47 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣5⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Tare fa da Kawu muke ya tsaya gaisawa da Malam ina jin yanzu za su shigo...Kan ta rufe baki Malam ya yi sallama suka shigo tare da Abba Tunda suka shigo yake raba ido ya ga inda zai hange ni. Baba ta yi saurin shimfida tabarma Bayan sun gaisa shiru ta biyo baya sannan Umma ta leko suka gaisa.‘Baba duk wani abu da ya faru ya wuce don Allah Alhaji Muntari ya yi min bayanin abin da duk ya ja haka, kuma ga shi tun kafin a je ko’ina Allah ya bayyana gaskiya, kuma Allah ya yi wa Rakiya sakayya akan kishiyoyinta tun a duniya wanda su suka biyo ta Rasa suka dasa kiyayyar Rakiya da abin da za a haifa a zuciyarsa, ga shi tun kan a je ko’ina Allah ya nuna masu ikon sa, yau gashi gaskiya ta bayyana, ko me ya faru a baya ya zama tarihi, a yafi juna. Wanda ma ya halice mu muna masa laifi ya yafe mana ballantana kuma junanmu. Ina fatan komai ya wuce tunda shi ma ba yin kansa ba ne.”Baba ta dan sauke numfahsi ta ce, Allah ya yafe mana gaba daya, mu dama fatanmu Allah yasa ya gane gaskiya.”Abba ya jima yana ba wa Baba hakuri, sannan ya fito tare da malam, Rukayya ta ce, “Ki taso yau yawo za mu sha.”Da sauri Baba ta ce, “Au ba za ku bar mini ita ta dan kwana biyu ba.”Na ce, ‘Baba ba kwana za mu yiba, na gayawa Abba zai bar ni na kwana biyu, ina ta dokin ganin Ummata, amma ta ki mu yi hira gara na san Abbana ba zai ki hira da ni ba. Amma Baba ko dan ke mu kwana muna hira.” Rabu da ita Safiyya irin wannan bakar mara kunyar ce ta yi min babban SANADI, kuma da ba kya nan tana kwana da hotanki tana kuka.”Umma ta dago da sauri muna hada ido ta sunkuyar da kanta muna dariya muka fita da Momyna. Sai da muka jira Abba suka gama magana da Malam, sannan ya taho wajenmu. Na tsugunna har kasa na kara gaishe shi, hannunsa yasa ya dago ni yana murmushi ya ce,“Ai dama mun gaisa ko?” Na ce, ‘Eh Abba, amma in mun dada gaisawa baba wani laifi.”Na juya wajen Momy na ce, “Momy ina son mu je wajen Daddyfa.”Lallai Baby ba ki san yawon da za mu yi ba, yanzu ba, yanzu haka Yakasai za mu daga nan mu je Hotoro, sannan mu je Sharada gidan Abba.”Sauran yawo kuma Abba zai bar mu mu jo tunda kawu ya ban mota.”Na dan sanya fuskata, To yanzu yausihe za mu gidan su Sadiyya ‘Ki bari zamu sa rana, yanzu Hotoro za mu fara zuwa gidan Inna Binta.” Da sauri na ce,wa cece haka?”“Ke Yayar Kawu ce, ni kakata ce ke kuma babarkice Na dan yi murmushi na ce, “Abba kana ganin duk a yau za mu gama zuwa gidan da Momyna ta lissafo?“Insha Allahu za mu gama zuwa, dukka ninsu suna zimudi su ga diyar kaninsu. Yanzu Hotoro za mu fara zuwa, sannan mu je cikin gida (Yakasai).”tunda muka dau hanya Abba yake ba mu labarurruka masu dadi da ban dariya. Babu abin da muke ni da Momy sai dariya har muka karasa, ya yi parking a kofar wani madaidaicin gida. Mu muka fara shiga. Momy ta yi wani loko tana k walawa Baba Laure kira, ni dai ina bin ta a baya. Tana shiga falon suka ci karo da Sagir (Jikan Baba Laure ne). Ta dan rage fara’ar fuskarta suka gaisa. Ya juyo wajena kur ya kuran ido, na ja dan siririn tsakin da yasa ya dauke idonsa daga kaina.Momy ta ce, ‘Kafa tsare mana hanya muna son shigewa fa.”Ya dan yi murmushi yana shafa kansa, ‘Sorry Barrister, na dan tafi tunani.” Yana fadar_haka ya juyo wajena na daure na ce.“An yini lafiya?” Ban saurari amsar da zai bani ba na shiga falon.Muna shiga ta cafi sunana (Ban yi mamakin jin ta ambaci sunana ba). Na karasa gabanta na zauna kamar na yi magana, ta ci gaba da cewa. Duk wanda ya kalle ki ya ga jinin Muntari, ga shi nan kin debo shi kin kuma debo mahaifiyarki, ke har ma wannan berar kuna kama.” Tana maganar tana nuna Rukayya da take kwance a gadonta.Ta ce, “Kai Baba tsohuwa da ke har kin san kama?”Ina dariya muka gaisa. Momy ta ce, “Bara na yi kiran Kawuna...” Kan ta karasa suka shigo tare da Sagir. Mun shagala muna hira Momy ta mike ta ce,Kawu ka mance muna da tafiya mun tsaya biyewa ‘yar tsoh uwar nan, sai zuba mana rikici take yi, in kuma ba kya rikicin tsofa to ki lissafan uku uku sau uku da rabi.”Tana dariya ta ce, “Ni dai yau ba zan biye miki ba, bare ki wahalar da ni yau. Ina murna da zuwa ‘yata ke kam bana maraba da ke.”‘Au! Haka ki ka ce?” Da sauri ta ce, “Na fada.”“Shi kenan zan ga me Kara kawo miki ita.” Da sauri na ce, “Baba ko ba ta rako ni ba na san hanya zan dinga zuwar miki da kaina har sai kin gaji da ganina.”“Ni kam ba zan taba gajiya da ganinki ba.” Sannan ta juyo wajen Abba.“Amma dai barinsu za ka yi sai gobe? “Za dai ta zo ta kwanan yanzu za mu je Yakasai da can Sharadan.” Har waje sai da ta rako mu, Sagir ya miko min katuwar bakar leda.“Kanwata ga shi in ji Baba.” Nasa hannu na karba.Muna zuwa Yakasai gida ya rude da murna. Sai wajen karfe shida muka ta no tare da Baba da sadiya, don ita kam ta ce dole ta je ta ga ummanta.Sharada muka nufa na ga mun tsaya a get din wani tafkeken gida. Wani Buzu ya taso da saurinsa ya bude get din gidan tare dayi mana barka da zuwa abba ya Karasa rumfar ajiye motoci ya yi parking, muka fito,A hankali na cewa Momy, “Wannan gidan wa ye?”‘Gidan Kawu ne ”Gaskiya gidan ya burge ni, don iya haduwa ya hadu. Muna shiga babban falon gidan muka tadda kakar rukayya baba binta wanda suke gida tare da abbana Tana ganin shigowarmu ta mike da sauri ta nufa wajena tana faman washe baki.“Lale marhabin da Safiyya. Allah mai iko ai ko a hanya na ganki zan iya bada shaidar ke ‘yar Muntari ce. Ina Rakiya mahaifiyarki baiwar Allah?”Na karasa muka zauna. Ta kara tambayata, “Ina Rakiya? Bayan mun gaisa Abba ya mike ya shiga Bangarensa. Rukayya ta ce, “Wato Kakus kin manta da ni ko?” Baba Sadiya ta ce, “To ba dole mu manta da ke ba muna ta sabuwar ‘yarmu.” Baba Binta ta ce, “Ke ki ke ma ta ita, wata bera daita.” ‘Okey na yarda ni din bera ce, amma bari bera ta tambaye ku in dai ku ka ban amsa ni na san kyautar da zan muku Ni dai ina zaune ban da dariya babu abin da nake yi. Momy ta ci gaba da cewa, “Ku gayan arba’in da hudu a tara da sha uku da kuma rabin arba’in da uku.”Baba Sadiya ta ce, “Ni kam yau ba za ki wahalar da ni ba, z a ki fara lissafin abin da ba zai kirgu ba.”Baba Binta ta ce, “Kin ga Halima (Sadiya) rabu da bera ko saurayi ba ta da shi.”Na dan juyo wajen Momy na ce, “Momy ina san zan yi fitsari.” Ta mike muka shiga barin da Baba Binta take.Sai karfe bakwai muka taho daga gidan Kai tsaye gidan Momy muka nufa, Tun kafin mu karasa yin parking Hajiya ta fito, ina fiitowa ta rungume ni.Tana rike da ni har muka karasa falon, na dan zamo daga kan kujerar da nake muka gaisa. Momy ta ce, “Hajiya kin kasa magana sai kallonta ki ke?” Ta dan yi dariya, ‘Farin ciki ya cikan zuciya nama kasa magana, sai Allah mun gode maka.” Ta shiga kiran Salim ya fito da saurinsa. Yana ganina ya tsaya cikin tsantsan mamaki, sai kuma ya hau dariya.Baba Sadiya ta ce, ‘To shashasha haka ake murnar kasa mu a gaba kana dariya?” Ya juyo wajenta da sauri, ya dan tabe baki ya ce, “Yau ma kin zo biko na ne, na ce na sake ki saki dubu, bana auren yanzu an daina yayanki sai yarinya sabon jin....” Dukan da ya ji a bayansa shi ya hana shi karasa abin da yake bakinsa. Ya juya da sauri sukayi ido hudu da Abbansa ya matsa gefe da sauri yana shafa keya.Abba ya ce, “Wato ka sa min mahaifiya a gaba kana mata dan biki.”“No Abba soyayya fa muke.” Ya juyo yana kallon Baba Sadiyya ya ce, “Darling ki gaya masa don Allah ba soyayya muke ba?”Tana dariya ta ce, ‘Gaskiyar na karfen muna maganar zuwa hoto ne ka zo kana dukar min maigidana. Dukkan mu muka sa dariya.Sai wajen karfe takwas muka fito daga gidansu Momy. Dakyar Momy ta yarda na taho mu da Baba Sadiya. Ina shiga soron gidanmu na jiyo hayaniyar Baba na karasa da saurii Tana garina, tace Yauwa ga yar halak.” Ina shiga falon na hangi Alhaji Nasir tare da imran sai ‘yan sanda biyu da suke bayan Imran. Baba ta ce, “Zo nan ki zauna daman maganarki muke,”Na ce “Baba tare muke da Abbana Yauwa maza ki yi kiransa ya shigo,”Bayan sun shigo na mike zan shiga daki Abba ya dakatar da ni na dawo na zauna kusa da kafarsa.‘Baba me ye yake faruwa ne?” Abba ya tambaya. Baba ta ce, “Wannan shashashan yaron ne ya zo mana da wata magana wai Safiyya matarsa ce don an daura musu aure a can inda ya tsare ta.”Cikin fusbi Abba ya ce, “Kai ba ma son iskancin banza, don ka ga mun rabu da kai ba mu dau matakin Boye mana ya da ka yiba shi ne za ka zuwa da mutane da maganar banza. To uban wa ye ya daura muku auren? Wallahi ka yi sa’a na rabu da kai ne darajar mahaifiyarka da Alhaji Nasir ne. Dube ka a haka kamar mutumin kirki.”Ya dago fuskarshi cike da ruwan hawaye, muryarsa na rawa ya ce, “Abba na san na yi muku laifin da na cancanci duk wani hukunci, kuma wallahi ban boye Safiyya don wani abu ba, sai don in ceto ta daga fadawa mugun hannu. Ina kaunarta tsakanina da Allah, na rantse da girman Allah Safiyya matata ce saboda kakana ya daura mana aure kuma ku tambaye ta ga ta nan da amincewarta aka daura mana aure.” Ya juyo gare ni.Kaina yana kasa, amma jikina ya ban ni yake kallo. Na ji muryarshi ta doki zuciyata. “Safiyya ki gaya musu gaskiya tsakaninki da Allah ke ba....” Kuka ya ci karfinsa ya kasa karasawa.Falon ya yi shiru babu abin da ka ke ji sai ajiyar zuciyar Imran. Abbana jikinsa ya yi sanyi da jin kalaman Imran. Baba Sadiya ta kalle ni ta ce.“Safiyya ki fadi tsakaninki da Allah shin da aurensa a kanki?”Na yi shiru har sai da Alhaji Nasir ya kara tambayar, sannan na ce, “Na san an daura mana aure da shi, amma bisa sharadin da an daura zai sake ni na taho Kano.” Na dan yi shiru. Abba ya ce, “Ki yi magana mana, to me?”“Abba tunda aka daura nake nacin ya sake ni ya ki har zuwa ranar da na taho.”Baba ta ce, ‘Yanzu dai kenan da aurensa a kanki?” Kafin na yi magana Abba ya ce, ‘To kai Imran mun yarda an daura muku aure, to kuma ga shi ta fada kun yi bisa sharadin za ka sake ta, don haka ya zame maka dole a yanzu ka sake ta Ya hau girgiza kai. “Abba ba zan taba sakin Safiyya ba ko da za ku dau raina, ina fatan na mutu a mijin . Safiyya. Ina sonta tsakanin da Allah, kuma ita ma tana sona.Na dago da sauri na kalle shi cikin sa’a muka hada ido nayi saurin dauke idona. Na ce, “Allah ni karya yake min bana sonsa bana kaunarsa, mai sonsa ma bana sonsa.”Baba ta ce, “Ni kaina bana fatan ki auri wannan ' mugun kuma ko ta tsiya sai ka sake ta.”Baba Sadiyya ta ce, ‘A dai bi komai a sannu kar mu yi shishigi a lamarin Alla..”Kan ta karasa dansandan da yake bayan Imran ya ce, ‘Lokacin ka ya yi magana suka mayar da ankwar da take hannunsa Na juyo wajen Abba da sauri na ce, “Don Allah Abba kasa ya sake ni kar ya tafi. Kar ki damu kanki Safiyya ya zama dole ya sake ki. Alhaji Nasir ya ce, ‘In ma bai sake ta ba Court ya raba auren Har sun kai bakin ksofa Imran ya juyo fuskarsa cike da hawaye ya ce, “Dady ina fatan samun goyen baya daga wajenka, amma kai ka fara shigowa da maganar court, to wallahi ban ga court din da za ta raba auren....’Kan ya karasa ‘yansanda suka hankada shi waje 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/22/2016, 9:51 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣6⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Haba Momy bai kamata a ce kin bar Imran cikin wannan halin ba, ni zan yi shaidar dan uwana ba zai aikata wani mugun abin ba a kan yarinyar ba.”“Ki yi min shiru! Ina tunanin duk halinku daya kana min maganar banza, yaro ya zubar min da mutunci a gaban jama’a bai ji kunyar Allah ba ya dauke ‘yar mutane mahaifiyar yarinyar nan har nan garin suka zo kuma tare da shi ake fita nemanta. Allah ya tsinewa irin son da yake mata, shi kansa Alhajin ya ce kar na kuskura na karbo shi.”Yusuf ya dan goge gumin da ya yi wa fuskarsa sallama ya dan sauke numfashi ya ce, “To ai Momy Malam ya je har gidan da ya boye yarinyar ya kuma daura musu aur....“Ban gane ba?” Ta furta da sauri.“Ina nufin ita yarinyar matarsa ce, malam kakanmu ya je da jama’arsa an daura musu aure da ita.”Stop! Yusuf ban san maganar banza Imran ya yi aure ba mu sani ba, lallai ya daukowa kansa...”Wayarta ta hau kara ta yi saurin dagawa. Tana gama wayar ta juyo wajensa.“Gobe Abbanku zai dawo, jikin Alhajin Sabon gida ya motsa.” Tana fadar haka ta mi ke ta shiga daki.Ya mike jikinsa a sanyaye ya fito daga falon, suka ci karo da Khadijah tana tsugunne babu abin da take sai aikin kuka. Ya karaso wajenta da sauri.“Lafiyarki Khadijah ki ke kuka?”Ta dago fuskarta cike da hawaye, kan ta yi magana ya kama hannunta suka shiga cikin dakinsa. Suna shiga ya zaunar da ita a gefen gadon. Ya tsugunna a gabanta.“Sister ki bar kuka na san kina tausayawa dan uwanmu halin da ya shiga, ina ganin kuka ba zai zama mafita a gare mu ba.”Cikin shashshekar kuka ta ce, “To yanzu yaya haka za a bar shi bara A je a karbo shi ba. Wallahi Yaya bai tsare Safiyya don ya cutar da ita ba, sai don ya taimake ta. Amma bai kamata Momy ta rabu da shi ba.”“Khadijah ba laifin Momy ba ne kin san irin kaunar da Momy take wa Imran Dady ne ya umarce ta da yin haka.”Na ce, “Yaya ga shawara.”“Yauwa kanwata na san yanzu za ki nemar mana mafita ina sauraranki.“Yaya ka taso yanzu mu je wajen Malam mu yi masa bayanin halin da ake ciki, na san.” Kan ta karasa ya rike hannunta suka fita. *** **** **** *** Karfe takwas Malam ya shigo gidan, na fito daga daki muka gaisa na mike zan koma ya kira sunana. Na juyo ya ce, kije abbanki ya zo ku je unguwa, daman na riga na gama nada kayana tuuda yau kwanana biyu a gidanmu.Baba ta ce, “Malam ka ce ya shigo mana.Kan ta karasa Umma tana jin Baba ta ce ya shigo ta mike ta yi cikin dakin. Bayan ya shigo sun gaisa Baba ta ce, ‘Ya maganar yaron nan.”Abba ya ce “Mun yi waya da Babansa ina tunanin gobe zai dawo, kuma zai sauka a nan garin, in ya sauka gobe zan zo na debe ku gaba dayanku mu je har gidan kakanin yaron tunda a ranar za a yo ballensa.”Allah ya kai mu ai gara a yi ta ta kare.”Ya mike suka fito tare da Malam, na juya ina kallon Umma na ce, “Umma zan tafi, amma ba zan dade ba saboda bana san na yi nesa da su Hassan, tunda na ga Umma ba ki damu da ni ba.”Ta dan yi murmushi, sannan ta ce, “Suma su Hassan ba sa san ki yi nesa da su.” Ta dan yi shiru tana kallon Baba, sannan ta juyo wajcna a hankali ta ce.“Yaushe za ki dawo?”Da saurina na ce, “no in ba kya so na tafi ki gayan sai na yi zamana.”Ta girgizan kai tare da kallon Baba. Na ce, “Umma ki daina kallon Baba in ba kya so na tafi to na leka na gayawa Abba na fasa bin sa na fi san zama a hannun Ummata, tunda tun farko tafi kaunata, shi din bai rike ni a lokacin da nake bukatar kulawarsa bar aka yi min gori ana kora ta.”Baba ta dago kai tana dariya, sannan ta ce, “Ni ban kore ki ba ke ki ka kori kan ki. Kin bar babanki a tsaye yana jiranki.”“No Baba ba zan tafi ba, Umma ba ta san na tafi na bar ta.”‘Ke bana san shashanci, ma za dauko kayanki ki bi mahaifinki.”Ta juyo wajen Umma ta ce, “Ke kuma ce miki ta yi in ta tafi ba za ta dawo ba da za ki hana ta bin mahaifinta?” Umma ta ce, “Baba ba hana ta na yi ba, ita ce ta tsaya.”Na dauko jakata ina dariya na ce, ‘Umma kar ki damu gobe insha Allahu zan zo na ganki.” Ina fadar haka na fita Yana jingine jikin motar ya zubawa kofar gidan ido, Yana ganin fitowa ta ya hau murmushi har na karaso na tsugunna na kara gaishe shi. Yasa hannunsa ya dago ni. Ai mun gaisa Safiyya, shiga mota mu je.” Na zagaya na shiga.Muna tafe yana min hira har muka karasa gidan. Ya yi parking kusa da wata sabuwar mota ‘yar karama mai kyau na duba bayanta na ga an rubuta Picanto, ya zagayo yana taba motar, sannan ya miko min key.“Abba na mene ne?” Na ce da shi ina kallonsa.“Ga shi nan ki gayan wadda ki ke so sai a canja miki.”Nama rasa bakin magana saboda tsabar farin ciki.“Safiyya na ga kin yi shiru ko ba ta yi miki ba?”Na girgiza kai na ce, “Abba ta yi min, na gode Allah ya kara budi.”“Me ye abin godiya Safiyya ke ‘yata ce zan iya yi miki abin da ya fi haka.”Yana fadar haka ya shiga ciki na bi bayansa. Baba Binta tana zaune a dakinta tana sauraran rediyo na shiga ta dago da saurintn cikin mamaki.‘Oho ni Binta yanzu Muntari ka yi sammako ka dauko ta kamar bazaku kara haduwa ba.”Na karasa kusa da ita na gaishe ta, ta amsa tare da tambayar Ummata na ce tana nan kalau tana ma gaishe ki.“Ina amsawa.’ Ta juyo wajen Abba.“In ce ko kana idar da sallah ka tafi don ni kwata- kwata ban ga fitarka ba?”“A’a Yaya na leko kina barci shi yasa ban tashe ki ba.” Ya mike. “Bara na karya na fita.” Yana fadar haka ya fita daga dakin.Baba Binta ta juyo wajena, Maza Safiyya je ki madafi ki daukar masa kayan karyawar ki kai masa.Na mike na fita ina mamakin aikena da ta yi tunda ni dai ban san ko ina ba a cikin gidan. Na fito na tsaya a falon ina tunanin inda zan nufa da zai kai ni kicin. Na bude wata kofa da na ganta kusa da dakin Baba Binta. A zatona shi ne kicin din, sai na ga akasin haka. Ashe wani hadadden daki ne wanda daga gani kwanan nan aka hada shi don komai sabo ne a ciki. Na kai kallona kan lafiyayyen gadon da ya sha gyara. Kai duk haduwar dakina na gidan Alhaji Nasir sai na raina shi da na ga wannan dan iya tsaruwa dakin ya tsaru.Na kai kallona kan tafkekiyar Plasma din da ke like a bango ga carpet ya malale dakin babu abin da ke tashi a dakin sai sassanyan kamshi. Na yi saurin janyo kofar na rufe sakamakon motsin da na ji. Na juyo na hango Abba ya fito daga wani dan karamin waje kamar gida hannunsa dauke da tire na karasa na karba. Kai tsaye dakina sa ya nufa na bi bayansa moka shiga. Kai duk haduwar dakin da na gani sai na raina shi da na ga wannan ya ninka shi kyau da tsaruwa. Na karasa inda na ga dinning table na aje. Abba ya yi cikin dakin ni kuma na samu waje na zauna. Bayan kamar minti sha biyar ya fito ga dukkan alamu ya yi shirin fita ne ya karasa dinning table din ya zauna, sannan ya juyo wajena ya ce.‘Safiyya ki taso ke ma ki karya mana.”Na ce, “Abba na koshi na yi break fast tun a gida.To taso ki min hira na ga duk kin ki sakin jikin ki ko ba kya san rabuwa da Umman taki ne?” Na yi shiru ina murmushi.“Ki zo nan ki zauna.Ban yi musu ba na taso na zauna, sannan ya hada tea ya fara sha. Na san kin fi son Ummanki da ni ko?” Na dago da sauri ina girgiza kai na ce, “Abba kai ma ina son ka sosai ina farin ciki da ka zamanto mahaifma.”‘To na gode Safiyya.” Ya dan yi shiru yana kallona. Sannan ya sauke numfashi.‘Safiyya me zai hana ki zame min SANAD1N dawowar Ummanki gare ni.”Na dago kaina da sauri muka hada ido na yi saurin dauke kaina.‘Safiyya ba kya so Ummanki ta dawo gare ni, kin fi san ta koma gidan Alhaji Nasir ko?”Da sauri na ce, ‘Wallahi Abba na fi so Umma ta dawo gidanka ko a mafarki bana fatan ta koma gidan Alhaji Nasir.”“To za ki shige min gaba.Na daga masa kai ina dariya.‘Yauwa Safiyya Allah ya yi miki albarka.” Na ce, ‘Amin Abba Kin san Kawun ki (yana nufin Abban Momyna) ya shirya muku tafi kc da RuRayya? Nima ,.uma na shirya muku tafiya to amma wannan yaron da ya zo da wannan maganar ya dakatar da mu don da tuni yanzu kuna Dubai.Na ce, “Abba me ye ruwansa da tafiyarmu?”‘Uhm! Safiyya ke matarsa ce a yanzu yana da hakki a kanki, don haka ba za ku tafi ba har sai ya sake ki.“To don Allah Abba ka je yau ka takura masa sai ya sake ni, ni bana son sa, ko me sunansa bana so. Allah Abba ko zai mutu akan sona ba zan so shi ba.” Ya zama dole ya sake ki gobe mahaifinsa zai zo da ni da ke har ma da Baba da Malam Mado za mu je can gidan a yi ta ta kare.” Na ce, “Yanzu Abba shi kenan na zama bazawara? Ina fadar haka nasa masa kuka. Hankalin Abba ya tashi ya hau lallashina. Wa ye ya ce miki kin zama bazawara? Ai babu abin da ya shiga tsakaninku ko? Kunya ta kama ni na yi saurin sunkuyar da kaina, sannan na daga masa kai.“To har yanzu ke budurwa ce aurc kawai aka daura muku, kuma shi za a warwarc. Kin ji share hawaycnki mu je na nuna miki dakin ki.”Na mike ina goge fuskata muka fita. Dakin da na bude dazu na ga Abba ya bude muka shiga na tsaya ina kallonsa cikin mamaki.“Safiyya ga dakinki ina fatan ya yi miki?”Ina dariya na ce, “Kai Abba ya yi min kyau sosai, amma ina tsoron kwana ni daya ba zan dinga zuwa dakin Baba na dinga kwana ba, ko kuma kasa Momy ta dawo mu dinga kwana tare zan fi jin dadi. In ta zo anjima ba zan bar ta ta tafi ba.”Ya fita ya shiga dakin Baba sannan ya dawo dakin ya mikon kudi.“Ga shi ko za a kawo talla in kin ga kina so sai ki siya.”Bai fi minti goma da fita ba Momy suka zo tare da Sadiya. Da gudu na taso na tare su na fada jikin Sadiya ina murna, har muka karasa falon ina jikin Sadiyya. Muka zube kan kujra ina dariya na ce, “Sister...” Sai kuma na yi shiru. Momy ta ce, Ki karasa mana.”Na dan yi murmushi, “Momy babu abin da zan ce.Sadiyya ta ce ko so ki ke mu gaya miki halin da Imran ya...” Kan ta karasa na katse ta cikin shagwaba na ce.‘Allah in ki ka kara yi min hirarsa zan gayawa Abba, ko Abba na gaya masa ban san hirarsa Allah zan iya mutuwa.”Ina fadar haka nasa mata kuka.“Lallai yarinyar nan Kawu ya shagwaba ki daga magana za ki sa mana kuka, bara na tuna miki wani abu a karshen wasikar da ki ka samin a jakata.”Sadiyya ta ce, “Kwarai Rukayya tuna mata.”Momy ta ce, “Ki ka ce ki min jaje Momy zuciyata ta kamu da ciwon son Imran na san lokacin da ki ke karanta wasikar nan na yi nisa da barin binin kano, ki bawa Imran hakurin rashina kuma ki gaya masa sakona ta....” Kan ta karasa na rufe mata baki.“Momy bana so Allah zan hada ki da Baba.” Na shiga kwala mata kirata fito da saurinta tana tambayata lafiya? Tana ganin momy ta tsaya.Momy ta ce, wato yar tsohuwa shi ne ki ka shagwaba yarinyar nan daga mun yi mata magana tasa mana kuka?”Ta karaso tana harararta, sannan ta kai dubanta ga Sadiyya.“Kin ci sa’a kina tare da bakuwa, amma da sai kin ga yadda ake daka bera.”Na ce, “Baba har bakuwar suke min kuma ita bakuwar ma kishiyarki ce budurwar Yaya Salim ce.” Tana dariya ta ce, “Ki ce kishiyata ce ta biyu ni har gida. To da me ki ka zo ko dan kin ga na bar miki ragowata to gayan da me ki ka zo da fada ko da neman sulhu? 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/23/2016, 10:30 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣7⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.c Sadiya dai ta kasa magana sai dariya. Ta zamo daga kan kujerar da take zaune suka gaisa da Baba. Momy ta ce ‘“Yar tsohuwa ko karyawa ba mu yi ba muka taho ganin Safiyya mun zo tana mana kukan shagwaba wai ba ta san hirar mijinta.Na nanata kalmar mijinta na ce wa ye mijin nawa?Baba ta ce, “Kin ga ‘yata rabu da su kar su bata miki rai .” Sannan ta juyo wajen Momy.“Ba dan ke zan kawo muku kayan karyawa ba, sai dan kishiyata, ta san nima na iya girki.”Tana tafiya na ja hannun Sadiyya ina cewa, ‘Zo ki ga dakina.Tunda muka shiga ba mu muka fito ba sai da Abba ya dawo wajen karfe hudu, dukkanmu muka shiga cikin dakinsa.Yana ganin Rukayya ya rike baki cikin mamaki ya ce, “Kuna ina ban ji hayaniyarki kina wahalar min da yayata ba?”Ta dan yi murmushi ‘Kawu muna dakin Safiyya tana ta zuba mana shagwaba.”Ya ce, “To ai Rukayya, Safiyya rainan ku ce, ku ne ku ka koya mata shagwaba, na ga kanwar taku saurin kuka gare ta, ko Sadiyya?”Momy ta ce, “Lah! Ni Kawu ban da saurin kuka ko da ina yarinya bare kuma yanzu sai dai Sadiyya.” Da sauri Sadiyya ta ce, “Kar ki min sharri Allah Abba ita ta shagwabata da muna school, ko laifi ta yi ba ta yi mata fada.” Na karasa gabansa na yi masa sannu da zuwa. Bayan mun gaisa ya juyo wajen Momy. Da fatan duk kin hado kayanki?”“Kawu na fasa dawowa nan.”Na yi saurin dagowa ina kallonta, Abba ya ce, “Saboda me? Gaskiya Kawu in na dawo kullum sai mun dinga fada da Safiyya ga shagwabar da ta tsira magana daya ta sa ma kuka.Na yi saurin tsugunna a gabanta na kama hannunta.“Don Allah ki yi hakuri ki dawo Allah na daina kukan, kuma ba za mu dinga fada ba.” Haka ko a school ki ke cewa kin daina min laifi, kuma ki kara zan kwana daya in na ga kin canza shi kenan.“Eh na yarda, ke ma Sadiyya don Allah ki dawo nan gidan duka mu hadu.” To zan dawo, amma ba yanzu ba.Na ce, “To yaushe za ki dawo?Tana dariya ta ce, “Sai na gayawa Baffana in ya bar ni zan dawo.Abba ya mike.“ko zamuje kuga motoci Muka biyo shi har gate ya umarci mai gadin da ya bude masa wasu motoci biyu da suke lullube yana bude su na ga irin tawa ce da ya nunan dazu.Ya ce, “Dazu na bawa Safiyya key din ta, ku kuma ga taku.”Momy ta yi wani tsalle ta dire gaban Kawu ta ce, “Kawu da gaske ka canjan mota?” Ya daga mata kai yana murmushi. Sadiyya ko ta ma kasa magana ganin abin take kamar a mafarki yau ita ce SANADIN Safiyya ta yi mota.“Allah na gode maka.” Ta zube gaban Kawu tana masa godiya. WASHE GARI Misalin karfe sha biyu, Abba ya dawo lokacin mu da Momy muna dakin Baba. Mu kai masa sannu da zuwa ya ce maza ku taso mu je tun dazu Alhaji Nasir yake min waya.Na ce, Abba ni wallahi bana san zuwa kawai ka je ku da Momy.Ya dan hade fuska “Ban san shirme, Rukayya ta ce maza taso.” Na mike da sauri na shiga dakina. Daman lokacin doguwar riga ce a jikinmu iri daya mu da Momy na dauko wani karamin hijabi fari nasa muka fito har ya fitar da motar da za mu hau.Kai tsaye Dorayi muka nufa muka dau Baba da Malam Mado, na so Umma ta bi mu amma ta ki haka muka tafi.Har muka je cikin Nassarawa Abba ya yi kiran Alhaji Nasir ya gaya masa inda muke. Bai fi minti uku ba ya zo muka tafi. Tunda muka shiga gate din gidan kirjina yake ta harbawa da sauri da sauri. Motoci sun fi goma a cikin gate din muka fita. Alhaji Nasir ya yi mana jagora har wani tafkeken falo. Ganin takalma rututu, jikina ya bani da mutane a falon. Momy ta matso kusa da da ni cikin rada ta ce. Me ye haka ne ki nutsu fa.Daga bayanmu Baba ta ce, “’Yar nan ni kaina na kasa nutsuwa.” Muka shiga falon Abba da Alhaji Nasir suna gabanmu. Mutane ne kusan su goma a cikin falo kamar an ce kalli gefenki na hange shi ya hada kai da bango. Kallo daya za kai masa ka hango muguwar ramar da ya yi ga uban baki kamar angoga masa bayan tukunya idansa duk sun kumbura kamar mai ciwon ido.Na ji an kama hannuna na juyo da sauri muka hada ido da Khadija, fuskarta dauke da murmushi, na yi saurin zama a kusa da ita. Abba ma suka samu waje kusa da wani tsoho wanda ban manta ba har da shi aka daura aurcna da Imran. Inda na zauna a nan su Baba suka zauna. Malam kuma yana tare da su Abbana. Kanmu na kasa muka gaisa da kowa.Dakin ya dan yi shiru, Malam Khalil ya ce, “Ku dan yi hakuri Salisun ya shiga ciki fito da Alhaji Dahiru.” Yana maganar yana kallon Abbana.Abba ya ce, “Babu komai, muma ai kun yi jiranmu.” Aka shiga falon tare da sallama. Idonsa cikin idon Baba cak ya tsaya bai yi gaba ba, kuma bai juya baya ba, daga bayansa Alhaji Salisu ya ce.‘Abba mu je mana ko kafar ce ta tashi?” Cikin rawar murya ya cc, ‘Maza ka kirawo min Hajiya.”Muryarsa da Baba ta ji nc yasa ta dago kanta da sauri, ba ita ba hatta Malam Mado sai da ya dago kansa yana kallonsa.Yusuf ya mike da sauri ya riko hanun kakansa ya kai shi kusa da mallam kalil haryanzu idonsa yana kan Baba ita ma din hakance ta kasance da ita. Har yanzu Baba da malam Mado suna kallonsa Ni kam ban san me ye yake faruwa ba kaina na kasa.Malam Khalil ya ce, “Alhaji Dahiru lafiya ko ka san su ne?“Ni ko na san su farin sani.”Malam Mado ya ce, ‘Muma mun sanka bakin sani, tunda ka yi mana SANADIN barinmu mahaifarmu. Ina dan mu da ka gudu da shi. Kalaman shiga kunnuwanmu. Daidai lokacin Alhaji Salisu ya shigo. da Doctor Khadija da kuma Hajiya, ga kuma Aysha a bayansu.Malam Mado ya kara tambayar Alhaji Dahiru “Ina dan mu ko ka siyar da shi.” Muryar Alhaji Dahiru tana rawa ya ce, “Ban saida danku ba sai rayuwarsa da na inganta masa har ya zama abin alfaharinku. Ga danku ya shigo.” Ya nuna masu Alhaji Salisu da hannu.Da sauri ya karaso gaban Alhaji Dahiru. Abbana ya ce, ‘Malam ya ku ke magana a baibai ne, kuma muna bayani dukkanmu kun saka mu cikin rudani.”Dahir (Yayan Imran) ya ce, ‘Alhaji Suf....” Kan ya karasa Alhaji Dahiru ya ce, Don Allah ki musu bayani ke kadai ce za ki musu bayanin da za su gane abin da ya faru.” Yana maganar yana nuna Baba.Ba ta yi musu ba ta ba su labarin abin da ya faru a takaice. Baba tana gama ba su labarin Alhaji Salisu ya ce, “Abba da gaske ba kai ka haife ni ba?”Ya daga masa kai idonsa cike da ruwan hawaye, sannan ya ce, “Salisu ga mahaifiyarka.” Ya nuna Baba.“Na san a labarin da ta bayar yanzu na san dukkanl kuna tuhuma ta me yasa akan me yasa na dauko shi? Na yi haka ne don na inganta rayuwar ya samu kyakkyawar kula da ilimi uwa-uba kuma da kaunarsa da ta shiga zuciyata a lokacin ina cikin radatfin rashin haihuwa. A lokacin mun fi shekara goma da aure, amma Allah bai ba mu haihuwa ba. Bayan zuwan Salisu da shekara biyu Allah ya ba mu kyautar Yusuf kwanansa daya ya mutu, ba mu kara samun haihuwa ba sai da Salisu ya cika shekara goma sha biyar muka haifi Khadija.Daga ita Allah bai kara ba mu haihuwa ba har kawo yanzu. Tare suka tashi da Salisu. Duk wani abu tare muke musu har kawo yau da Allah ya bayyana su Baba. Ina fatan za ka yafen boye maka gaskiya da na yi a da wanda a ‘yan kwanakin nan da jikina ya matsan nakc shirin gaya maka gaskiya ko da ta Allah za ta kasance a gare ni gudun rikici To sai ga shi cikin sauki Allah ya kawo iyayenka.Malam Khalil yana girgiza kai ya ce, “Ikon Allah ya fi ga haka, dole Imrana ya kaunaci Safiyya ashe kanwarsa ce Ni kam saboda tsabar mamaki nama kasa dago kaina zuciyata cike da mamakin Baban Imran mutumin da na tsana a rayuwata, mahaifinsa shi ne yayan Ummata. To yanzu me ma tsayin sa a wajena? Maganar Hajiya Amina ce ta katse min tunani. Na dago da saurina, fuskarta cike da murmushi ta ce, “Tunanin me ki ke Abbanki yana kiranki Na kai dubana wajen da Abbana yake zaune na ga ban gan shi ba, ta ja hannuna har gaban Alhaji Salisu na tsugunna a gabansa kaina na kasa na gaishe shi.Daidai lokacin Abba ya shigo a she waya ya fita ya amsa. Alhaji dahiru ya ce, Yanzu kam matsalar Imran ta zama ta gida. Kai muktar kai ne mahaifin Saflyya don haka kai ne za ka duba abin da ya gudana tsakaninsu.”Abbana ya ce, “Maganarta gaskiya ce ni kam zan zamo uba ga Imran, kuma na tabbata Rukayya (yana nufin Ummata) za ta goyi bayan danta, amma kafin haka muna so mu ji daga bakin Malam me ye gaskiya radan a kan aurensa da Safiyya shin kai ne ka daura kamar yadda ya gaya mana?Malam Khalil ya ce, “Tabbas nina daurawa Imran aure da Safiyya.”Hajiya Amina ta ce, “Malam kalin ta yarda a daura musu aure ya mata alkawarin da an daura zai sake ta?” Doctor Khadija ta ce, “Ni ina ganin duk abin da ya faru a baya a tsakaninku ki ture shi Safiyya, Imran yana kaunarki ki tausaya masa halin da ya shiga haka.Shi ma Yaya Dahir ya ce, ‘Kanwata ina da yancin zabar miki miji don haka na zaba miki yayanki a matsayin miji ina fatan ba za ki ban kunya ba.” Na daure na yi murmushin da bai kai zuci ba ganin yadda kowa yake ta magana. Ni dai kaina na kasa. Safiyya ya ce babu wanda zai wa ‘yata auren dole ya zama dole Imran ya sake ta a yanzu-yanzu.Tunda suka fara magana bai daga ko idonsa ya kalle su ba sai yanzu da ya ji maganar da mahaifinsa ta furta ya juyo a razane ya dago kansa. Idonsa fal da ruwan hawaye, yana kallon fuskar mahaifin nasa ya kara kwatsa masa tsawa.“Maza ka sake ta kamar yadda ki kai bisa sharadi?” “Ba zan iya ba Dady ba zan taba iya budar baki na saki Safiyya ba ku bari in ciwon sonta ya kashe ni Dady ko a mafarki bana fatan bakina ya furta kalmar da za ta batawa Safiyya rai bare ta kai mu...”Kan ya karasa Alhaji Nasir ya katse shi da cewa, “Ka yi shiru da bakinka Imran insha Allahu babu wanda zai raba ku da matarka taso mu je waje ka ji.Bai yi musu ba ya bi bayansa.Kiran sallar da aka yi ne ya tashi kowa. Muna fitowa daga falon na bi bayan Abbana ya juyo da sauri Lafiya Safiyya? Sai da na waiga na ga babu kowa a bayana sannan na karasa gabansa na fara kuka. Ya dago fuskata.‘Me ye ya saki kuka, muna cikin farin ciki za ki bata ranki? .Cikin shagwaba na ce, “Ni fa Abba bana son sa Allah in kuka auran shi zan iya mutuwa.”“Kin ga ki bari in mun je gida ma yi wannan maganar, yanzu ki shiga ciki ki yi sallah.”Ni dai ba zan koma ba gida zan tafi ka ban key din motarka.”“To ita Rukayyar fa....” Kan ya rufe baki ya hango tata taho inda muke. Ta karaso.“Kin dagan hankali ina ta nemanki ashe kina wajen Kawu kamar zai gudu.Abba ya ce, Kin ganta tana rigima har da kuka wai sai ta tafi gida.‘Uhum Kawu na dago ta fa bara mu je gidan kawai. Ya zaro key din motarsa ya miko mana.Na ce, ‘Abba wajen Ummata za mu.Muma yanzu za mu taho.Muna fita daga gate din gidan muka hangi Yusuf (yayan Imran) ya daga mana hannu muka tsaya na juyo ina kallon Momy kan ya karaso na ce, ‘Me ye na tsayawa dan ya daga mana hannu?' Ta juyo tana harara ta sannan ta ce, “Saboda ya cancanci na tsaya masa ne. Kan na yi magana ya karaso fuskarsa dauke da murmushi sai na ga suna matukar kama da Imran.Ya na ga za ku tafi ba za ku tsaya mu tafi tare ba?” Ya karasa magana yana kallon Momy.Ta ce, “Amaryarku sannan ‘yar shagwabar Abba ce ta ce sai mu je ta ga Umma.Ya dago yana kallona.‘Kanwata ba za ki kira angon naki ya kai ki ba, kin san yayanki cikin damuwa. Ina fatan za ki tausaya masa Ya juyo wajen Momy.ina son mu yi magana ga shi kun fito, in babu damuwa ina bukatar number wayarki. Bayan ya karbi number ta ya zagayo wajen da nake ya yi kasa da muryarsa ya ce, “Kanwata ina fatan za ki shigar da ni wajen Antyn taki a hada mu a sha biki.” Yana fadar haka ya juya cikin gida. Na juyo wajen Momy ina murmushi na ce, ‘Ina fatan ya samu karbuwa.Kai tsaye ta ce, “In har Imran ya samu karbuwa a wajenki to nima Yusuf ya karbu.Nan da nan na hade fuska har muka karasa ban Kara yi wa Momy magana ba. Tana yin paking na fito, ina shiga muka ci karo da Hassan na yi saurin surarsa ina dariya.“My Boy ina Umma da Hussaini? Kai masa wayo kana gudu ka bar shi yana fama da rarrafe ko?” Ya wangale baki yana dariya. Na karasa ciki yana hannuna. Umma tana jin sallamata ta dago da saurinta muna hada ido ta mayar da kanta kasa na karasa gabanta na rusuna na ce, Umma mun yini lafiya Ta ce, ‘Lafiya kalau. Ina ki ka baro su baban?” Kan na yi magana Momy ta shigo. Umma ta kara, tambayarta ina su baban? Momy na dariya tace su baba suna can gidan cikin farin ciki yanzu ma zasu taho nace umma yunwa nakeji ta mike bara na kawo muku abinci tana fita momy ta dawo kusa dani fuskata a hada tace: wallahi safiyya kije tsoron Allah me imran ya miki kike masa wannan muguwar kiyayyar ina guje miki ranar da imran zai rama abinda kike masa kin san a yanzu ko zaki mutu ba za a raba aurenku da Imran ba. Ina baki shawarar ki janye wannan kiyayyar da ki ke wa Imran ta baki don na san zuciyarki ba haka ba ne zan iya bada shaidar kina mutukar kaunar Imran ina fatan za ki taimaki kanki ku zauna lafiya da mijinki tunda yanzu magana tarewa za a yi mu....Kan ta karasa na katse ta da cewa, In ke ce Abbana ko Ummata sai kisa na zauna da shi.” Ina fadar haka na sa mata kuka. Ta dago tana harara.‘Dan kin ga in kin yi kuka ina lallaba ki to yarinya ki yi kukan jini, wallahi ba zan lallaba ki ba, kuma insha Allahu sai Allah ya zuba miki kaunar Imran a zuciyarki, kina ab....Shigowar Umma ce ta hana ta karasawa ina mike ina kuka na yi cikin dakin, Umma ta bi ni da kallo cikin mamaki.Momy ta ce, “Allah Umma, Safiyya ba ta san gaskiya duk wanda ya ga Imran sai ya tausaya masa, ‘yan uwanshi sai lallaba ta suke amma ta ki kula kowa karshe ma Kawu ya fito zai sallah ta biyo shi tasa masa kuka sai mun tafi gida shine ma fa yanzu muka taho, kuma Umma an gano baban Imran din shi ma dan baba ne, ita ta haife shi tun yana yaro ya bata. Kin ga Imran ya zama yayanta ga zum...Kan ta karasa suka juyo hayaniyar su Baba, yanzu ma gaba dayansu suka taho. Abbana, Alhaji, Nasir, Alhaji Salisu, Dahiru, Yusif, Doctor Khadija, Imran, Hajiya Amina, Khadija, Malam Mado Baba ga kuma Malam Khalil.Umma ta bi su da kallo cikin mamaki har suka gama shigowa. Umma ta bi kowa da gaisuwa, Alhaji ya kalli Malam Mado ya ce, “Baffa wannan ce kanwar tawa.” “Ga ta nan kanwarkan kamarku daya babu abin da yarabaku.Doctor Khadija ta ce, Tun farkon zuwanta nake gayama tasunakama da ‘ya’yana.Malam Khalil yace, “Ina matar tawa ne ina ta raba ido ta fito mu yi sallama?”Momy ta ce, “Malam tana cikin daki kanta ne ke ciwo ina tunanin barci ta yi.Yace, “Allah yasawake, ga wannan kiba ta tayi shirin tare wa bazan kuma zuwa ba sai ranar da za a kai min ita.” Yana fadar haka muka sa dariya.Ya jima yana nasiha mai ratsajiki tare da wa’azi, sannan ya mike bayan yayi wa kowa sallama Dahir ya mike yazo gaban Baba yana murmuishi, yace, Kaka ban gaji da ganin ki ba barana kaiMalam filin jirgi.” Bayan fitarsu Umma ta mike ta yi cikin daki, hakaAbbana tare da Alhaji Nasir sukafita, sannan Doctor Khadijah ta tafigida, domin girkin tarar maigida da ‘yarta Aysha wadda take karatu a ABU. Ya rage daga Malam sai Abban Imran da Hajiya Amina, sai Malam Yusif, Imran, Khadijah sai kuma Momy.Abban Imran yace, Baffa sai mu yi shirye-shiryen zuwa can Adamawar.Yusif yace, “Don Allah Dady mu tafi gobe, daman ina san mu dinga zuwa wani garin.” Malam yace, ‘Dukkanmu zamu hadu mu tafi, in munzo mu hudu sai da shanunmu za mu koma mun zama da yawa.Hajiya Amina ta ce, Kan mu tafi sai a yiwa Aysha waya ta tafi, don dukkanmu za mu tafi.Dahir ya yi sallama ya shigo yana kallon inda Imran yake zaune kusa da Baba ya zauna sannan yace, “kai me ye haka dukka bi katakura kanka, baka san nan gidan ka bane kana tare da matan ka biyu tsohuwa da sabuwa Baba ta ce, ‘Ai kaine mijina ni bazan iya kishi da takwara ta ba gara damatarka.Imran yadan yi murmushi yana kallon fuskar Momynsa, sannan yace brother bana jindadin dadin jikina ga kuma fushin da su Dady suke da ni, don Allah Malam ka sa baki suyi hakuri su daina fushi da ni, kalli Momy sai harara ta take ya zanyi da raina duka biyu nikam bazan bi su mu koma Lagos ba a wajen ka zan zauna har sai kun ban matata Safiyya.Malam yace, “Kama daina maganar Safiyya, tuni Safiyya ta zama taka lokaci kawai za a tsayar mu yibiki. Abbanka in har yana farin cikin ganin mahaifiyarsa to ya daina fushi da kai, ita Hajiyar in tana taya shi farin ciki to za ta daina fushi da kai.Barrister Amina ta yi murmushi sannan ta ce,Wallahi Malam ina matukar farin ciki da samunku a matsayin iyayen mijina gaskiya, a da na yi niyyar daina fushi da I mran don duk cikinsu shi ne dan lelena, bayyan nan safiyya matsayin yata yasa bazan daina fushi da shi bahar sai Safiyya ta yafe masa, kuma in har ta ce ba ta san zama da shi to ya sake ta shi ne kawai zai sa na daina fushi da shi.Dady yace, “Kin yi daidai Amina nikaina bazan yiwa yata auren dole ba, in ba ta son sa dole yasau wake mata. To gayan wanda take so na aura mata? Ya dago idonsa cike da rowan hawaye yana kallon Dadynsa muryarsa narawa yace, “Don Allah Dady karkayi min haka wallahi Safiyya tana sona kunyar ta fada take kuma kutambayi kawarta.Baba ta ce, ‘Ai kaine mijina ni bazan iya kishi da takwarata ba gara da matarka. 🅰bbagana hausa novels@ facebook. [12/24/2016, 9:44 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Sai karfe takwas muka fito za mu tafi har Khadijah, Momy da Dadyn Imran za su kwana gidan Baba, Doctor Dahir ya tafi Nassarawa. Mu kuma Yusif da Imran za su kai mu a motar Dadynsu.Tun da muka shiga Momy da Khadijah suke hira, Imran kuma da Yusuf ni daya ce na yi shiru. Yusif sai tambayata yake lafiya? Muna shiga gate din gidan kan motar ta gama parking har na fice, Khadijah ma ta biyo bayana.Imran ya juyo yana kallon Momy fuskarsa cike da damuwa ya ce, “Rukayya anya ko za mu sami masauki a gidan nan, duba ki ga irin kallon da Safiyya take min.Ta dan yi murmushi, sannan ta ce,Kar ka damu Imran za mu shigo ciki.Ni kam ina shiga muka yi dakin Baba Binta suna tare da Abbana, na yi sallama muka shiga. Baba ta ce, “Yar halak yanzu muke maganarki an kusa shirin bikiniku.” Khadijah ta karasa gaban Abba suka gaisa. Na ce Baba kanwata ce fa.Ta dan yi murmushi, Allah Sarki Muntari ya ban fari ciki ai da an gan ku an ga ‘yan uwana. Momy ta shigo tana harara, baba ta ce, Ke kuma lafiyarki kin shigo kina faman zare ido.“Kin ga ni ba zan miki magana ke goyuwa ki ke da bayanta.” Ta juya wajen kawu ta ce, “Dan Allah Kawu ka fadi gaskiya.” Shi dai murmushi yake ya dukar da kai.Kawu tare muke da su Imran su biyo mu za su kwana tunda muka shigo take harare-harare, yanzu muna shigowa gate kan a karasa parking ta fice inda tsautsayi ta fito za ta iya faduwa ta ji ciwo fa Abba ya hada fuska yana kailona wannan gangancin kina harara, to wa ye ki ke harara duk motar yan uwanki ne.Baba ta karashe da cewa, “Bare kuma har da mijinki maza Rakiya ku shigo da su.” Na dago da sauri ina kalion Baba.Abba ya ce, “Baba rabu da Rukayya ta huta ita ta jc ta shigo da su.” Na yi saurin dagowa ina kalion Abba nace, “Abba ni zan shigo da su.Ya Kara hade fuska, “To da da wa nake maza ki shigo da su.” Na mike na fita.Suna tsaye a jikin mota na karasa ina kalonn Yusuf, kwata-kwata na ki kalion inda Imran yake. amma ina ji a jikina Imran yana kallona. Na daure na saki fuskata na ce. Yusuf ku shigo.Kanwata muna shirin juyawa ne." Na dago kaina ina kallonsa na ce, Saboda me za kujuya? Ya ban amsa da saboda bamu samu fuska a gurin kanwarmu ba, tunda muka tawo taki kula kowa, kin ga gara mu juya. Na dan yi murmushi.Kaina ke ciwo Yusuf, amma yanzu ya warke zan maka hira har sai ka kore ni.Cewa za ki yi za ki mana hira sai mun kore ki tunda ga Imran ko? Na dan juyo na kalle shi cikin sa’a muka yi ido biyu na ko zabga masa harara, sannan na juyo wajen Yusif ina girgiza kai Ban kula da mutum a kusa da kai ba Ina fadar haka na juya tare da cewa Abba na jira Yusuf ne ya bi bayana shi kam Imran yayi shiru yana tsaye saboda bakin cikin da ya cika masa zuciya. Wanan wacce irin kiyayya Safiyya take min haka? Ya ya zan yi da son wadda ba ta sona? Ya Allah ka kawo min d'auki, wannan masifar bar ina...“Imran! Imran!! Imran!!!” Ya ji muryar Abban Safiyya yana kiran sunansa. Ya dago kansa da sauri kamar wanda ya tashi daga barci ya yi saurin tsugunnawa yana gaishe shi. Abba ya dafa kafadarsa cikin tausayawa ya ce, “Haba Imran kai da ka ke namiji bai kamata a ce ‘ya mace tana saka kana zubar da hawaye ba, kar ka kuskura Safiyya ta ga hawaye a fuskarka za ta raina ka. Bara na gaya maka daga yau ka rabu da Safiyya kwata-kwata ka fita a hanyar ta.Ya dago da sauri bakin shi na rawa ya ce, “Please Abba kar ka raba ni da Safiyya in ka raba mu ban san ya rayuwata za ta kasance ba, don....Hannunshi ya kama muna falo suka wuce tare da Abba, har dakinsa suka shiga. Kan Imran na kasa Abba ya ce, Imran bana nufin in raba ka da Safiyya, kuma na fi kowa murna da ka zama mijinta. Alhaji Nasiru ya gayan kwanan nan ka dawo daga karatu, shin ka samu aiki ne? Ya ce, “Na samu Abba tun washe garin da na dawo a U.B.A Bank, kuma kwanan nan na karasa ginin gidana a Bietoria Island To masha Allahu abin da nake so na ji daga bakinka kenan. Don haka in har ka s hirya rana ita yau safiyya zata tare a gidanka. Don farin ciki bai san lokaein da ya mike tsaye ba, ya yi saurin zubewa gaban Abba yana godiya Me ye abin godiya Imran? Ina fatan za ka rike Safiyya da amana ko babu aure tsakaninku Safiyya kanwarka ce. Ina kuma ba ka hakuri kan abin da Safiyya ta ma a baya kar ka ce za ka rike shi a ranka.‘Abba ban taba rike abin da ya faru tsakaninmu da Safiyya a raina ba, kuma...." Ya dan yi shiru.Abba ya ce, “Ka yi magana mana ko a kara lokaci ka yi shirin ka? Da sauri ya ce, “A’a Abba na gama shirina gobe ma zan tafi Lagos din, daman maganar su Dady nake tsoro.” Abba ya dan yi murmushi, “Kar ka damu gobe zan je na samu Dadyn naka za mu yi maganar, kuma duk wani shiri da za a yi za a yi shi cikin ‘yan kwanakin a yi komai kowa ya huta, kar ka damu kanka fatana ka rikc Safiyya da amana kanwarka ce ni kuma ita daya Allah ya ban ina fatan za ka zauna da ita tsakanin da Allah.‘Wallahi Abba na maka alkawarin zan rike ta tsakani da Allah, ina kaunar Safiyya tsakani da Allah ba zan taba cutar ta ba. Zan kuma yi hakuri da duk abin da za ta yi min har zuwa lokacin da za ta kaunace ni. Imran safiyy tana kaunarka kuma nan gaba za ka ga haka.”Ya mike “Na gode Abba bara na je falon mu gaisa da Baba.” Ya fito fuskarshi cike da annashuwa. Khadijah ta ce, “Brother lafiya ka ke jin dadi kai daya? Ya juyo da sauri dan bai san ya shigo falon ba suka hada ido da Khadijah “Uhm! Sister kawai zuciyata ce cikin farin ciki shi yasa ki ka ganni haka, raka ni dakin Baba mu gaisa.” Kwata-kwata bai kalli inda Safiyya take ba, abin da ya bawa Yusuf mamaki, haka Momy. Khadijah ta mi ke suka shiga cikin dakin.Khadijah ta ce, ‘Baba ga imran din ya zo gaishe ki tare kuma da ban hakurin abin da ya faru a baya, bar ma kuma da kokon bararsa.” Ya tsugunna a gabanta suka gaisa.“Komai ya wuce a wajenmu tunda abu ya faru a rashin sani, mu kam mun riga mu baka.Ya kara sunkuyar da kansa kasa yana godiya, hannunsa ya zura cikin aljihunsa ya zaro rafar dari biyu ya dire mata. Sannan suka fito falon.“Anty Momy yunwa nake ji.“Tun dazu abinci yake jiran ka a dinning table, kai daya mukejira.Na mike da sauri na je dinning table din na na debo nawa na dawo na zauna. Yusuf ya juyo.Kanwata ya kika debo naki ke daya? Na dan tabe baki na ce, bana sakewa a dinning gara nan.Momy ta ce. “Ku tashi mu je ku rabu da ita.Washe gari har wajen yamma ban ga Imran ba, sai Yusuf da Khadijah. Muna falo su Momy suna hirarsu. Wayar Yusuf ta yi kara ya zaro da sauri ya daga.Hello Brother ka sauka?" Ya dan jima suna wayar sannan ya ajiye. Khadijah ta ce, “Ya sauka?‘Tun dazu ma ya sauka wayar shi ce ba caji.Jibi za ta taho kun san abin ya zo a korarran lokaci? Momy ta ce, “Nima jiran Sadiya nake mu yi shirin da za mu yi kar lokaci ya kure, sai ta waya nake gayawa kawayenmu.Karfe tara har na kwanta, Abba ya yi kirana na shiga dakin tare da yin sallama. Bayan na zauna Abba ya ce, “Safiyya kin yarda da ni a matsayin mahafinki?” Na daga masa kai.“Yauwa Safiyya kuma kin san duk wani uba nagari ba zai kai ‘yarsa inda za ta wulakanta ba. Yana burin samar mata miji nagari, wanda ya yardada nagartarsa, ya kuma yarda da Addininsa. Kuma kina sane da cewa duk; abin da Allah ya zaba maka zai zama alkhairi a gare ka.” Na kara daga masa kai.‘To Safiyya Allah ya zaba miki Imran a matsayin mijinki na aure, ina fatan za ki karbi zabin Ubangiji da kuma abin da nake so.Na dago a razane, muryaryata a sarke na ce, “Abba kana nufin ba za ka raba auranmu da Imran ba? Cikin karfin zuciya ya ce, “Ba zan ja da abin da Ubangiji ya kaddara ba amadadin hakan ma ranar Lahadi za a kai ki gidansa kin ga sai ki yi bautar kasarki a can. Ina fatan ba za ki ban kunya ba a matsayina na mahaifinki?Na dago fuskata cike da hawaye na ce, ‘Abba ba zan taba ba ka kunya ba, zan maka biyayya, zan zauna da Imran ba don ina son shi ba, sai don na faranta maka.Ina fadar haka na sunkuyar da kaina na fara kuka.Kar ki yi kuka Safiyya, na fasa hada ku tunda ba kya so, shi kenan kin zabi mutuncina ya zube kuma kin za6i na rasa Ummanki?Na dago kaina. “Ka yi hakuri Abba zan yi maka biyayya bana so ka rasa Ummata na maka alkawarin zama da Imran ka yi hakuri in na bata maka rai. Ina san kasan cewar ka tare da Ummata zan yi duk abin da ka ke so don na faranta maka.” Na yi shiru ina ajiyar zuciya Shi kenan Safiyya Allah ya yi miki albarka, sai ki je ki sami Rukayya ku yi duk shirin da za ku yi. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/25/2016, 4:32 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Ya zaro kudi cikin lokar gadonsa.“Ga dubu dari biyu ki rike kin ji ko za ki yi wata bukatar in ma sun muku kadan sai ku gayan.Nasa hannu na karba. Har wajen karfe goma ina dakin Abba yana min nasiha mai ratsa jiki, sannan na flto babu kowa a falon don haka kai tsaye na yi cikin dakina.Tuni Khadijah ta yi barci sai Momy da take waya. Ina shiga ta dago tana kallona na karasa cikin dakin, na samu gefe na zauna, Ina zama na ci gaba da kukana, Momy ta katse wayar ta matso kusa da ni ta yi kasa da muryarta kamar mai rada ta ce.“Don Allah Safiyya ki nutsu ni wallahi ban taba ganin mutum irin ki ba, haka kawai don masifa ki tsani mutum ban ga laifin da ya yi miki ba, duk abin da za ki yi yanzu Imran ya zama dan uwanki da Ummanki da mahaifinsa uwarsu daya ubansu daya. Yanzu don Allah ba za ki ji kunya Khadijah ta farka ta ga kina kuka akan ba kya son dan uwanta ba? Haba Safiyya ya kamata Imran ya ci darajar Ummanki don Allah ki daina nuna masa kiyayya haka. Kalli irin kaunar da iyayensa suke miki, kalle irin soyayyar da kanwarsa take miki, ta bar iyayenta ta taho wajenki amma duk ba ki ga wannan ba. Ni ban ga mummunan laifin da Imran ya yi miki ba da har ki ka daukar masa wannan matakin ba, ya kamata ki kai kukanki wajen Ubangiji ya yi miki zabi mafi alkhairi ba ki zauna kina kuka ba.Na dago fuskata idanuwana duk sun kumbura na ce, “Ni Momy na rasa ya zan sarrafa zuciyata taso Imran in....Ta katse ni da cewa, Baby kina kaunar Imran kuma nan gaba za ki yarda da abin da na gaya miki. Na bude baki zan yi magana ta katse ni, ‘Mu bar maganar nan yanzu shirin biki za mu yi don maganar da muke da Yusuf kenan ki ka shigo.Na dago ina harararta.“Ni babu wani shiri da zan yi don ta nima kada a yi komai ga kudi in ji Abba. Ina mika mata na haye gado na kwanta. Tunda na yi sallar Asuba na koma na kwanta har wajen karfe tara ina kwance, hayaniyar Salim ce ta tashe ni na dago ina kallonsa.‘ Amarya kin sha kamshi.Na dan harare shi na ce, Ka zo ka katse min barci za mu hau court, ni ba amarya ba ce, Sadiya ce amarya.Ya sa dariya Da kin ki da kin so dole mu kira ki da amarya. Ni da kin taimaka kin yi wa Kawu magana a hade bikin da nawa da kin ga gama min komai.Na ce, “Ka ga don Allah ni ka rabu da ni ban tashi ba, ka je tsohuwar matarka tana kiran ka.Ya juyo yana dariya har ya kai bakin kofa ya juyo. Ki fito muyi shirye-shiryen party.” Na daga masa kai.Sai karfe sha biyu na farka, gidan shiru. Na yi wanka na fito na nufi dinning table na yi break fast, sannan na shiga dakin Baba. Yanzu nake shirin shiga na ga lafiya ki ke barci haka.Na dan yi murmushi, ‘Lafiya kalau Baba. Na tsugunna muka gaisa na tambaye ta Abba ya fita? ‘Ai tun karfe takwas Muntari ya fita ya je can gidanku, su kuma su Rukayya sun fita da yayan Imran wai za a kama wajen da za ku yi party.” Na mike “Baba bara na je wajen Ummnata.“To ki gaishe su.Na koma daki na dauko key din motata na fito. Kwata-kwata bana jin dadin zuciyata na daure na fita . Ina daidai Gadon Kaya an tsayar da mu na dan sauke glass din motar na yi kiran mai saida dabino na zaro dari biyu na mika masa.Ina zuwa kofar gidanmu na tarar da motar Abbana na karasa na yi parking cikin gidan Malam Mado na yi babu kowa a gidan sai auta. Na tambaye ta ina Baba Magajiya ta ce ta shiga gidanmu, na shige cikin dakinta na yi kwanciyata. Na jima a kwance auta ta shigo.Yaya Safiyya ana kiranki.Na ce, Wa ye yake kirana? Abbanki ne. Na mike da sauri na fito. Yana kofar gidan na karasa gabansa.Abba gani.Ya dago yana kallona? Me ya hana ki shiga gidan bayan tun dazu ke nake jira? ‘Abba shiga na yi mu gaisa.” Okey na je mun yi magana da Alhaji Salisu kan maganar tarewarki, kuma na san in kin shiga za ya tambaye ki ra’ayinki na ce kin amince, kar ki shiga ya tambaye ki ki yi magana akasin tawa.Na ce, Abba zan gaya masa kamar yadda ka yi min ummurni kuma rashin shigowata in ta bata maka rai ka yi hakuri. Na mike na shiga cikin gidan tare da sallama muka ci karo da Hussaini yana kokarin fitowa, na dauke shi ina dariya. ‘Boy yana ga ka kara girma mai Umma take ba ka? Na ji muryar Baba ta ce, “Yana girma ne don ya bi ki ku tafi Lagos zaman aure Na juyo da sauri ina kallonta. Na dan yi murmushi na ce, “Ni da ke zan tafi ba da Hussaini ba.“Ni Allah yasa in na je ma abude min kofa.” Na dan yi murmushi na tsugunna muka gaisa. Na shiga falon tare da sallama. Dady Imran ne shi kadai a zaune sai Hassan da yake kan cinyarsa na karasa gabansa na tsugunna na ce, Daddy an tashi lafiya? Lafiya kalau Safiyya, ya mutan gidan? Na ce, “Duk suna lafiya suna ma gaishe ku.Na dan yi shiru ina wasa da hannun Hussaini.“Yanzu muka gama maganarku da Abban nake ya yi min maganar tarewarki to shi ne na ce sai na ji ra’ayinki don ba zan yarda a kai ki ba in har baki amince ba.” Na kara sunkuyar da kaina.‘Ki yi min magana kin amince?” Na daga masa kai. Ya dan yi murmushi, Allah ya yi miki albarka.” Ya mike.Bara na je mota na dawo ki shi ga ku gaisa da su. Yana fadar haka ya fita.Na mike na shiga cikin dakin Momyn Imran ta juyo tana kallona fuskata cike da murmushi. Na karasa gabanta na tsugunna muka gaisa na juya wajen Umma na gaishe ta kanta na kasa ta amsa. Dady ya kira Momyn Imran ta fita na karasa gaban Umma cikin taushin murya na ce, “Don Allah Umma ki taimaka ki koma gidan Abbana, ki yi hakuri da abin da ya faru a baya. Abbana yana son ki yana kaunar ki dawo ku ci gaba da zama, kuma na san ke ma kina sonsa kin ga na amince zan zauna da Imran tad ago da sauri tana kallona tace, Da gaske kike? 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/25/2016, 5:22 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 9⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Na daga mata kai.“Umma na amince zan zauna da danki, don Allah ke ma ki amince ki koma wajen Abbana kan....Kan na karasa Momyn Imran ta shigo hannunta dauke da hotona ta miko mini.“Ga shi in ji Daddynku ki zabi wadanda suka yi miki gobe zai tafi can Lagos din kin ga sai a siya a can.Na ce, ‘Momy ki zabar min da kanki na san za ki yi min zabi mai kyau.Ta dan yi dariya ta ce, “Ni daman na riga na zabar miki.” Ta mikon wasu hotona guda biyu na karba kaina yana kasa na karba. Iya kyau saitin kayan gadon sun yi na mika mata hotunan.Na ce, “Momy sun yi kyau.” Ni na san za ki yaba, ina fatan Allah ya zaunar da ku lafiya ya tsare ku daga shairin makiya.” Baba ta amsa da amin.Barrister Amina ta mike “Bara na je Nassarwa. Bayan fitarta ya rage da gam sai Umma, Baba da Dady. Abbana ya shigo gidan tare da sallama, Dady ya leko suka shigo tare na mike na koma daki ya rage daga Baba sai Abbana da Daddy. Abba ya ce.‘Yanzu muka yi waya da Imran yake tambayata na gaya muku kun amince.Dady ya ce, ‘Amincewar ‘yata ita ce amincewarmu na tambayi ‘yata kuma ta amince gobe ma za mu tafi gyara dakin ‘yata. Ya mikowa Abba hotiman da Momy ta zabar min kayan daki.“Ga kayan da ‘yata ta zaba ina fatan kai ma zabinta ya yi maka. Abba ya dan yi murmushin jin dadi. ‘Sun yi kyau. Allah ya taimaka har zan yi waya Nasiriyya ka gan ma huta da jigilar kava kan ku tafi na kawo kudin sai a siya a can.Abba ya dago fuskarsa ta nuna alamun rashin jin dadin maganar da Abba ya yi. “Yanzu don zan wa Safiyya siyayya shi ne za kace za ka ban kudi na siya, ina tunanin Safiyya’ ‘yata ce tunda yar kanwata ce zan iya yi mata komai ba tare da na bukaci tallafin kowa ba.Abba ya dan girgiza kai ‘ban fadi haka da wata manufa ba wallahi Safiyya 'yarka ce halak-malak, ni daman kara zan yi da kuma gudunmawata amma tunda ba ka bukata na yi wa dana gudunmawa. Dady ya ce, “Gara dai ka yi wa dannaka gudunmawa ka kuma hada da jan kunnensa ya kular min da ‘yata sosai don ba zan laminci ya dinga cutarta ba, ni kam zan yi shaidar ‘yata na san ba ta da matsala.‘Bara na shigarwa mijina. zan ba da shaidarsa wajen hakuri sabanin kishiyar tawa da take sarkin rashin hakuri.Abba ya ce, “Alhaji Salisu nima ina da muhimmiyar magana da za mu yi. amma sai bayan mun gama da su Imran amma kafin lokacin na san barristcr Amina za ta gaya maku ina fatan za ka shige min gaba. Dady ya dan yi murmushi ya ce, “Tu jiya Hajiya take gayan kuma mun yi magana da Baba har ma da Malam duk sun amince dari-bisa-dari. Kuma mun yi magana da Alhaji Nasir shi kansa ya gayan cewar ya hakura da Rukayya, ya bar maka in har ta amince za ta koma gidanka. Don haka yanzu aikinka dava ku sasanta kanku da ita, amma ina fatan za mu bar wannan maganar sai bayan mun gama bikin ‘yata.Washe gari su Momy, Dady da YayarDahir-suka koma Lagos don shirin biki, kuma ranar Aysha ta zo hutu daga Zariya. Tana zuwa gidan Doctor Khadijah ta yi wa Yusif waya suka fita dauko ta,suna fita Sadiya ta zo. daki ta shigo na dago ina kallonta. Ta dan harare ni ta ce Malama ki yi waya tun dazu nake kiran wayar Rukayya ba a daga ba sai Abban Yusrah ya kira yake tambaya s kuna gida.Na ce, “Wa ye Abban Yusrah? Tana murmushi ta ce, “Yaya Salim. ‘Uhm! Allah ya sauwake muku.Ta karaso kusa da ni ta ce, “Amarya kin sha kamshi, ya na ga sai wani kyalli ki ke, kina kiba?“Kina zagina kawai inda auren soyayya zan yi to in kin fadi haka ba zan karyata ki ba, amma ana shirin auran mutumin da na tsana a rayuwata ina batun kiba da kyau baya ga tarin rama da kuma tashin hankali.” “Kin ga ni ba wanann maganar ce a gabana ba, kin san ba kya sonsa me ye ki ka amince za ki zauna da shi? Wallahi Safiyya ki ji tsoron Allah kar ki cutar da imran. Ina baki shawara ki gayawa Abba na tabbata ba zai miki aurcn dole ba, kar a yi abin da zumunci zai zo ya yi rauni, maimakon ya kara karfi tun kan abu ya yi nis..Da sauri na katsc ta da cewa, ‘Sadiyya ina son Abbana bana son ya rasa Ummata, in har ban amince na zauna da Imran ba, to na tabbata Umma ba za ta ta6a yarda ta dawo wajen Abbana ba. Ni kaina na rasa laifin da Imran ya yi min nake masa kiyayya haka.Haba Safiyya, Imran dan uwankine ya zama yaya a gare ki, ya kamata ko ba kya sonsa ki bashi kyakkyawar kulawa. Imran na kaunarki tsaka ni daAllah ya kamata ki cirewa ranki kiyayyarsa, ki maida ta kaunarsa. Ke in ma ba za ki saka kaunarsa ba to kisa tausayinsa ki bar ganin kulawar da iyayensa suke baki kiga kamar don kin nuna ba kya kaunar dansu ba za su damuba.Na dago kaina ina kallonta. Shi kenan Sadiyya zan yi yadda ki ke so. Na fadi haka ne don mu bar hirar ni kam ta gudire ni banga shigwar dadin bakin da zai sa ni na kaunaci imran ba a zuciyata na kudiri ba zanyi sati biyu a gidansa ba tare da bakin cikin abinda nake masa yasa ya sake niba, muna dakin momy suka dawo aysha ta shigo da gudunta tana kiran sunana na dago ina murmushi aysha sannu da zuwa ta fado jikina tana dariya khadija tace sai na gayawa yaya imran nace aysha zata balla cinyar anty safiyya Na mike na kama hannun aysha zo muje ku gaisa da abba naji shigowarsa muna fitowa muka ci karo da hajiya hassana (mahifiyar rukayya) na karasa wajenta da sauri nayi mata sannu da zuwa ai bazan amsa ba fushi nake dake tunda zuwa daya ban kara ganinki ba ina murmushi nace ayi min afuwa hajiya yau n ace zanzo ta danyi dariya ko dai angon ne ya hana zuwa? Na tsugunna muka gaisa aysha ma suka gaisa sannan ta shiga dakin baba mu kuma mukayi cikin dakin abbana. 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).