shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 27 July 2015

QARIN********JINI--- 16

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 16

Yaya naziah dai tasan mafarkine kawai nay
sabida haka tacemun shikenan za'afasa auren
kidaina kuka gobe zanyi magana da baba ta
lallabani har barci ya sake awon gaba dani
mafarkin dazu dai na sake mai mai tawa amma
a cikin mafarkin nawa sai na tambayeshi address
dinsa yagayamun, bayan natashi daga barci
koda na tuna address din sai naga address din
gidanmu ya bani, tun safee yaya naziah tazo
gurina ta ganni curko curko dani a daki.! na
maimaita abinda na gayamata dadare naqara da
cewa idan kuma ba hakaba Wllhy ZAN KASHE
KAINAH...!!! Hankalin ya naziah yay balaeen
tashi dajin maganar kisa bashiri ta kira babana
tagayamishi, baba bashiri yazo gidan, yaya ta
kirani nazo nagaisheda baba, yace oumulkhair
bani nazo miki da maganar aureba ke kikazomin
da ita, kuma ban aminceba saida na baki lokaci
nace kiqara tunani kikace kinji kin amince,
tabbas mutunchina wani abune da bana wasa
dashi duk abinda zaisaka mutumchina ya zube
zan barshi na farko duk wanda yaji kin kashe
kanki zaice auren dole na miki sabida haka ni da
kaina zanje gidansu Abdullah in basu haquri su
janye maganar auren Allah ya hada kowa da
rabonsa, ya miqe zai tafi natashi na russuna
gabansa ina kuka, baba dan Allah ka yafeni
wllhy ashirye nake da in maka biyayyah koda
kuwa zan rasa raina wllhy zan auri Abdullah
kuma harga Allah ba abinda zan aikatawa kaina,
baba kaci gaba da yimin addu'ah, baba ya shafa
kaina Allah ya miki albarka oumulkhair amma
aure anfasa bazanso in rasakiba akan abinda
bakyaso, ya qara gaba inata kiransa amma ina
baiko waigoba ya tafi, yan kwanakinnan naci
kuka har saida zazzabi mai qarfi ya kamani
kwanana biyu ina kwance ran na uku na warke
yau saura kwana bakwai aurena amma ba wani
shirye shirye da naga anayi yaya naziah
kolokacinda banida lafiya ba wani kula dani
takeba, haka dana warke ko magana batamun
umma kuwa tunda na fara zazzabi ko ya jiki
balle Allah qara lafiya abin duniya ya isheni
narasa inda zansa rayuwata inji dadi, na shirya
najee gidan mu natarar baba bayanan yafita
umma ina mata magana ko kallo ban ishetaba,
da taga na fara kuka sai tatashi tabar min palon
ina zaune saiga yaya habeeb ya shigo ko kallona
baiyiba ya wuceni nagaisheshi yayi banza dani
zai fita naqara gaisheshi ya juyo ya makamin
wata arniyar harara saida naga jiri,yace
mahaukaciyar yarinya wacce haukarta
tafiyemata mutunchin mahaifinta, daga yau karki
qara kiranada yaya niba yayanki bane wawuya
kawai hankalinki ya kwanta baba yaje gidansu
Abdullah yagamasu kinfasa auren yay tsaki
yafita, baba yaje gidansu Abdul tashin hankali..!!
haka nazauna a palon ummatata amma ba
wanda yake mun magana yaya saeed ma da
nakebi dana gaisheshi ashar ya duramin, narasa
abinda yakemin dadi ina zaune naji qarar motar
baba da gudu naje gunsa fuskarsa a daure naje
na fada jikinsa ina kuka...
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive