shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 22 July 2015

WACE CE*******ITA? 71

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.??

71
.................by.........muhd-Abba~GanaTa sadaqar kawai har zata danna power Off ta
kulle wayar sai ta tsaya tayi clear din duk abinda
ta bude tabar wayanda ta gani ta danna power
off ta bude bayin, Tana jiran ya fara masifa akan
me zata Taba mai waya amma taga ya shiga
bayin baima kalleta ba tana ganin haka tayi sauri
ta ijiye masa kayan sa tana ijiye wa ko hannu
bata daukeba alarm ya fara bugawa na sallar
asuba.
Allah yasota da ya buga Tana bayi ai da asirinta
ya gama tonuwa, tayi murmushi yana fitowa
itama ta shiga tayi alwula tayi sallah......
********
Aiki ya sami iffatu duk yinin ranar Tana biye
dashi a latitude duk inda yaje Tana biye dashi
haka tayita saka mai ido har kwana uku ta gano
gurin da yake xuwa kullum ta gano gunda yake
yawon dare, hatta gurinda yake parking din
motarsa ta gane so zata fara aiwatarda aikinta
akansa.
Farkon abinda ta farayi ta Riga ta gano gunda
yake parking kuma tasan lokacinda yake xuwa
gurin, saida ta tabbatarda yana office ta kira
driver tace yakai motarta gurin ya ijiye tamai
kwatance ya kuwa je ya ijiye farhaan an qare
aiki akazo gantali tashin hankali abinda ya fada
kenan lokacinda ya hango motar ta, ko miya
kawo wannan yarinyar anan gurin?? Ya fara
tunanin ko tazo nemansane ya tafi akan tazo
nemansa ne kawai, bai tsaya bata lokacinsanaa
jikinsa na rawa yabar gurin bayan ta duba taga
yaje sai kuma taga ya bar gurin ya nufi hanyar
nasiha restaurant Tana ganin haka Tama driver
dinsu magana akan yaje da sauri ya dauko
motar bayan ya ijiye motar a gida dama tayi
kwalliya kamar wata amarya, yana dawowa ya
ganta kuma, ya kalleta kwalliyan ta ya sakashi
zargi,! To Ina taje miye na kwalliya ma! Cox bata
taba masa irin wannnan kwalliyar ba, Yanason
Ya mata magana amma yana tsoro, yasan
zatace shima mi yajeyi a chan? Ko kuma tace
ina ya ganta? Tinda bai gantaba gara ya bari
har y kamata da kanshi, haka ya zauna yana
tafarfasa har yayi bacci Dan baqin ciki ranar ko
fitar dare baiyiba..
Goben ranar sai baije gurin ba daga office ya
dawo gida kuma idan ya dawo saiya ganta gida
zaune ba inda tajee har kwana uku ranar na
hudu yaje gurin tana ganin haka ta tura driver
yaje yayi parking din motarta daga kan hanya
hanya ta yanda dole dole yaga motar tazo tayi
kwalliya abinta ta kame bayan ya fito hotel din
yaga motarta, mamaki ya kamashi, tana kallon
duk wani moving dinsa a latitude yana yawo
hakan ya tabbatar mata da nemanta yakeyi a
gurin tayi murmushi ya fito wajen gurin yayin
parking yana jiran ta fito kusan awa daya yana
jiran ta tafito amma bata ba labari, ya gaji. ya
riqa ya tabbatar da cewa nan gurin tazo yaja
mota Kamar wani mahaukaci.....
muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive