shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

WACE CE********ITA? 88 & 89

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.??

88


*******by*********

muhd-Abba~Gana


Okay.! zauna muyi kallo ya zauna suna kallo har
guraren 1 na dare iffaat idonta gyam akan TV ko
motsi yanayi yana satar kallonta amma batada
niyyar tashi, ya fara gyangyadi, ya karbi remote
ya kashe dole sai sunje sun kwanta, iffaat kuwa
ta fuske tace yaje xatazo yaga dai batada niyyar
tashi sai ya wuce yace yana jirinta tace mai OK,
iffaat dai anan ta gyangyade sai bacci da asuba
farhaan ne yaxo ya tayar da ita bacci yana Dan
shashafata har ta bude ido tamai murmushi ta
tashi taje tayi alwula tayi sallah ta dawo Palo
zata kwanta farhaan yasha gabanta yace idan
dai dannine ki kwantar da hankalin ba abinda
xan miki murmushi kawai tayi ta rabashi ta
wuce, taje taci gaba da baccin ta qarfe 9 ta
tashi ta hada mai breakfast ta shirya a D table
ta dawo tayi kwanciyarta sai goma ta tashi da
yake ba lecture ta Dan dima abincin a taje
taganshi yana sharar bacci wanka ta shiga ta
fito ta dandasa kwalliya ta saka wasu arnan
kaya cikin kayan da tasiyo ita kanta tasan tayi
ta fesa turare taxo kusa dashi ta shafa
kumatunsa a hankali ya bude ido ya kalleta
tamai murmushi ya janyo ta jikinsa sosai yayi
kissing dinta a kumatu, tadan goce ka tashi
muje kayi wanka, yayi miqa hadi da salatin
annabi ya miqe yaje wanka bayan ya fito tazo
tayashi goge jiki da shafa mai, daxai chanxa
kaya sai ta miqe xata fita ya janyo ta ina
xakije,? ta Sosa kai xan dauko abune a Palo yayi
murmushi aranshi yace mata da mijinta amma
tana guduwa. Ya saketa bata dawo ba saida ta
tabbatar da ya saka kayan sannan ta shigo.....
WACE CE ITA..?? 89


********by*********

muhd-Abba~Gana


09039016969

Ta kalleshi ta riqe kunkumi iyeee kaganka
kuwa.!? Kayi kyau kamar sabon ango, ya kalleta
ya kanne ido yace ai angonne ko kinmanta har
yau baisha maiba,! Ta gane mi yake nufi sai ta
basar da zancen muje kayi breakfast kaje ka
gaida su Abba da umma, yace to my princess,
sun zauna ta kawo breakfast nan ma yasa
rigima har yanxu bai warwareba sai ta bashi a
baki, haka ta riq biye mai tana bashi yana chi
idan ya cijeta tace sai ta rama haka zata samu
wani guri shima ta chije shi har suka kammala,
ta rakashi har mota ta dawo ta tattara kayan
gudu gudu cox tanada lecture 12 gashi 11:30 ya
wuce ta qare ta wuce skull.
*******
Zaman iffaat da farhaan dai xan iya cewa lafiya
lau duk wani kula dashi tanayi ba abinda za'
nuna mata tun daga kwalliya har girki da tattalin
miji saidai har yau taqi bada hadin kai farhaan
yayi yayi amma taqi..
Ranar dai ya tirketa tana baccin rana a daki
yaxo ya dabai bayeta ya fara yan shafe shafensa
chan ta farka ta bude ido ta kalleshi tace miye
haka?? Yace mata sunnace haka, tace sunna
kuma? Yace eh bakisan annabi yace duk Wanda
ya aikata Wannan sunnatawaba daidai yake da
Wanda yayi jihadi ya kashe arna dububa. Ta
kalleshi ta kyalkyale da dariya har saida tayi
kwalla, sannan tace Yy farhaan watana hudu
gidannan watanka uku muna kwana daki daya
gado daya bargo daya bakasan da a kashe arna
ba sai yanxu farhaan kam ya fara nisa ba wani
jinta yakeba tuni tasa qarfi ta tureshi gefe ta
miqe zaune ta kalleshi rai a bace wallahi kada
ka qara kuskura kace zaka kusanceni! Ya kalleta
ido sun wani Kada haba iffaat mi yasa kike min
hakane? So kike na koma abin farko da nakeyi?
Wannan kuma ya rage naka ko yanxu waya sani
ko ana lallabawa dubunka ce bata cikaba na
kamaku, ko kuma anji tsoron cell shiyasa ake
kama kai amma dai badan iffaat ba kuma ba
Dan tsoron Allah ba.!.
Ta wuce Palo ya zauna saman gado yayi tsaki
wannan yarinya mayaudariyace wallahi, ta
koramin yan mata kuma ta hanani kanta kuma
gata kamar aljana duk abinda nakeyi tana gani,
yayi tsaki yadan kwanta akan gadon qafafunsa
suna qasa ya dafe kai miye abinyi??
Da gaskiyar ta Dan tsoron cell naqi Neman
matana amma yakamata na bari Dan Allah
badan kowaba. Yayi ajiyar numfashi...


muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive