WACE CE****ITA? 48
WACE CE ITA..?? 48
Na ABBA-GANA
Tayi ajiyar xuciya Ta juyo ta kallesu sunyi cirko
cirko dasu, da kunburarren bakinta take musu
magana, kiyi haquri Dan Allah wallahi bansan
lokacinda na daki qawarkiba, sukace ba komai
kema kiyi haquri, nan dai suka yafi juna suka
qulla qawance da ita da alqawarin zasu
taimakamata da duk abinda sukasan zasu iya.
Haka suka zauna Kowa shiru har aka tashi
makaranta..
*
iffaat na zuwa gida mama ta fara tambayar ta
lafiya kike kunbura haka kamar jabo tayi kuka??
Wallahi mama anyo korane, zasu shiga class tayi
karo da wata frnd dinta sai kuma ta fadi qasa
shine bakinta ya kunbura, Subhanallahi. Kinga
yanda kika kunbura kuwa? Allah ya tsare gaba
ta amsa da amin ta wuce dakinta.
Bayan ta shiga daki ta cire uniform, ta zauna ta
fara tunanin abinda yan matannan suka fada
tabbas kuwa idan har abinda suka fada shine
kaji kanason mutum to wallahi tanason Yaya
farhaaan, aiki jaa wanda zai zama mijin yayarta
takeso??
Dole ta dauki mataki wa zuciyarta.! Tayi
murmushi Kai amma so shegene shine ya hanata
sukuni shekara da shekaru! Amma so ya
wanketa! Waima miyasa bata ganeba? Tayi tsaki
ni ko zan mutu zan auri Yy farhaan ne gashi da
shegen son mata! Duk maganar da takeyi aranta
takeyinta amma Sam zuciyarta bata aminta da
ko kalma daya tataba, kawai tana fadane amma
tasan yanda takeji da gudu idan yace yana so
zata amince,...
Hmmmm dole zuciya taso Yy farhaan ta saba
dashi, yy farhaan duk inda namiji mai lfy zai
shiga yana shiga haka tayita karanto siffarsa da
maganar sa da tafiyarsa da murmushinsa tana
murmushi, lallai ta yarda tanasonsa but miye
mafita???
Dole ne ta ijiye sonsa taci gaba da danneshi har
Allah ya bata mijinta tayi aure??
Anya zata iya kuwa??
Zaki iya mana dayar zuciyarta ta bata amsa aiki
ja gabanta..
Suhaila ce ta shigo tana waya ta gane da
farhaan take wayar kuma taji yanayinda ta saba
ji amma ta basar.....
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.