shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 27 July 2015

WACE CE*********ITA? 92

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??92
Na Abba gana
Yana shigowa ko kallonsa batayiba, duk kunya
ta kamashi, gashi ma abinda yajeyi ya kasa
aikatashi ya Dan Sosa kai yace bakiyi bacci ba!?
Tace nayi faarkawa nayi yanxu, yaga kamar
batayi fushiba sai ya matso kusa da ita zai
zauna tayi xunbur ta tashi kada ka kuskura ka
matso kusa dani tamai kallon raini kamar taga
wani kashi,
Ta kalleshi ai shi mai hali baya barin halinsa
tunda ka saba da Neman mata wallahi ba abinda
zaisa ka daina, ya xa'ayi na iya bacci bayan na
auri miji manemin mata, ido cikin ido ta kalleshi
tace farhaan nayi Dana sanin aurenka, nayi
baqin cikin kasan cewa tare dakai, babban abin
godiya ga Allah shine ba'abinda ya shiga
tsakaninmu, bare ayi xancen hada zuri'a na
tabbatar da yarana sai sunyi baqin ciki da
samin uba mazinaci irinka.!! Amma yanxu kaga
Hankali kwance zan nemi wani miji nayi aurena
kuma wallahi saina fadawa umma halin da kake
ciki..
Farhaan zuciya tayi xafi waishi take gayawa zata
nemi miji tayi aure, yaso ya mammaketa amma
sai ta wuce shi nan ya zauna yana Allah
wadaran halinsa yayi tsaki yafi sau dubu ya kasa
shiga dakin har bacci ya saceshi, iffaat kam ko
dar bata ga bacciba gari ya waye kamar kada
tamai breakfast Amma ta daure ta hada mai
taxo tasa qafa ta shureshi ya tashi, ta kalleshi a
wulaqance tace to aje ayi wanka a tsarkake jiki
ayi sallah, a karya aje gun Neman wasu matan,
aranshi yace wai dan wulaqanci da qafa xata
tayar dashi yaji bala'en haushi Dan kuwa da
atayar dashi da qafa gara a gyaleshi, kuma ga
magan ganun banxa tana gayamai ya kalleta
waike waya gaya miki Neman mata naje?! Cikin
isa da tsabar rasjin kunya Tace sabida ba
namijin kirkin da xai bar gidansa 12 na dare ya
dawo 3 sannan yace ba gun banxa yake
zuwaba, bare kaida akasan halinka na Neman
mata....
Farhaan dai ya kasa magana yayi wanka ko
karyawa yakasa yi ya Dan saba tana bashi a
baki yau kam yasan koxai mutu bazata bashi
abakiba,
Haka ya dawo office guraren yamma ta qare
girki tayi kwalliyarta kamar ba itaba.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive