"ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"
"ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"
Shafe-shafe yana da illoli masu tarin yawa
musamman ga ’ya mace.
1. Na farko yana canjawa mace launin fatarta.
Fatar da ba a yiwa shafe-shafe, ita take bada
kariya daga cututtuka da sauran kwayoyin da
suke yiwa fata barazana.
Fata ta asali tana ba mace garkuwa daga zafin
rana.
Bayan mace tayi bilicin zata kasance cikin yawan
laulayi, bazata iya yawo a rana ba domin zataji
kamar ana kwara mata ruwan zafi, saboda tarasa
fatarta ta asali datake bata garkuwa daga zafin
rana.
2. Abu na biyu shi ne, mai bilicin bazata sami
kariya daga cutar daji ba wato (Cancer), wadda
cuta ce mai ban tsoro da wuyar sha’ani, ba
kasafai aka fiya samun maganinta ba.
Cuta ce wadda take kama sassan jikin mutum,
yawanci akan yanke gabobi ko wuraren data
kama.
Duk wannan yasamo asali ne a sakamakon
bilicin.
3. Mai bilicin za ta rasa kuzari, Idan kafin ta fara
bilicin tana iya yin aiki na tsawon sa’a uku bata
gaji ba, to yanzu ba lallai bane ta iya na sa’o’i
biyu, hakan ya haifar mata da nakasu, maimakon
a nemo kiba sai aka iske rama.
4. Ba a nan kadai illar shafe-shafe ta tsaya ba,
akwai illoli masu tarin yawa da kuma tsoratarwa.
Misali bilicin na jawo gyambon ciki abin da aka fi
sani da olsa (ulcer) wanda mafi yawanci akan
dauketa a matsayin rashin cin abinci ke kawota.
Daga ciki akwai kassara dukkan wasu sassan
jikinki masu amfani walau wadanda ake gani a
zahirance da kuma wadanda ba mu iya gani,
kamar irinsu:
1. Hanta.
2. Qoda.
3. Hunhu da sauransu.
Wadannan duk suna tagayyara ne sakamakon illar
bilicin.
Da fatan za'a kiyaye.
jaxa kallahu kairan
ReplyDelete07068059339
ReplyDelete