DOMIN KEDA MIJINKI
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Babban abin da mai son jin dadin aure ya kamata
ya lura dashi shine:
Mace tagari, ita zata iya zamar masa zinariya,
duk lokacin da tayi datti in aka wanke sai
qyalqyalinta yafito sarari, amma aure don kyau
(wanda shi muke yi yanzu) kamar baqin qarfe ne
da aka shafa masa kumfar zinare, yana daukan
ido da ban sha'awa, da zarar kayi amfani dashi
Daya, Biyu qyalqyalin zai fita munin kuma ya
bayyana, daganan ba sauran sha'awa kuma,
galibi qyalqyal banza dinnan su maza suka fi so,
shiyasa mai haja yake tallata musu don samun
kasuwa.
Maganar gaskiya duk wani dan kasuwa riba yake
nema.
Mace tagari za a sameta da:
1)KAMEWA,daga duk wani abu da zai sosawa mai
gidanta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa
da sauransu.
2)GASKIYA.
Idan zatayi magana bata qarya, domin samun
riqe gidan gaba daya.
3)ZA'BIN MIJINTA A KAN ZABINTA.
Tana buqatar abu amma in bayaso zata barshi,
ko tayi don shi yanaso koda kuwa bataso.
4)AMINCEWA.
Duk abin da yakeso tayi ta amince, don yarda
dacewa bazai halakar da itaba, tana qaunarsa.
5)TAWALU'U, ta qanqar da kai gareshi koda kuwa
tanada ilimi, arziqi da shekaru sama da shi,
kamar dai Khadeejah (R.A) da Annabi (S.A.W).
6)NATSUWA, kar tariqa tuno abubuwan da suka
gabata, kuma tadena tsoron masu zuwa.
7)KUNYA, tariqa jin kunya, wannan ado ne gare
ta, masamman idan tana tareda mijinta a cikin
jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
8)KWANCIYAR HANKALI.
Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura
farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
9)GODIYA, duk abin da yazo dashi ta nuna masa
jin dadin zuwa dashi komai girmansa komai
qanqantarsa.
10)HAQURI, akan duk abin dazai bayyana daga
miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da
yawa).
11)TSAYUWA QYAM, a wajen bauta da qarfafa
mijin da'yayansu.
12)AMANA.
Tazama mai amana, karta yarda mai gidanta
yaga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, tariqa
gaya masa abin da za tayi domin maganin
shedan.
13)CIKA ALQAWARI.
Yana Daya daga adon mace da namiji.
14)TSORON ALLAH, a duk abinda zatayi.
15)DANNE ZUCIYA.
Yayin da aka baqanta mata rai kada tanuna
fishinta a gaban mijinta.
Wadannan abubuwa guda 15 su suke nuna mace
ko miji nagari, kada kariqa binciken qyalqyal
banza, kema ki daina kallon kudi kiduba
rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa
idan ba kwanciyar hankali baza kiji dadinsu ba.
Sai Mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
allah ya bmu ikon yiwa mazamu biyayya su kuma allah ya basu hquriN xama damu
ReplyDelete