shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 22 July 2015

WACE CE******ITA? 73

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??73
Na ABBA-GANA
Farhaan kuwa zaune ya kwana yana ta tunane
tunane, kamar ya hade rai ya mutu Dan baqin
ciki...
Ya janyo wayarsa ta bude hotunan ta yana kallo
tabbas yasan yana son iffaat babban abinda
yake damunsa idan ya tuna WACE CE ITA.. Yar
aikinsace fa wannan gani da yake mata har
kullum shi yakesa baya darajata, amma yasan
yanasonta babban dalilin da yasa ya qara
aminta da auren Suhaila Dan sunyi kama da
iffaat ne, hakadai yayita mulmula saman gado
kamar an xuba lemu a paranti sai zagayawa
yakeyi yana juyi wata zuciya tace idan ma Yar
aikinkace ai matarkace yanxu yakamata ka bata
haqqinta na matarka, ko ka sami sauqi, chaiiiiii.
qarshe ya tafi akan iffaat bazata taba aikata
hakanba amma xaiyi magana da driver dinta yaji
gaskiyar magana,.
Hmmmm nidai abba Bantaba tunanin farhaan
yana son iffaat hakaba ba sai yau Ashe shima ya
kamu bamuda story,
Haka gadon ya masa fadi yasaba da kwanciya
tare da ita koda ba abinda sukeyi amma yana jin
qamshin jikinta, yanajin dadi amma yau babu...
Tunda qarfe 8 yaje daukota umma tace sai ya
dawo office sannan yazo ya dauketa..
Yinin Ranar dai bai gane komaiba gashinan sai a
hankali, har ya taso ya dawo office yazo umma
tamusu fada musamman shi, sannan suka tafi,
iffaat dai taji tsoro fa yanda ya mata ya firgitata
ba kadanba, amma bata nuna masaba
So ta yanke shawarar bazata qara kai motar ta
gurinba...!! Iffat Kura ga tsoro ga ban tsoro.!!
****
Farhaan ma haka bai qara xuwa Zaria hotel ba.
Bayan yayi bincike ya gano shirinta dariya kawai
yayi, lallai wannan yarinya akwai rigima..
Yanxu ta saka masa ido sosai a latitude tana
yawan ganin yana zuwa wani guri so abinda ta
farayi shine ta sami mai adaidata sahu ta
biyashi tace kawai ya bishi na kwana biyu yaga
mi yakeyi a gurin ai kuwa an kawo mata labari
wata yarinya yake dauka gurin tasa aka duba
mata gidansu yarinyar da komai nata, ta riqa ta
shirya abinda zata mata ta kiyaye lokacinda
yake sauketa ya wuce. ta sami almajirai su biyar
tace aiki zasu mata farhaan na sauketa ta riqa
ta tare hanyar tasa yaran suka tareta har ta fara
xaginsu iffaat taxo ta wanketa da mari tace
wayannan almajiran sun fiki daraja Yar iska
yarinyar.! mamaki ya cikata hakadai iffaat tace
ta shiga wani kongon gida zasuyi aiki, ta turje
sai tasa almajiran nan suka durata cikin kongon
gidan taso tayi taurin kai sai taga batada mafita
illa miqa wuya, bayan sun shiga iffaat ta zauna
saman wani bulo tabata almakashi tace ta yanke
gashin kanka ta fara gaddama iffaat ta qara
waske banxa da mari saida bakinta ya fashe da
jini ba shiri yarinyar ta karba ta aske iya yanda
zata aiya iffaat tace bai mataba haka tasa reza
ta mata tall kobo almajiran sai dariya suke nima
abba gana dai na dara cox mace ba gashi batayiba!!
bayan ta mata gwandal tace saura Abu biyu
kuma, matar ta fara kuka tana tataimaketa iffat
tace ta rufawa kanta asiri ta bari suyi aikinsu
idan ba hakaba zata qara mata wani
punishment,mata kuwa sai kuka take tana roqon
iffaat tayi haquri amma iffaat ko kallonta
batayiba tasa almajiranta suka danne mata ita
ta mata bille guda biyu a fuska sannan ta fito
da bulalarta ta zaneta saida ita kanta ta gaji da
dukan nata sannan ta barta tace idan an
tambayeki wa ya miki haka kice iffaat ce ko kice
Mrs PURHUUN..... ta fita tabarta nan tana
kuka.....by abba gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive