WACE CE ITA???****46
WACE CE ITA.?
46 by
Abba~Gana
To mama mixance dasu?? Yy amin yace kice na
aiketa har yanxu bata dawoba, ta tafi cike da
baqin cikin da jimamin faduwar Yar uwartah Allah
sarki Suhaila akwai sanyin hali.
Bayan ta tafi yaya yake tambayar mama miyasa
baki fada mata gaskiya ba?? To sai kawai nace
tana kallon su sai ta suma ai kaga dole aji
tabakinta kamin ayanke hukunci,ya jinjina kai
hakane, anan suka zauna har saida su farhaan
suka tafi, Suhaila taxo ta fada musu sun tafi, su
tashi su koma cikin gida. Iffaat tace ita batason
chikin gida dakin yayanta zata zauna, dama
iffaat da naci sukayi sukayi Amma inaaa ko bude
Ido batayiba bare ta tankasu suka gaji suka
barta, har sunkai bakin qofa, Suhaila ta dawo.
Suhaila tace Iffaat na kawo miki kayan da Yy
farhaan ya siyo miki??
Ta daka mata tsawa da bataso. saida su mama
suka jiyo kuma duk abinnan da akeyi idonta a
rufe suke taqi budesu, tana budewa hawaye ne
zasu fito..
******
Bayan faruwar haka da yan kwanaki iffaat yanda
take jin ta tsani Suhaila ba dalili yana matuqar
damunta, duk abinda takeyi idan Suhaila ta saka
hannu sai ta tsani wannan abin tabarshi kenan
har abada, idan kuwa ta saka bakinta sai ta
gwaleta gaban ko waye, ranar maman Suhaila
hajiya kulu taxo gidan yini dan yinin da tayi ta
fahimci yanda iffaat ke yiwa Suhaila sai ranta
baiyi dadiba har take tambayar Suhaila tana
kuwa jin dadi bayan xuwan iffaat?? tace lfy lau
idan kikaga tana haka to wani ya bata mata rai
a skull sai ta sauke akaina, maman Suhaila tayi
dariya tace kice iffatun dai har yanxu hukumace
kenan suka dara gabaki dayansu...
***
Ranar iffaat tana zaune gindin bishiya a
makaranta tana shan malt da snack sai taji
wasu yan mata suna tadi akan soyayya ta kuwa
kashe kunne, dayar take bada labarin cewa
tanason yaron qanin baban ta amma batasan
yanda zata bullowa abinba tana bayanin duk
abinda takeji a ranta game dashi dayar ma tana
fadar nata keni Zumar abinda yafi bani haushi
baimasan inayi, Zibraheeem tace kar kuwa
kisake ya sani Dan raini ne zai shiga tsakaninku.
Iffat sai taji d same da abin da takeji suma shi
sukeji, ta juyo ta kallesu sun girmeta duka ta
musu sallama, please tambaya ce dani, naji kuna
wata magana, yanxu kuna nufin duk maijin
wayannan abubawan da kuka fada shine me,??
dayar tace its mean ya fada tarkon soyayya!! ta
kallesu, kuna nufin nima na fadane? Toni wa
nakeso?? Suka kalli juna suka kwashe da dariya,
mu muka San Wanda kikeso, dayar tace Wanda
kikejin haka
akanshi shi kikeso!!
Ta zare Ido kuna nufin YAYA FARHAAAH
NAKESO??
suka kalleta sukayi tsaki ke baquwace yarinya
dayar tayi dariya tace kinji suna mai dadi daji
gayen zai hadu, daji akwai zafi a gunsa har naji
inasonsa !! Iffaat ta juyo a fusace keeee ta
wanketa da mari.....uhumm toh fah!! mu hadu a kashina gaba
Abba~Gana
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.