WACE CE ITA 41
Na ABBA-GANA
Tun da safee iffaat ta shirya kayan da take
buqata sai rawar jiki takeyi duk da har yanxu
zuciyanta a qunci take hakan bai hanata
zagwadin ganin mahaifiyarta ba, goggo ta
sakata taje tayi ban kwana da mutanen , taje
tayi bankwana dasu, wasu nata mamakin
natsuwarta kowa na fadin albarkacin bakinsa,
taje gidan qawayenta dijee da tsohon ciki abin
sai Wanda ya gani, tana tsaka da ban kwana
akace mata yayan ta yazo zasu wuce, a gurguje
tayi sallama ta dawo gida...
Ranar goggo tayi kuka kamar ranta zai fita tana
ganin kamar hanyar samunta duk ta to she
kenan... ta manta samu da rashi na Allah ne....
**************
Guraren 6 na yamma suka Isa zaria birnin
zazzau amma iffaat anyi bacci a mota so bata
gane garinba, direct unguwarsu aka wuce da ita
gyallesu, iffaat sun tararda mama tana ta gyare
gyare tarbon autarta, tana ganina taxo ta
rungumeni tana yan hawaye, nima hawayen
nakeyi Yaya Ameen kuwa yanata dariya, yace
mama murnace haka harda kuka haba miye aciki
Dan ba iffaah tunda nida Yaya Ali mumanan,
dama kullum ta damesu da zancen iffaah
autarta, mama ta harareshi ai kowa matsayinsa
daban, taja autarta suka wuce daki suna
marmarin ganin juna,
a takaqaice zuwan iffaat yayimusu dadi babban
yayan su mai suna Yaya Ali shine babba kuma
Allah ya azzurtashi matuqa tun bayan rabuwar
mamansu iffaat da babansu ta dawo birni gurin
yayanta dama chan su yayyen iffaat gurin yayan
mamansu suke suna karatu so basuyi zaman
qauye ba iffaat ce kawai gurin mamar kuma da
suka rabu da baban sai ya kwace ta da qarfi da
yaji... Yaya Ali Allah ya azzurtashi sosai bayan
business da yakeyi tareda qanin mamanshi yana
aikin Kaduna in short dai suna shanawa wannan
gidan ma da suke ciki shiya Gina ma mamashi...
Iffaat ta kalli gidanda suke ciki aranta tace
wannaan gidan kenan gadansune zatayi duk
abinda take so bawanda zai hanata rayuwa
sabuwa jin dadi sabo komai sabo saidai batasan
bazata iya chanza kuntacciyar xuciyartaba....
Lol.
WACE CE ITA? 41
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.