shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 26 July 2015

WACE CE********ITA? 79 & 80

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.?? 79
*******by**********

muhd-Abba~Gana


Kusan sati daya da tafiyar farhaan amma still
siyo abinci take ta kula iffaat akwai saurin sabo
kuma batada matsala amma kuma batason
shishigi, ranar suna zaune sai matar tace yau
nayi mafarkin Dan wanke, iffaat tace Allah ko! Ki
bari anjima idan na fita sai na siyo miki, matar
tace aah gara dai mu girka kayan mu ko mi kika
gani, iffaat tace gaskiya ban iyaba, sai na koya
miki ko bakyaso tace tanaso, anan iffaat tabata
labarin cewa tunda take bata taba girkiba, matar
nata mamaki ace mace bata iya girkiba, haka dai
matar ta dage ta koyama iffaat girki kunna gas
yanda akeyin komai tace akwai books na girki ta
siya, tace mata, wallahi girki shine mace duk
kyanki da yanga idan baki iya girkiba baki cikaba
bakida daraja a gurin miji, matar dai ta kula
iffaat gayun banxane bata iya komaiba, a labari
iffaat take fadamata cewa ai idan taga mijinta
yana magana da wata ubanta takeci ta mata
aski da bille matar tayi dariya sosai wai bille,
tace to aike iffatu ba haka akeyiba baki
kyautatawa miinkiba ya za'ayi yaqi Neman
mata, kina gani maxan yanxu ko kin kyauta tasu
ya kuke qarewa bare baka kyautata musu,
wallahi kiyi hankali ki San ciwon kanki ki fara
dafe mijinki sosai sannan idan kin Ganshi da
wata sai kisan abinda zaki mata, amma haka
kawai baxaki hanashi abinda yakesoba ke baki
biya mai buqatansaba ki hanashi ya nema!! Ai in
gaya miki kina zaune saidai kiga kishiya, ta dafe
qirji kishiya!!? Sosai kuwa kishiya, Allah ya
rabani da kishiya, Yan zu maman Nargees ya
zanyi,? Ya zakiyi kuwa illa ki koyi girki ki iya
kwalliya koda naga kwalliya ke ajin farkoce ki iya
shagawaba idan yana gida ki manne masa duk
motsinsa akan idonki, iffaat ta kwashe da
dariya.! Miye abin dariya? Tace ba komai, haka
dai tayita gaya ma iffat abubuwan ta bata
sirrikun mallakar miji wani abin iffaat tayita
dariya tana mamaki, bayan ta tashi taje ta
kwanta a nan ta fara tunanin maganganun da
ake fada mata gaskiyane dole ta fara saba masa
da kanta sannan taje chin uban na waje....
WACE CE ITA..??

80
muhd-Abba~Gana

To amma ai ba laifinta bane? Shine bai
nemetaba! Wata zuciyar tace yaga fuska bare ya
nemeki? Aike ya dace ki kwatanta kiga yanda
zai dawo hannunki, wata zuciyar tace kawai ya
rainakine yana jiran kikai kanki ya qare dake,!
Tayi tsaki. Miye mafita idan bata mantaba Aysha
armiya'u mada ma haka tace mata farahnax ma
da taxo haka tace mata a skull ma idan suna
tadi zancen kenan daya kyautatawa miji, ga lada
ga la'ada. Tayi murmushi ta janyo wayarta ta
dauko hoton farhaan tana kallo tana zooming
batasan lokacinda tayi kissing din bakinsaba tayi
jimm gatada miji har miji amma manemin mata!
Lallai ta bala'e bazata wani gyarashiba ya
kamata ta dandana masa Zumar ta sannan ta
kasa ta tsare idan ta kama ta raka anan ne idan
yaqi dainawa taci gaba da chin ubansu..
100% ta aminta da haka so tana jiran dawowar
farhaan ne taga yanda zata fara, kunya takeji
anya zata iya? Taya zata fara!? da shedana da
wasa zata cusa kanta, har komai ya daidaita, ta
lashe lebenta tayi murmushi ta rungume pillow
Allah ya shirya min kai Yy farhaan.. Haka dai
madam iffaat tayita tunani har bacci ya dauke
ta,...
***********
suna waya akai akai amma dai ba wani chanxi
data nuna mai, shikam hadda cemata yake yayi
missing dinta takanso tace bawani Dan tasan
yana tare da yan matansa amma kuma sai ta
share...
kwanci tashi har farhaan yayi wata daya a qasar
iffaat kuwa lokacin ta gama iya girki nikaina abba
idan tayi girki badan kada aga kwadayinaba
wallahi dasai naci, amma ba hali, girkinta haka
yake qamshi kamar me maman nargess hatta
yanda ake tafiya gaban oga saida ta koya mata
da yanda ake shagwaba a narke jikin miji duk ta
koya mata cox practice sukeyi maman Nargees
ce iffaat iffaat ce farhaan sai tace ta fita waje
tana shigowa maman Nargees taje ta rungume
ta tana mata wani Abu iffaat Dan dariya har
hawaye takeyi, anya zata iya yin haka kuwa??
Maman Nargees kuwa sai qarfafata takeyi, har
dai taji zata iya, ga iffaat gwana gashi dama ba
auki zatayi dadin kakkarya jiki....
Daidai wannan lokacin farahnax ta haihu ta
sullubo yarta kyakyawa kamarsu daya da
farhaan idan kaga Yar kace ta farhaan ce Dan
kamar har ta baci da iffaat ta tura mai hoton
baby ya gani yace da babyn Suhaila ta rayu da
itama yasan kamar shi zata dauko iffaat dai
batace dashi komaiba, yace amma insha Allah
ina dawowa zan samo wata zaki tayani nemowa,
tayi kamar bata gane mi yake nufiba, tace eh
mana duk inda ake siyowa kaima ka siyo yayi
murmushi ya basar Da maganar....


muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive