shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 7 August 2015

INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.

banna.jpg

A MATSAYINKI NA MACE BUDURWA
INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA
DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.
(1) ki tsayar da saurayi guda daya tak na
kirki bisa la akarai da ayyukan sa da
halayensa na zahiri.
(2) kitabbata kina sonsa sosai kuma shima
yana sonki sosai.
(3). Kada ki yarda kidade da saurayi, ko
kishaqu dashi ko ki nuna masa tsananin so
batare da iyayensa sun gana da iyayenki
ba.
In yaqi turosu kirabu dashi tunkafin
yagama sace zuciyarki.
(4). Kizama mebin shawarar iyayenki, da
neman shawararsu a harkar soyayya, kada
kibi shawarar Qawaye ko saurayi kobin
shawarar zuciyarki.
(4). Kada kiyarda a kawo miki gulmar
saurayinki ke kuma kidauka koki kama
zargin sa.
A'a sai kinyi bincike na adalci ko kingani
da idonki.
(5). Kada ki kuskura kiyiwa saurayinki
qarya kizama me fada masa gaskiya ,da
yimasa bayanin komai iya saninki.
(6). Kizama me yawaita addu'ah da bawa
Allah zabi a dukkan lamarinki..
(7). kikiyaye zargi da binciken laifinsa
matuqar ya sanar dake komai bai 6oye
miki gaskiya ba.
(9). kidauka dan adam tara yake bai cika
goma ba, kinga zai iya kuskure, dan haka
sai kiyi masa afuwa.
(10). kizama me kare mutuncin kanki ,da
kuma kulada matsayinki batare da girman
kaiba ko jan aji ga masoyi...
JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE
HAIFARWA SAI NADAMA.
idan saurayinki ya tsaneki ko yagudu
yabarki ko kin rasa wani abu da yake baki,
kiyi haqury kada kijuya masa baya, kisa
masa shakka a ransa yadinga tunanin anya
kuwa kina son sa da gaske ???
KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA
IYA TAKUNKI
(11). Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki
fuska yana shigo miki da kalmomin da
basu daceba ko dabi'u.
kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar
waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga
fulawarki ,ko zai auna kaurinki dadai
sauransu.
SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI
ADUK SADDA KIKAGA HAKA, KODA
YATAFI KIRABU DASHI, DAMAN BA
NAGARI BANE, SOYAKE YA BATAKI.
Wakilin shaytanne.
(11). Kizama me yiwa saurayinki Al-
qawarin nuna masa soyayya bayan
aurenku, sannan dayi masa biyayya dai dai
gwargwadon
iyawarki.
KISANI DAYAWAN SAMARI AKWAI
MAKIRCI.
Wani yasan ba aure zaiyi ba amma zaizo
yabata miki lokaci.
Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo
wajenki yayi tayi miki qarya batare dakin
fargaba zai dasa miki ciwon so, YA KORAR
MIKI SAMARIN KI NAKIRKI.
Wani kuma kawai so yake yana zuwa
wajen fati dake.
Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala
yana fira da ke zai fake da cewa SAI
YAGAMA School KO SAI BAYAN YAGAMA
KARATU ZAI TURO KUYI AURE.
Duk fati ko fikines zai daukeki kutafi.
Wani kuma soyake kawai yana taba jikinki
yaji dadi koda bai kwanta dakeba, saboda
haka zaita binki sauda qafa yana
soyayya dake.
Wani kuma so yake ya bataki.
Irin wadannan samarin sunfi kowanne
hatsari.
Idan yaganki yana sonki yana fara karantar
halayenki IDAN YAGA KE USTAZIYACE TO
ZAIYI SHIGAR USTAZAI HARDA
LITTAFIN SA A HANNU ,HAKA ZAITA KAFA
MIKI TARKO HARSAI KIN FADA.
Idan yaga 'yar BOKOCE zai fito miki a dan
boko.
Idan yaga ke yar duniya ce toshima a
hakan zai fita.
Irin wadannan samarin har kayan mungani
munaso suna kaiwa budurwa, har
iyayensu suna turowa daga qarshe daya
kwanta dake shikenan yabiya buqatarsa,
bazai bari kisami cikiba zaibaki qwaya da
zarar yaga baki da ciki yasan yayi free
tunda yasami abinda yake nema, zai
Qirqiri laifi yalaqa miki domin ku6ata a
karbo kayan sa daga gidanku, koma yabar
miki kayan...
Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran
soyayya ga budurwa, domin sukanyi kukan
hawaye a gaban budurwa duk da sunan so
amma yawanci domin ya raunana zuciyar
kine.
Yakan maqale miki har unguwa yana
rakaki koda yaushe.
YAR UWA IN SOYAYAYYA TAI GARDAMA
WAYE YAFI SHAN WUYA DA
TOZARTA ???
SHIN ANAIWA NAMIJI CIKIN SHEGENE KO
BUDURWA AKEWA ???
IDAN ABIN KUNYA YAFITO WAYE ZAI
ZAUNA A GIDA KO MAQOTA BAI ZUWA
DAN KUNYA NAMIJI KO MACE ???
MEYASA NAMIJI ZAI IYAYIWA YAN MATA
BIYAR CIKI BATARE DA AURE BA AMMA
INYAZO NEMAN AURE SAI ABASHI ???
IDAN KUWA MACE TAYI CIKI SAU DAYA
DA
KYAR TAKE AURUWA KOMA SAI TABAR
GARIN ???
MEYASA MACE INTAI CIKI AGIDAN SUMA
TSANARTA AKEYI ,AMMA NAMIJI DAYA
KAWO RAGO DA KUDIN ICE SHIKENAN ???
MATA NAWANE SABODA CIKIN SHEGE
SUKABAR GARINSU KO RAYUWARSU
TA GURBATA AMMA SHI NAMIJI
KAMARMA BAIYI KOMAI BA ???
KO KAMUWA KIKAI DA MUGUN CIWO
WAZAI KULA DAKE YABAKI KUDIN
MAGANI DUK WATA ???
KINTABA GANIN ANSA WUQA A
WUYAN NAMIJI ANCE INBAKA FADI
WACCE KAYIWA CIKIBA SAINA
YANKAKA ???
AMMA WA AKEWA HAKA ???
'Yar uwa kada dadin soyayya, ko dan kudin
da saurayi zai baki kodan zai saki a gaban
mota ,kodan wasu yan riguna dazaina saya
miki HAKAN TASA KIBASHI DAMA HAR
YASANKI 'YAMACE WALLAHI KIN KADE.
IN HAKAN TAFARU TO KITUBA GA
ALLAH (S.W.T) DOMIN SHI MAI
GAFARANE.
FATAN "TAFARKIN TSIRA" ANAN SHINE,
ALLAH YASHIGA TSAKANIN NAGARI DA
MUGU.
ALLAH YAHADA KOWACE YA MACE DA
SAURAYI NAGARI DA ZATA KAISU
GA AURE NAGARTACCE.
MUMA MAZAN ALLAH YABAMU MATA
NAGARI.
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive