shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 20 July 2015

WACE CE******ITA? 58

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 58
Na ABBA-GANA
Ta sa hannu tana qoqarin kwacewa amma ta
kasa ya qara janyota da qarfi saigata saman
qirjinsa, ta daga kai tuni idonta sun cika da
kwalla Dan tsabar azabar da takeji, da qarfin
hali, tace, so bansan kacika wayayyeba sai ka
aikata abinda kake da niyyar aikata wa aikana.!!
yanxu ya gane manufarta tuni ya saketa yayi
tsaki ya fada bayi ya kulle kansa cike da baqin
ciki da nadama, a duniya ba wacce ya raina
kamar iffaat amma itace take gwadamai axaba,
iffaat kuwa tana samu ya saketa ta fita da sauri
ta wuce gida tana zuwa ta fada dakinta ta kulle
tana kukan takaicin rayuwa da mutum irin Yy
farhaan ta daga kai taga hoton Yaya Suhaila da
Yy farhaan sun rungume juna suna dariya tayi
tsaki,ta tashi ta cireshi ta saka a drawer ta
dawo taci gaba da tunaninta har barawo bacci
ya dauketa, bayan ta tashi taje gun mama..
Ah ah yaushe kika dawo?
Tayi murmushi wallahi tun dazu na dawo nasan
kina bacci lokacin shi yasa banma zo natayar
dakeba, okay suka yi tadi mama tana tanbayarta
ta gyara Gidan dakyau kuwa? Dan tasan son jiki
ya mata yawa
Laaa mama kin manta nayi aikatau suka saka
dariya gaba daya, Yaya Ameen ne yazo da Yaya
Ali suka zauna akayi tadin dasu suna cikin
magana Yy Suhaila ta kira...
Sister sorry na sakaki aiki da yawa,!laa kinji dai
Yy Suhaila wane aiki kuma idan ban mikiba
mawa xan yiwa, ta fara godiya, wallahi idan
kinamin godiya zan kashe wayata, to nabari yi
haquri, kin tarar da farhaan a gida?? Wallahi
Naso nace idan yananan ki masa Dan girki,
Tseeeet tayi kamar ruwa ya cita qirjinta yake
bugawa, lokaci daya ta tuna abinda ya faru
tausayi Yy Suhaila ya kama ta Amma bazata iya
fada mataba, hello kinajina kuwa sister? Tayi
xumbur ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi..
Inaji Yy Suhaila, to ki bawa mama wayar na
miqawa mama ta tashi tsaye, Yaya Ali ya kamo
hannunta..
bayan sun qare yace wani abokinane yakeson ta
kinma sanshi Nurane mama tace nikam ko
sunansa banaso bare shi na tsani wannan yaron
akwai shegen rawar kai, iffaat tace wallahi nima
mama na tsani Nura kamar me nima dai jabo ba
abarni a bayaba gun tsanar sunan Nura mugu.
Duk aka saka dariya kowa ya tsani Nura Allah
sarki har ya bani tausayi......
**
Goben ranar tinda safe Suhaila tayi waya da iffat
ta gaya mata sun kamo hanya
Guraren qarfe 11 iffat na zaune da mama dasu
yaya da yake yau Saturday, wayar iffat tayi qara
laaaa yy Suhaila hatman sun iso, hello Yy
Suhaila kuna ina? Kun kawo hala?
Taji namiji yace ke sister din Suhailar ce ??
Tace Eh kai waye?
Sorry Dr ne daga Chika, yayar Ki sun sami
accident Allah ya mata cikawa driver kuwa
gashinan kwance ya kakkarye?
Iffaat wata irin qara ta saka ta fadi
sumammiyaaa....
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive