shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 22 July 2015

WACE CE*******ITA? 68

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 68


by

muhd-Abba~Gana


Gari ya waye ma amaren farhaan yana jiran
amai breakfast amma shiru har 12 yunwa ta
isheshi ya duba ko ina ba alamar girki sai
hayaniyar mutane, Yakama hanya ya fita abinsha
bai dawoba sai guraren daya na dare bata
damuba cox yan ganin amarya da qawayenta
sunanan sunyi girki sun debe mata kewa, bayan
sun tafi sannan ta fara tunanin ina yaje!? Daya
na dare ya dawo daya shigo tamai kallon
tuhuma tana Palo bai kula da itaba ya wuce
dakinta,
Koda ta shiga ya shiga wanka ta zauna bakin
gado har ya fito ta kalleshi yana goge kai alamar
wankan xxxxxx yayi. Ta fuskanceshi da kyau,
tace ina kaje yau? Gurin abokaina ya bata amsa
yana chire doguwar rigar dake jikinsa dagashi
sai towel bata taba ganinsa hakaba sai yau tsoro
yakamata ta tashi ta koma palo, ranar dai batayi
bacciba zuciyarta cike da tuhume tuhume, sai
guraren asuba bacci yayi awon gaba da ita bata
farkaba sai guraren 12 Subhanallahi yau tayi
lettin lecture dole taje ta nemo abinci ta tashi ta
fita direvan bayanan an ma fita da motar da ake
kaita skull da ita tayi tsaki tafito ta taka sosai
sannan ta sami mai adaidaita sahu ya dauketa
koda taje Al nasiha restaurant abincinda takeso
ya qare aka mata kwatancen wani guri inda zata
sami abincin ta qara tsayawa chan saiga mai
adaidata sahu ta tsayar dashi suka tafi sun isa
gurin tace ya jirata ta fito tana zaune tana jiran
a hada mata abincin taji ance farhaan, wani rass
taji mace ce ta kira Sunansa ta juyo ta kalleta
ga dukkan alamu tasan ta amma ta manta ina
tasanta Dan kamar ta qara fari yanxu, ta kashe
kunne taji tace Tana xuwa yanxu. Iffaat tace ina
xataje oho? Tana fita tabi bayanta Tana kallo ta
tsallaka titi sai taga ta shiga wata villa a gun,
tayi tsaki, ta dawo abinta ta karbi abinchinta ta
shiga adaidata sunxo daidai villa taga motar da
ake kaita makaranta....
Jiki na rawa ta tsayarda mai adaidaitan tace
Tana xuwa qirjinta kamar ya fito Dan tsananin
tashin hankali wata zuciya tana kije wata na
fadin kada kije, haka ta shiga gurin taje gun
Masu coffee ta nuna musu hoton farhaan
mutumin ya gaya mata dakin da yake zama
kullum, taje dakin da qarfin guiwa za'ayi kashin
kai wallahi!
Ta bubbuga farhaan ya taso ya bude mata,
tsaye yayi yana mamakin mi tazo yi anan gurin
ya kalleta mi kikeyi anan ta watsa mai harara
abinda kakeyi shi nakeyi ta shiga dakin ta duba
ko ina ba mace, tazo ta kalleshi karuwar taka
bata Iso bane??
Keeee waike bakida hankaline?? Mutum bai isa
ya fito shaqatawa ba sai ace yaje gun karuwai
wall.......
Sheeee ta katseshi da Dora hannu a lebenta...
da kunnena naji kana waya da karuwarka kana
taxo ka iso tazo kuyi iskancin da kuka sabako??
Ya daga hannu zai wanka Mata mari tuni ta riqe
hannunsa,...

muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive