WACE CE ITA..?? 38
Na ABBA~GANA
Tana bude ido taga Su umma sun zagayeta Yar
budurwar na zaune gefenta itada farahnax, sai
nan ta tuna da abinda kunnuwanta suka jiyo
mata, LAAA KINGA NA MANTA IFFO BANGAYA
MIKIBA, KINA QAUYE AKA YIWA YAYA FARHAAN
BAIKO DA SUHAILA..!!!! Hawaye ne suka wanke
mata fuska shaaaaar, idan bata mantaba
Wannan maganar itace qarshe maganar da taji
sai yanxu da ta farka ta ganta a asibiti, ta
motsa hannu taji yayi nauyi ta qurawa Suhaila
ido mi yasa taji tana Sonta aranta?? Amma sai
take ganin kamar ba sontane takeyiba tsanarta
takeyi,?? Tanajin Suhaila har cikin ranta amma
kuma tsanarta tayi yawa a zuciyanta. tana tsaka
da tunani umma ta dafataa ta mata sannu, ta
kalli umma tace hajiya miya faru?? Ya akayi
mukazo asibiti?
Umma ta bata amsa da kin samu sauqi dai ko?
suna haka sai ga nurse tazo ta dubata aka
tabbatarda yanxu ba abinda yake damunta, illaa
kawai ta rage tunani....
Ta tashi zaune anan farahnax ta bata labari
muna tadi dake nake gaya miki an yiwa Yaya
farhaan baiko da Suhaila sai kawai naga kin
danne kai kina juyawa kika miqe tsaye sai kuma
naga kin kika fadi sumammaiya, Suhaila ta katse
wayar mukayo kanki muka kira umma taxo aka
saka miki ruwa amma ko motsi daga qarshe sai
Abba yace a kawoki asibiti, farahnax tace miyake
damunki iffo?? Tunda kika dawo gida kika chanja
ko su sukace miki ki riqa yi mana haka? Wallahi
iffo banajin dadin ganin ki a haka, Dan zaman da
mukayi na Saba da tsokanarki da labaranki
Masu dadi, shiyasa ma na kawo Suhaila itama ki
bata labarai sai Kuma haka ta faru, please ki
saki jiki damu ke Yar uwarmuce kinji.!? Aranta
tace da nasan abinda yake damuna Dana fada
kodan samun natsuwar xuciyata..
Ta kallesu tayi murmushi ba komaifa, sai tayi
shiru hawaye suka gangaromata,umma ta matso
Ku bar min yarinta ta qarajin sauqi sannan Ku
fara mata jarida. Dukansu suka saka dariya har
iffaat din saida tadan murmusa.
Saida ta kwana daya da yini sannan aka
sallamesu.
**
sun koma gida umma da farahnax suka sa iffaat
gaba sai ta fadi abinda yake damunta. Amma ta
murje ido tace bakomai koda yake ba komai din
tunda ita kanta batasan abinda yake damunta
ba, nifa tinda ta dawo Hutu banga dariyarta sau
ukuba, umma tace nimadai banganiba umma
ranar abbanku yace a kirata ta bashi labari
amma tazo ba wani labari,
Iffaat!! Na'am hajiya! Ki mana magana zama
damune kike gajiya dashi ko kuma wani yake
quntata miki ko kuma wani Abu yake faruwa a
qauye??
Kawai sai ta fashe da kuka, kuka mai tsuma
zuciya, ita kanta batasan sanadin kukanba,
sukayita rarrashi har tayi shiru, ki fada mana
minene idan mune mu gyara muryan ta a dishe
tace wallahi Baku bane hajiya, nima wallahi
bansan abinda yake damunaba haka kawai idan
ina zaune sainaji raina ya baci ko kuma na
riqajin inason wani Abu amma bansan ko miyeba
qunci yamin yawa hajiya ta qara fashewa da
wani kuka, sukayi chirko chirko, chan iffaat tace
mamarta takeso .....
WACE CE ITA? 38
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.