shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 5 August 2015

Sireenah**********3

muhd.jpg

Sireenah 3


Tsohon ambassador Nigeria na misra wanda a
yanzu yana rike da sarautar sarkin Arewa yana
zaune garin Abuja tare da iyalansa, Alhaji Yahya
Yusuf mutum ne mai saukin kai gason
talakawansa haka Kuma yana Kishin kasarsa
sosai Kafin ya gina ma aikata kasashen waje sai
da yatabbatar da ya gina fiyeda da goma a
kasarsa wanda akasarin masu hannu da shunin
yanzu babu ruwansu da kasar su sai dai akai
arziki wata kasa "ya "yansu bazasu zauna
kasarsu ta haihuwa karatu ba sai an fita daganan
wasu "ya "yan zakuga an tashi ba tarbiyar kwarai
Allah yadai yasa su gane amma fa duk da haka
wasu ra'ayine ke sa su fita karatu waje! Mai
martaba Yahya Yusuf yana da mata kwaya daya
tal mai suna Amina tahaifi yara biyar hudu mata
while autansu na miji NE gabaki daya matan
hudun sunyi aure saura auta mai suna Suhail
wanda yana karatu a Nile university Yana karatun
Medical Doctor suna matakin karshe ne, Suhail
yaro ne matashi kyakkyawa mai kiran mazan
kwarai (kusan akwai wasu maza kamar mata
idan ka kallesu ) Yana da farin jini ga yan mata
sosai mata dayawa sun yi sha awar yaso su koda
na second ne but yagagaresu don yasani badon
Allah suke sonshi ba shiyasa gabaki daya baya
kula mata, mata biyu ne yake kulawa dayar "yar
abokin maihaifinsa Azeeema itama tana karatu a
Nile university course dinsu daya hakama ajin su
daya shiyasa ko ina zaka gansu kusan tare kake
ganinsu with their friends ita Azeeemar ta maida
abin soyayya shiko Suhail ba haka abin yake a
wurinsa ba kawai dai he took her as friend
Azeema bakalarsa bace, kada kuyi tunanin
Azeema mumuna ce a'a itama tana da nata
kyaun daidai gwargwado sai dai gaskia bata da
halaye masu kyau takasance irin "ya "yan richies
dinnan ne masu takama da kudin su ga girman
kan tsiya tana kyamar talakawa sosai Inshort
tamayar da talakawa slaves hardai masu yi masu
aiki a gida duk inda taga talaka sai ta toshe
hancin ala dole suna wari bata ma kaunar taga
talaka yakusance ta tsanesu sosai shiyasa Suhail
baya iya soyayya da ita balle yazauna da ita
matsayin mata don shi mai saukin kaine ba
ruwansa da wannan talaka ne ko mai kudi
wurinsa duk dayane. Yana kaunar maccenda ta
dauki rayuwa so simple wadda baruwanta da kudi
etc Sai dai shi a ganinsa ba a samun macce irin
haka Shiyasa yatattara mata yasa su cikin
kwandon shara amma banda wata qawarsa
wadda yake tsananin ji da ita he can even
sacrifice his life for her saboda she is special don
yana ganin tana 70% cikin abubuwan da yakeSo
(wacece wannan mai sa a? anya kuna ganin ba
sonta yake ba? Gamu gani nikaina Abba~Gana
banda amsar wannan tambaya amma Abdallah
bazai rasa ba )Suhail yana da problem kwara
daya dake damunsa mahaifansa sun takura mashi
daya fidda mata koda baiko NE ayi masa amma
ina abu yagagara kullum shi maganar sa baiga
wacce yake so ba har ma iyayensa sun fara
tunanin baya da lafia basu san garau yake ba ni
aganina bawani matsala bane wannan ga mata
nan buhu- buhu sai yazaba ko ba haka ba? )
Nasan masu karatu zasu ce Kuma wanene
wannan Suhail? duk da nadanyi bayanin
waneneshi but nasan kuna bukAtar karin bayani
ko?
***********
Sireenah yace ga Alhaji Sadam Saraki wanda
shahararren dan kasuwane yayi fice ta bangaren
kasuwanci a countries da dama harda gida Ngeria
yana da companies da dama tundaga Nigeria
zuwa outside countries, yana zaune ne da
matarsa mai suna Hajia Aisha Ashrab wanda
auren soyAyya ne sun hadu lokacin da yaje
kasarsu kasuwanci asalinta yar shuwa Arab ce
bayan aure suka dawo Nigeria dazama sunfi
shekara biyar ba haihuwa sun yi yawon asibiti da
dama aka tabbatar musu lafia lau suke daga baya
suka dangana sai daga baya tasamu cikin
Sireenah wanda tun randa tasamu cikin yafara
bata wuya wato cikin yazo da laulayi mai tsanani
har yayi sanadin samo mata macce mai kula da
ita mai suna Fateema irin mutanan ne dasuka
jiku cikin bariki idan kunga yadda take behaving
zaku zata ko samata hannu a baki akayi bata iyA
cizawa, sun shaku sosai da Hajia Aisha sanadiyar
Kyawawan halin data nuna har Alhaji Sadam yana
ji da ita ashe basu sani ba Fateema zagon kasa
takeyi musu tana jira ne su gama sakakancewa
da ita daganan tasan yadda zata salwantar da
rayuwarsu ta ci dukia domin tayi bincike kan
Alhaji Sadam maraye NE tun tashin sa baya da
kowa sai abokan arziki, tana sane Hajia Aisha ba
yar 9ja bace shiyasa take ganin zasuyi saukin
kashewa, watarana Fateema ta saci hanya sai
guriin boka a garin kogi dayake banisa sosai
tasamu biyan bukata wurin boka Adeku don
yabata tabbacin samun nasara mudin tasa cikin
abincin Hajia Aisha bayan dawowarta ta aikata
abinda boka yace aiko Hajia nagama cin abinci
tafara zubar da Jini dole akayi rushing dinta
asibiti dakyar aka ceto ran jaririyar while Hajia rai
yayi halinsa Alhaji Sadam yayi bakin cikin
rashinta ba yadda zaiyi dole yahakura ya rungumi
yarinyarsa KO banza jaririyar tana Kama da
matarsa. Fateeeema itama tayi kukan rashinta
kamar dagaske (kunji makirar mata kamar ba
itace silar hakan ba. Bayan angama biki inda
jaririyar taci sunan Sireena
muhd-Abba~Gana
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).