shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 22 July 2015

WACE CE******ITA? 66

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??66by

muhd- Abba~GanaTaci pizzar sosai suna dan labari sama sama
chan ya sako zancen auren ta da farhaan irin dai
yana son ta amince ya nuna mata illar fushin
iyaye akan yayansu, jiki a sanyaye tace mishi ta
amince, Dan murna baisan lokacinda ya tashi
yayi rawaba ya juya itama abin ya bata dariya
nima abba abin ya bani dariya, yana ta saka
mata albarka, yaje jikinsa na rawa ya gayawa
mama da Yy Ali sun ji dadi ko ba komai sun
yanke shawarar idan taqi aminta za'a bar
auren..
*************
Magana ta kowane ban qare ta kan kama iyayen
sai murna suke sunata shirye shirye, amma
amaren kam ko a jikinsu, ana saura kwana biyu
daurin aure saiga goggo da dijee da rukayya
sunzo, koda sukazo iffaat tana skull Dan ita
wannan shirye shirye bai hanata zuwa
makarantaba,
Koda ta dawo bakin qofar dakinta taga wasu
takalmi Masu kama da kito amma dai na
matane, ta shiga dakin saiga su dijee anyi arshe
arshe tsakayar daki da yayanta biyu rukayya ko
yarta daya da ciki ta kallesu ta kwashe da dariya
harda durqusawa qasa Dan dariya, tayi dariya
saida ciknta yayi ciwo suko sun tsaya kallon
ikon Allah ta dago ta qara kallonsu nan ma ta
kwashe da dariya dijee tace ke bamusun iskanci
Dan kin zama Yar birni zaki ijiyemu kina mana
dariya kamar Kinga tutu...!!
ta harareta ta zauna da kyau tana dariyar tace
wallahi mamaki nakeyi wai dijee da Yara har
biyu! Ta qara saka dariya dijee ma sai ta dara,
ta kalli yayan tace amma dai dijee kina dukansu
ko? Rukayya tayi charab ta chabke tace ai
yanzu duk bala'en dije akansune Dan har danbe
tanayi da uwayen yara akansu, dijee tace ke
rukayya banason sharri da zuwa ko gaisawa
ba'ayiba zaki fara mini sharri, nan dai qawayen
suka yini suna tadi suna dariya duk da qauyanci
su bai sa ta gyamacesuba tunda itama chan aka
fito sun cire mata kewa matuqa kuma bata bari
suka gane cewa auren nata sai a hankali bane..muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive