shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 22 July 2015

WACE CE********ITA? 70

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??


70


...................by.......
....


muh-d Abba~Gana


Taje ta zauna sai ta kasa chin abinchin don an
hanata fita kuma sai a hanata xuwa skull...
Wasa wasa iffaat na Neman wata daya Gidan
farhaan baya kulata itama bata kulashi amma
rashin xamansa gida na damunta ko ina yake
zuwa Allah masani kuma bata gane takunsa,
Ranar tana zaune dabara ta fado mata yanda
zata gane ina yake tafiya, bayan ya dawo
gantalinsa na dare ya kwanta bacci, dama
batayi bacciba tana jiransa ya dawo ya ijiye
wayansa tana tabbatarda yayi bacci ta dauki
wayansa ta shige bayi ta kulle ta danna power
off screen din yayi duhu ta duba da kyau sahun
hannunsa ya yake zana pattern dinsa bataci
wuyaba tana zagaya yanda taga sahun
hannunsa yabi tayi sa'ar bude wayar pattern
dinsa ba wahala ma, tana budewa ta fara aiki,
farko saida ta budamai Google account sannan
taje play store tayi downloading din latitude
tamai register dama tana dashi ta dauko
wayanta tayi sending request ta karba shikenan
ta gama da wannan duk inda yake matuqar data
dinsa a kunne take zata Ganshi baya buqatar
GPS latitude din, ta shiga SMS bata sami
komaiba taje contact ba wani number da bata
yarda dashiba harda searching na sunayen yan
matansa data sani amma babu ta duba logs nan
ma babu da qanqaro WhatsApp a kulle yake
kuma da pin number kawai zai bude bata
wahalda kanta ba taje gallery ba wasu hotuna
daga nashi sai iyayensa sai kuma na margayiya
Suhaila, gasunan sunfi 100 wani qololon baqin
ciki da kishi ya taso mata ganin hotunan da
Wanda suke tare da Wanda rake ita kadai amma
ba nata ko daya kamar ta goge amma kawai
saita fasa har zata fita sai taga wani folder ta
shiga akwai wani aciki ko wanne an rubuta
empty haka tayita dannawa saida ta wuce folder
14 sannan takai gunda aka rubuta Mrs
PURHUUN, ta shiga ciki hotunan tane aciki daga
kan wayanda ya mata lokacinda ta fara koyon
gayu gun Yar baqa Dana zuwa qauyen da yayi
wasu ma ya saka su a cikin frame mai heart
wasu kuma itada Suhaila ne amma an gutsure
Suhaila ko farahnax wasu ma batasan ya
dauketa suba irin tana zaune dinnan tana shirme
ko kuma tana surutunta tun kamin ta qare
wayewa gasunan dai kala kala, mamaki da jin
dadi suka mamaye mata zuciya ganin ya damu
da ita hatta hotunanta a wayar, sai wani video
da ta gani rawar da suka tabayine itada
farahnax a daki sukayi video ko ina ya samu
ohoooo tana tsaka da kallo taji yana qwanqwasa
bayi tsoro da tashin hankaline suka
baibayeta.....byyy
muhd-Abba~Gana
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive