sireenah***********--7
Sireenah 7
muhd-Abba~Gana
Suhail marina fa kayi kan waccan sharar? Haba
azeema waike har yaushene zaki canza? kullum
cikin wulakanta mutane kike bakya tunanin kema
Allah ya jarabbaceki dazama talaka? ko kina
ganin ana dauwama cikin jin dadine? suma ai
talakawan Allah yana sane dasu yayi su ahakan.
Bansan me wannan baiwar Allah tayi maki ba duk
kin takura mata. Azeema takaici yasa takasa
furta masa komai banda kallonsa da take cikin
mamaki tun tasowarta ba'a taba samata hannu
ba balle a mareta amma gashi yau Wanda take
kurin yana sonta shine yadaga hannu ya mareta
kan wata kucaka. Da suhail yaga bata da niyyar
kulasa yakoma kan Sireenah kiyi hakuri baiwar
Allah, Allah zai saka maki.. Lokacin sireenah
tasamu damar amsa masa Wanda yayi daidai da
haduwar idanuwansu abin mamaki zuciyoyin
junansu yabuga da karfi bashiri sireenah tasauke
idanuwanta daga nasa, bakomai nagode malam
sai anjima. Harta tafi yana mamakin zakin
muryarta a ganinsa baidace da'ita ba. Tafiyar
sireenah keda wuya Azeema da suhail su kayi
fada sanadiyar haka suka rabu, suhail yaji dadin
rabuwarsu daman tana takura masa while
azeema bataso fadan nasu ba amma girman kai
irin nata yahana ta amsa laifinta takara tsanar
sireenah a ranta......
Ranar wanka ba'a boyon cibi.... yaune ake
birthday din suhail mai aikata sai aikace aikace
akeyi komai cikin tsari akeyinsa gwanin sha'awa
anyi decorating na mussamman bama kamar
gurin da aka kebe domin gudanar da shagalin
daga india aka dauko masu decorations din
bazance tsayawa fadin yadda aka aka kawata
wurin sanin kanku ne babu Wanda yakaisu
(Indians) iya decorations ........
Tun karfe 10 na safe muneera take gidansu
sireenah tare sukayi aikace aikacen da sireenah
keyi basu gama ba sai 1:30 don haka suna
gamawa sallah sukayi hadi da wasa ruwa.
Yakamata ace sunci abinci ko don uwar aikin da
suka sha amma bahali muneerah bata damu ba
saboda tana sane da hali irin na mommy tee,
kinsan Allah kamar mommy tee bazata barni naje
partyn ba kinga yadda suke shirin birthday din?
Komai fa daga Dubai fa akayi order kamar su
za'a yiwa hatta motocin dakike gani can a rufe
nasu ne domin wannan rana aka tanadesu, ni
bama shi yafi damuna bata kaunar na kusance su
yakike ganin za'ayi partyn muna inuwa daya
dasu? Nidai kawai tashi mutafi ki gaya mata
zakije lectures Kuma daga 3pm za'a fara zuwa
dare.
Dama a sireenah a shirye take nan ta dauko
powder dinta wato shoe shiner tafara gogawa,
muneera salati tasaka tana tambayar sireenah
kanki kalau Kuwa? wannan shine powdernki?
Bata bawa Kawarta amsar tambayarta ba sai
bayan tagama shirinta tsab kana ta kwashe
labarin dokokin mommy tee muddin tana son
zuwa school muneerah har hawayen bakin ciki sai
da tayi, Don't worry Kawata kicigaba da hakuri
wata rana sai labari oya zomuje kinemi izininta,
sun kama hanyar Zuwa sashen mommy tee bayan
sun kai bakin kofar sireenah tayi sallama har sau
3 ba'a amsa ba har suna batun tafia kana sukaji
magana Lafia wane? Mommy tee ni ce, karaso
daga ciki, daman nazo ne nasanar dake zan wuce
makaranta, Kije mana fatar kina da kudin taxi ?
Eh mommy inada. Daman ko bakida bai dameni
ba bazaki ci kwandalana ba koda yake ga
matsiya ciyar Kawarki nan nasan zata baki nidai
kin tabbatar kin karemin dukkan ayukkan dana
saki? Eh nakare. Idan ma baki kareba wallahi ko
1:00am na dare ne sai kin tashi kinyi shi; fita
kibani Wuri Allah yasa a bokon kiyi cikin shege!
Haka tafita dakin mommy jiki a sanyaye idan da
sabo yaci tasaba da zagin mommy tee muddin
zataje school da muguwar addu'ar datake hadata
Allah yashirya mana mommy tee.
Sun danyi tafiya mai nisa kafin suka kai daidai
wurinda muneera tayi parking din motarta,
mommy tee batasan muneerah 'yar manya ce ba
da tuni ta rabasu bata kaunar wani/wata mai
arziki su kusanci sireenah saboda hassada irin
nata, duk zuwan muneerah gidan bata isa da
motarta gidan sai dai tanemi guri tayi parking
kafin taje gidan shiyasa mommy batayi tunanin
yar masu dashi ne kallon kaskanci mommy tee
take mata!
Bayan shigarsu mota basu nufi gida ba sai wurin
masu gyaran fata, gashi, lalle etc. Sai 'ya 'yan
wane da wane ke zuwa gun, anyi musu gyara na
mussaman bama kamar Sireenah wadda asalin
Kyanta yafito tayi kyau tamkar ita tayi kanta,by abba gana
bata da babbanci da sabuwar amarya har wankin
hakora anyi musu! Duk Wanda yagansu sai sun
burgeshi suna dan da yanayi da muneera but
gaskia tafi muneera kyau babu yadda za'ayi kaga
Sireenah ka shaidata sai idan kayi mata farin
sani tun farko! Basu bar shagon gyaran ba sai
dare around 8:57pm kenan saura 1:03 afara
birthday partyn.
Zan cigaba Insha Allah...
muhd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz
Pls ayima post din sireenah daga 8 xuwa karshe
ReplyDelete