WACE CE ITA..?? 37
Na Abba gana
*********
Kwanaki sunja gaba har anyi sallah qarama,
iffaat zata koma gidan aikinta a birni, tun lokacin
da farhaaah yazo batayi waya dashiba jifa jifa
tana kiran su umma ta gaidasu, kuma farahnax
tana turo mata recharging wayanta.
Ta shirya tsab sai birni,
Su umma sunyi murnar zuwanta matuqa ko
banza umma nasonta Dan akwai bada labarin
ban dariya kamar me shi yasa daga umma har
Abba zaune sukeyi tana basu labari suna kwasar
dariya.
Wannan karo an samu chanxi iffaat ta dawo
amma ba komai tsakaninta dasu, musamman
umman farhaan kunyar su takeji! Da kuwa zaune
take tasasu gaba tana basu labari suna dariya,
gashi kullum tanada sabon labarin da zata
bayar, bata maimaici amma yanxu Dogon motsi
bata iyayi gabansu, Ashe akwai abinda zai iya
chanza wannan hatsabibiyar yarinya,?? Hmmm
sai soyayyah.. soyayyar da ita kanta batasan
tanayiba,
Kai amma ni abba na jinjinama duk soyayyar da
tayi tasirin chanxa wannan yarinya koda ta qara
wayewa yanxu...
*****
Iffaat miyasa tunda kika dawo kika daina bamu
labari?? ta sunne kai qasa tayi murmushi ba
komai hajiya! Nidai wannan zuwa hutu baiyimin
ba yarinya duk ta susuce sai rama takeyi? Ko
wani Abu ya faru bakyason fada mana??
Laaa hajiya bakomai Abba yace ki kyaleta kinsan
fa ta qara girma hankali yana shigarta, duk aka
saka dariya,
Farahnax ce ta shigo tare da wata yarinya
kyakyawa zatakai 24yrs kyakyawace sosai, tana
shigowa tace kinganta, yarinyar mai amsa sunan
suhailah ta gaida su umma da abba a kunyace,
ta kalleni cikin fara'a tace Ashe ma qaramace
sosai gata kyakyawa kuwa saidai tafini kyau da
kike cewa munyi kama., umma tace ai kuwa
nima sai yanxu naga wannan kama da kuke
cewa sunyi, saidai yata iffaat tafi kyau, sukayi
dariya gaba daya iffaat ta gaisheda suhailah
umma tace kuje daki mana, suka wuce umma
tace na bisu mama na tashi na bisu, anan
farahnax take baiwa Suhaila labarina sunata
dariya, sai nadan saki jiki dasu dama wani lokaci
zaman kadaicine ke haifar mata da damuwa bata
saniba..
Suna tsaka da hira wayar Suhaila tayi qara, ta
dauka tana kashe murya, duk da cewa da English
suke maganar hakan bai hanani fahimtar dawa
take maganaba kuma mi suke fadaba, farahnax
tana bani labari amma hankalina Sam baya tare
da ita qirjintane ke dukan uku uku wani baqin
ciki Mara dalili takeji Wanda ya haifar mata da
rashin natsuwa lokaci daya, Daidai nan kunnenta
ya jiyo mata maganar da takasa tantance
sanadiyar rudewarta sai ganinta tayi a asibiti....!
WACE CE ITA? 37
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.