KOZAN IYA QARA GASHI, SABODA MIJINA ???
KOZAN IYA QARA GASHI, SABODA MIJINA ???
Malam nayi rashin lafiya kaina ya kwakuye,
mijina yana bakin ciki, idan yaga kaina.
Kozan iya kara gashi, don zaman auranmu ya
kara dadi ???
AMSA.
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To 'yar uwa wata mace taje wajen Annabi
(s.a.w) tabashi labari cewa:
'Yarta tayi rashin lafiya gashin kanta yazube,
kuma gashi mijinta ya umarceta data kara mata
gashi, shin zata iya Qarawa ???.
Sai Annabi (s.a.w) yace mata:
A'a, saboda an la'anci masu Qara gashi"
Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba
ta:4831.
Hadisin yana nuna cewa:
Baya halatta mace taqara gashi, koda kuwa
mijinta ne ya umarceta.
Saboda hakan zaisa tashiga tsinuwar Allah.
Allah shine mafi sani.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.