Gudanar Da Harkokin Gida
# Darasi Na 3
# Tsafta
A taqaice tsafta kalma ce da take nufin kawar da
qzanta ko dauda ko datti da kuma mummunan
wari
ko kawar da duk wni abinda baya da kyawun gani.
Don haka tsafta ta shafi abubuwa kamar haka:
1. Jiki: Idan aka ce tsaftar jiki ana nufin wanke
gangar jiki da ruwa da sabulu ko abinda zai tsaya
a
matsayinsu su wanda zai taimaka wajen kawar da
dauda da wari.
Haka kuma akwai wata hanya da mace zata kawar
da dauda daga jikinta ba tare da amfani da ruwa
da
sabulu ba, wannan hanyar ko ana kiranta da
Dukhan
wato hayaqi, ana amfani da itacen farar qaya ko
magarya.
Yadda ake yin sa kuwa shine mace zata rufe
dukkan
jikinta da bargo a lokacin da ta tube ta zauna ta
ware qafafafunta alhali wannan itacen yana
qarqashinta, yana bada hayaqi a hankali, shi itacen
za’a dan jikashi da ruwa sannan asa a cikin wuta,
dalilin jiqawa shine domin kada ya haifar da zafi
sai
dai hayaqi. Yana matuqar gyarawa mace jiki da
matancinta domin yana mayar da mace yarinya
kuma ya ma fi wanka tsaftace jiki. Amma kafin
mace
ta shiga cikin bargon zata shafe jikinta da KARKAR
(wani mai ne da ake hadawa in babu sai a shaf
man
zaitun)
dan
mu qaru>
GA YADDA AKE HADA KARKAR
Za’a samu bawon lemon zaqi a jiqa ya kwana a
ruwa tare da kanunfari sai a zuba a tukunya mai
tsafta tare da man simsim (Ridi) ko man zaitun ko
man kwakwa ko man gyada tare da wuta mara
qarfi
yana dahuwa har ya tafasa za’a sauke idan aka
karya kanumfari aka ga ya karye to yayi.
2. Baki: Daga cikin tsaftar jiki akwai tsaftace baki,
aqalla awanke baki da maganin wanke baki ko
aswaki sau biyu ko uku a kullum, kuma dadi akan
haka ya kamata mace ta riqa amfani da alawa
(sweet) mai dadi mai bada daddadan qamshi a duk
lokacin da zata kusanci mijinta.
3. Aski: Anan ana nufin aske wurin da suke tara
gashi, kamar hammata, mara da sauransu, wanda
dama yana cikin fitra guda biyar da Manzon Allah
S.A.W ya fada, aqalla mace ta tabbatar tana yin
wannan aski duk bayan kwana arba’in.
4. Qumba (Farce): Shi ma yanke qumba yana daya
daga cikin fitra guda biyar wanda shi ma jigo ne
sosai a cikin duniyar tsafta. Idan so samu ne ya
kamata a qalla a yanke qumba a cikin kowanne
sati,
amma sai kaga wata farcenta kamar ta
gwagwgwan
biri.
5. Kaushi: ya kamata uwar gida ta kula da kaushin
qafa tabi hanyoyin da zata bi wurin kawar dashi ko
magani ko wankewa ko zuwa saloon dss. Wata
hanya da mace zata iyayin maganin kaushin qafa
shine ta samu ruwan zafi ba sosai ba ta zuba
shampoo a ciki sai ta saka qafafauwa a qalla minti
goma sai ta goge qafar da dutsen goge qafa sai ta
fitar ta shafa mai kamar basilin ko zaitun sai ta
sanya qafar a cikin leda kamar minti biyar amma
ba
wai sai zata tafi unguwa ba.
Tsaftar Gida
Tsaftar gida ya hada da wurare kamar haka:
1. Bandaki: dole mace ta kula matuqar kulawa a
wajen tsaftace bandaki a kullum tare da amfani da
magungunan kashe qwayoyin cuta da kuma masu
sa wuri qamshi in harda hali, duk da cewa basu da
wata tsada, rashin dai wasu basu saba ba, idan
kuma babu halin saya wankewar da kawar da
yanar
gizo-gizo a kullum, sai a kula tare da watsa
kalanzir a wasu lokutan ko kullum musamman
bandakin da yake na kowa da kowa ne.
2. Dakin Girki (Kitchen): Kitchen yana daya daga
cikin wuraren da ake tantance mace mai tsafta da
qazama, saboda haka dole mu riqa kulawa da
tsafatar kitchen kuma kasancewar wuri ne da ake
dafa abinci wanda munsan abinci yana daya daga
cikin jigon rayuwar ‘dan Adam, sai muka ga ya
zama wajibi a kula da wajen da ake tanadarsa.
3. Tsakar Gida: Dole mu riqa kulawa da tsaftar
tsakar gida, domin hakan zai taimaka wurin
tabbatar
da tsaftar sauran wurare kamar kicin, bayi, dakin
kwana dss, dadin dadawa duk wanda ya shigo
gidan
zaiga gidan fes-fes wanda da ma a matsayinki na
mace ana buqata a kowanne lokaci ki kyautata
ganin Maigida da sauran jama’a a matsayinki na
makaranta mai tarbiyyantarwa, da kuma tattara
kayayyaki ko wane a sa shi a muhallinsa, na kicin
akai kicin, na bayi a kai bayi, na daki kuma a
shigar
dasu daki, ba wai a barsu a tsakar gida ba ko da
an wanke bare ace ba’a wanke ba.
4. Dakin Kwana: ‘Dakin kwana dole ne mu kula da
gyaranshi fiye da ko’ina a cikin gida, domin nanne
wurin da Maidiga yake samun cikakken nutsuwa
da
hutawa da samun kwanciyar hankali da dai
sauransu. Saboda haka dole ne mu riqa kula da
gyaranshi qwarai da gaske, da kuma qoqarin
qawatashi da duk abinda Allah ya hore, da qoqarin
sanya turare da abubuwa masu sa qamshi a
kowannen lokaci musamman lokacin kwanciya. In
har Allah ya hore yana da kyau ayi amfani da
turare
na ruwa ko na hayaqi kala daban-daban, kina iya
amfani da kala hudu ko biyar a lokaci daya
kowannen ki sa shi a bangare daban. Misali na
zanin gado daban, na filo daban, idan filon yafi
daya
kowanne ki sa masa nashi daban, na labule daban,
na tsakar daki daban, na kujeru daban dss. Hakan
zai bada wani irin qamshi mai tada hakalin
Maigida
ya rasa wanne irin qamshi ne wannan kuma daga
ina yake fitowa !!!
Tufafi
1. Tsaftar Tufafi: Dole ne mace ta kula da tsaftar
tufafinta da na ‘ya’yanta da na Maigidanta, mu
sani
cewa yawan kayan sawa wata baiwa ce daga
Allah,
amma tsafta da wanki da guga da fesa turare idan
ana gida shi ake nufi da tsafta, da wannan ne
mace
zata amsa sunanta na mace.
2. Kwalliya: Ya kamata mace ta kasance mai
yawan
kwalliya da cancanja salo kala-kala ta zamani
domin Maigidanta, ba abin kunya bane dan mace
taje koyon kwalliya, ka da ta tsaya ga sa hoda da
jagira kawai, akwai yanayin kwalliya kala-kala,
hatta
su kansu kayan akwai yadda zaki sa su su birge
Maigida.
3. Wajen Girki: Ana buqatar mace ta kula da
tufafinta a lokacin da take girki dan haka shi zai
qara tabbatar da tsaftarta. Saboda haka sai ta riqa
amfani da qyalle ko tusmma na goge-goge, hakan
zai taimaka qwarai wurin zama da kwalliyarta ko
da
tana girki kamar yadda bayani ya gabata, in kuma
ta
gama girkin sai tayi wanka idan akwai buqatar
hakan amma bada ruwan qanzo ba!
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.