shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 20 July 2015

WACE CE******ITA? 56

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 56
Na ABBA-GANA
Su ZZ an qare skull an bar su Iffaat yan mata
anata gwagwatawa Da students, dama ko ita
kadai tana abinda taga dama....
Cikin ikon Allah iffaat ana shirye shirye kammala
secndry skull any qara hankali amma fa har
yanxu tana jinyar soyayyar farhaan a zuciyarta,
ba Wanda yasani sai qawayenta ZZ....
****
Wata Ranar Suhaila taje sokoto bikin dangin
mamarta kusan sati biyu tayi bata gari, ana
gobe zata dawo tace wa iffaat taje ta gyara
mata gidanta tasan yayi qura ba kowa aciki
tunda tasan farhaan aikin banxa ne ba abinda
yake iya tabukawa kuma idan ta dawo ma ba
wani abin kirki zata iyaba gata da tsohon ciki
kwata 7 , dagyar iffaat ta aminta shima saida
aka hada da mama sannan ta aminta. mama
batasan sirrin ba iffaat tun lokacin da abin nan
ya faru bata qara zuwa Gidan Suhaila ba sai
wani zuwa da sukayi duba Suhaila itada mama,
sai kuma yau...
Waike Dan Allah idan bakiyimata wa zaki yiwa??
yarinyar tana qaunarki ta damu dake amma ke
kina Neman ki yanke zumunci mama dai haka
tayi fadanta dole tasa iffaat ta tafi Gidan..
Hmmmm Su farhaan ba'asan da zuwan iffaat
gidanba, kuma yasan sai gobe matar shi zata
dawo hankalinsa kwance shida karuwarsa...
iffaat tazo ta gyara ko ina na Gidan har ta
kammala Basu saniba suna chan ciki. haka
kawai taji tanason shiga dakin farhaan ta gyara
kuma batasan yana gidanba.
Takama hanyar dakinsa Ta buda qofar tajita
abude sai ta tsaya ta qara budewa Sanyin Ac da
qamshin turarensa ya daki hancinta ta lumshe
Ido ta dauke numfashi hadi da wani ajiyar zuciya
ta tura kai dakin tana bude ido sai taga mace
kwance tana sharar bacci daga ita sai wasu
tsinannun kayan bacci, numfashin tane ya tsaya
chak..!! tama rasa mi zata mata ta gane ta tsab
hafsa ce tsohuwar budurwar farhaan, ta tsaya
waige waige ta hango Yar yawo gefen fridge ta
Ciro ta zo zata fara zabga mata sai ta tuna duka
ana bacci bashida xafi sosai, ta bude fridge ta
samo ruwa ta juyesu a jug taje ta yaye bargon
da ta rufa ciki da qarfi, hafsa ta juya cikin
shagwaba tace dear kabarni zuwa anjima
mana.!! tace kinci ubanki keda dear. ta watsa
mata ruwan da qarfi a fuska, hafsa ta wani
zabura da qarfi tana miqewa zaune iffaat ta
kwashe banxa da mari saida ta koma kwance
tuni hafsa ta gigice, iffat kuwa batayi qasa a
guiwa ba tafara zuba mata bulala hafsa tana ihu,
ta mata lilis chan farhaan ya fito bayi da gudu
yayi turus da ganin madam iffaat.....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive