shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE**ITA? 42

WACE CE ITA..?? 42
Na ABBA-GANA
Rayuwa gidan mahaifiyarta Yana mata dadi
matuqa tana samun gata ta kowane fanni,
Sai yanxu ta gane cewa wannan garin garinsu
farhaaah ne, koda ko za'a kasheta bazata bata
gane gidan su farhaaan din amma dai ta gane
makarantarda aka sakata da tana gidansu
farhaaan nan guraren PZ ne. Yanxu kuma Hall
Mark international school aka sakata kuma duk
gurare dayane...
mama ta samo mata mai lesson Yana mata a
gida, islamiya ma tana zuwa anan unguwarsu ta
gyallesu,
saidai a tunanin iffaat xuwa gidansu gun
mahaifiyarta zai sa ta daina damu wa batasan
ba anan gixo yake saqaba ita zuciya kawai
burinta takai ga wannan abin da takeso idan ba
hakaba kuwa ba zaman lfya..
***
Wata rana maman iffaat take tambayarta lfy
bata walwala? Tace ba komai mama. Mama tace
kodai bakyajin dadin zama damune?
Laaaa mama wallahi ba haka bane nafison nan
da ko ina har gidansu..... Sai kuma tayi shiru sai
mama tace har gidansu waye?? Ba kowa mama,
hmmmmm.
nidai da yawa mama nakanji banajin dadine
saina riqajin kamar inason wani abu Amma
bansan ko miyeba haka zan kasance chikin
damuwa.... iffaat tama mama bayanin abinda
takeji, tace wani abin mama sai idan na tuna
yaran gidan da nayi aiki,! Sai nayi tajin raina
yana wani iri, kawai mama shine ba wani abubw
kuma inaga kamar sabone ko mama, mama tayi
murmushi tace Eh inaga sabon ne kawai.
mamadai ta gano cewa iffaat wani take so
amma itama mamar bata fahimci ko wayeba
Kuma iffaat din har yanxu batada wayon da zata
san cewa ta fada tarkon soyayyar farhaaan ne,
mama da ta fahimci halin da yarta take ciki sai
ta dada janta jiki ko zata mantar da ita wannan
mugun ciwo da yake addabarta..
Sau da yawa idan iffaat ta shiga daki ta fara
tunane tunane sai taga kamar ba ita bace.. taci
kuka taci kuka har ta godewa Allah....
*
Wata rana iffaat bayan ta fito a class sai ga
wasu yan samari sun wuceta tana jikin class
suka fara mata hy yan mata ji mana,! iffaat
kamar bata jisuba, sukayi iskancinsu suka gaji
suka wuce bata ko daga kai ta kallesuba, har
sukaje suka dawo suka qara mata tayi banxa
dasu....
Bayan sun wuce tana zaune sai ta fara tunanin
iskanchin da aka mata ta gyale, anya nice iffaat
kuwa? Wacce Ko ba'akasa dani nakan siya,
nakan sayi fada da kudina bare a tsokaneni,
waima wayannan yaran zasu min iskanci na
gyalesu tayi tsaki kamar an tsira mata allura, ta
tashi ta fito tsakiyar makaranta don nemansu,
fitanta keda wuya tayi karo da malamai suna
kora a koma class juyawanda zatayi head boy
dinsu ya fara tsula mata bulala tayi class a guje
amma taji bulalar ba kadan ba taso ta bisu ta
musu nata rashin kunya aka koreta, ko minti 10
ba'ayiba ta manta da abin ta koma tunaninta da
baida natija ,.....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive