shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

QARIN**********JINI 1 &2

qarin-jini.jpg

QARIN JINI MARUBUCI MUHAMMAD ABBA GANA

QARIN JINI 1


Na abba~gana
Rufemin baki wawuyar yarinya wacce batasan
abunda takeyiba..!! Wllhy oumulkhair idan bakiyi
hankaliba sai na gayawa umma abinda kikeyi
wawuya kawai..!! ana miki magana kin sakowa
mutane ido kamar wata mujiya, ki tashi kibani
guri mashirmaciyar yarinya kawai..! Yaya naziah
wllhy...... Wallahi me!? rufemin baki duk abinda
zaki fada maimaitawane na dade kina gayamin
haka, tafada cikin fushi.. kawai niki bacemun da
gani.!
Sumui sumai tatashi tay dakinta...
Tabbas nima nasan abinda nakeyi yasabawa
hankali kuma bawanda zaiji ya saurareni har ya
bani uzuri idan har mai hankaline, toni ina zan
saka rayuwata.? Banida abokin da zangayawa
matsalata ya saurareni hatta meenah slow
qawata wacce muka tashi tare da ita
nagayamata matsalata, amma sai dariya kawai
tamun, sun maidani mahaukaciya wacce batasan
mitakeyiba, kumafa hakane banida maraba da
mahaukaciya, garama mahaukaciya tasan cewa
haukan takeyi nifa ata qaice dai mahaukaciya
tafini..
Cox ni abinda nakeyi bashida dalili ko kadan,
wasu zafafan hawaye suka gangaro akan
kyakyawar fuskata wacce rabon datasaka mata
powder tun kamin mota ta kadeta akaita asibiti,
naci gaba da kukana wanda yazamomin sabo
yanzu, har akay kiran magriba sannan natashi
na dora arwula nai sallah da addu'oena dana
sabayi bayan duk sallar magrib har akay esha
itama nayi sannan nazo nakwanta inyi barci da
wuri ko zanga DREAM GUY dina......!!

QARIN JINI.2


Na abba~gana
OUMULKHAIR yarinyace kyakyawa wacce basai
natsaya muku bayanintaba duk inda ya mace
takai a kyau oumulkhair takai inda Allah yayta
mara qiba amma akwai hips sosai a tare da ita,
in shot oumulkhair tanada kew na jiki dana fuska
tubarkallah masha Allah khair ta hadu wallah, da
kunsan wata qawar jabo ummu rubab, dasai
nacee muku oumulkhair tafita girman kai, daji
dakai, da daukar kai, da yanga da gayu, da
kwalliya, tabbas khair akwai girman kai sosai
wacce idan tanason abu saidai ta mutu bazata
iya cewa abatashiba ita dole kar mutunchinta ya
zube ko clss dinta ya ragu hmmmm. khair
kenan....
A gurin yayarta naziah tagirma wacce suke uwa
daya uba daya, nazia bayan aurenta da shekara
takwas Allah baibata haihuba sai ta dauko
qanwarta oumulkhair tadawo gurinta tun tanada
shekara goma har yanzu da takeda shekara 18
agurin yayarta take, iya gata mijin yayarta yaya
rabiu yana nunamata,baya bari amata fada ko
kadan wanda kullum ya naziah ke cewa shiya
batata, babanta kuwa dama kaman bayasonta
kullum fada yakemata dukda cewa itace autar
gidansu amma sai fada shiyasa banatason zuwa
gida dan gudun fadan su baba,
Taqare secondary school dinta shekara biyu da
suka wuce, yanzu tanason tay applying a AYNN
US.amma babanta yaqi barinta taje karatu
aqasar, wai ba addini a gasar tofa kaji iyayen
addini baban su oumulkhair.
Yanzu dai shekara ta biyu kenan tana zana exam
na shiga university a naija nata rubutawa ba dai
daiba dan kar taci kuma tana faduwa, amma
AYNN Kuwa wannan shekaran ma sun karbeta
amma tsohonta yaqi yarda da tatafi qasar
karatu tofa.....

muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive