shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

QARIN***********JINI---15

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 15

Tun da na dawo gida nasamu baba nagayamasa
abinda yasa nadawo gida, yace inje inqara tunani
shima zaiyi tunani bayan sati biyu da maganar
da nayiwa baba yakirani nazo,
Oumulkhair dama nakirakine akan maganar da
kikazomin da ita sati biyu da suka wuce, nace
kije kiyi tunani mikikayi tunani akai?? Khair tayi
shiru batace komaiba na tsawon minti uku...
kinyi shiru, baba ni nariqa na bar komai a
hannunka duk hukunchinda ka yanke shirye nake
da in karba,!! Kanta aqasa ta bashi amsa. Allah
yay miki albarka dama tun lokacinda wannan
mutumin ya kadeki da mota ya cemun yana
nemawa qaninsa aurenki nace masa yayi shiru
sabida yanzu andaina auren hadi, yan mata da
samari sun waye sabida haka sam bazasu yarda
da auren hadiba ya dade yana min maganarki
qarshe nace ya bani lokaci inyi shawara jiya
muka hadu dashi a saman gidana, sai gashi ya
dawo min da maganar yanaso aba qaninsa dama
yazo gurinki dan ku dai daita kanku ke kuma
gashi kinzo da wannan maganar inaga shikenan
sai a baiwa yaron dama yazo ku dai daita
kanku. Nidai baba idan kayi bincike akan yaron
ka tabbatarda cewa yaron kirkine iyayensa
mutanen kirkine basai yazoba kawai adaura
auren na amince.! aah oumulkhair bazamuyi
hakaba kibari kawai yazo kema kiganshi yafi
nidai baba basai yazoba..! To shikenan Allah ya
miki albarka.. bayan sati daya da maganar
dangin gidansu Abdullah sukazo gidanmu ganin
amaryarsu, tabbas danginsa mutanene masu
kirki da girmama jama'a yaya naziah ta tarbesu
tarba ta mutunchi da girmamawa nikaina naji
dadin ganinsu ko bakomai naga dangin mijina
suna da mutunchi zanji dadin zama dasu, chan
wata mata wacce ina kew tata zaton matar
yayanshine ko kuma inche mutumin da ya
kadenice tace, ashe Abdullah jinin da yabayar wa
matarsa ya baiwa jinin gatanan Allah yayi shi
zai aureta duk akai dariya harnima saida na
murmushi, abinda yafi bani mamaki shine
maman Abdullah sai ina ganin kamar na santa
sosai, har inajinta acikin rayuwata amma narasa
inda nasanta maganar aure ta kankama ansaka
rana da sadaki da komai amma kuma har yanzu
bansan wazan auraba.. Yau watana daya da
dawowa daga AYNN tun da nadawo dream guy
dina na daina mafarkinsa sai daren yau nay
mafarkinsa mafarkinda yay balaeen daga min
hankali naganshi ya durqusa aqasa yanata kuka
kuka mai tsuma zuciya nazo kusa dashi amma
na kasa masa magana, yacemin yanzu sabida
girman kai irin naki yasa kika tafi kika barni
yanzu sabida son zuciya irin naki kika gujeni da
kinsan yanda sonki yake a cikin qirjina da baki
barniba haba. Khair ki tausayamin mana wllhy
ina qaunarki fiye da tunaninnki inason
kasancewa tare dake har qarshen rayuwata karki
barni.. na kallesa nace masa sai dai kayi haquri
yau saura kwana tara adauramin aure
WHAT..!!!??? Wllhy duk ranarda kika auri wani
baniba KHAIR zan kashe kaina..!! saina kashe
kaina..! rayuwata bake batada amfani zan masa
magana sai naga ya juya ya dauko wuqa zai
dabawa kansa a figice na farka daga barci na
kwarma ihu da kuka mai qarfi yaya naziah
tashigo lafiya oumulkhair?? Yaya na fasa aure ni
dream guy dina nakeso....
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive