shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 7 August 2015

sireenah**********--10

samp906c78071de1d454.jpg

Sireenah 10********NA***********
muhd-Abba~GanaFunny girl lafia? Daman kinsanni ne? Naga kamar
kin tsorata daganina, Ko kinfasa so nane? Please
funny girl talk to me. Dakyar sireenah amsa masa
da uhm...mm a' a bakomai cikin jerin tambayoyin
da yayi mata. Okay toh zauna mana ga wuri nan
dana tanadar miki! An kayata wurin swimming
pool din sosai, ruwan cikinsa yanada haske
tamkar ba'a shiga cikinsa! Kujerun shakatawa sun
zagaye ruwan, ta bangaren ruwan akwai
matsakacin rumfa wanda a karkashinsa akwai
kujeru biyu da table saman table din akwai
furanni da kayan motsa baki Wanda kamar lover
boy ne ya tanadawa sireenah. Bayan sun zauna
ne yafara bayani kamar haka:- Nasan zakiyi
mamakin sosai akaina, abinda nake gaya maki a
chat bashine kika gani a zahiri ba, yanuna mata
cewa shi dan dako ne, primary school kadai
yakare baisamu damar cigaba karatunsa saboda
halin rashi na mahaifansa dalilin haka yabar
karatun don ya tallafa masu a karshe shine ke
dawainiya dasu. Gashi Taga tsabanin abinda
yafada mata fatarsa da tufafin dake jikinsa kadai
sun isa kasan koshi waye, balle shi sannanne ga
mutane, sireenar ma tayi masa farin sani. Nasan
ko asalin suna na baki sani ba koda yake
laifinane bangaya maki ba kema baki nemi sanin
sunan nawa, bansan meye dalilinki ba sai dai ni
inada nawa dalilin bakomai bane face nasamu
mai sona tsakani da Allah, sanin kankine dakyar
nasamu mai sona idan zan nuna ni wani. Dayake
Allah maijin rokon bayinsa ne yahadani dake
wanda nake ganin tamkar nafi kowa sa'a duniya
samun macce irinki sai an tona, fuskarki kadai na
gusar da bacin rai, muryarki koda zan sauraresa
daga safe zuwa daare bazan gaji ba gaskia
Alhamdullah. Ni suna na Suhail Yahya Yusuf
nasan bazaki rasa sanin waye ni muddin a garin
Abuja kike zama but never the less ni haifafen
dan kebbi ne ina karatu a Nile university studying
medicine mun kusa gamawa gidanmune nan, nine
ake yiwa birthday ,haka yacigaba dagaya mata
koshi waye batace masa uffan ba har yakare
already tasan koshi waye but bana tunanin suhail
yaganeta amma kamar yana zargin muryarta
kamar yataba jinsa sai dai yakasa tunawa,
yabukaci sireenah tabashi labarinta wanda tayi
alkwalin bashi duk randa suka hadu sai gashi
haduwarsu ba'a yadda tayi tunaninsa bane, nan
tasoma bashi wani labari daban inda tace masa
sunanta Safnah tana karatu a Nile university zata
cigaba da labarin kira yashigo mata koda taduba
mommy tee Ce cikin rawar jiki ta amsa kiran,
"kitabbatar kindawo gida cikin mint 15 ko baki
gama lectures din ba i dont care, akwai abinda
zakiyi mani kada kifi 15mints baki dawo ba
muddin kikara ko minti daya cikin 15mnts din
kinsan saura! Ganinan tafe mommy insha Allah!
Tana gamawa kiran muneerah yashigo Sireenah
kizo mutafi yanzu aka kirani gobe dasafe zamuyi
test Kuma idan nayi missing zanyi kari over dinsa
anyi mani booking flight in 20mnt jirgin zai tashi
so hurry up please kizo mutafi. Gani nan tafe
yanzu nima mommy tee tasanar dani tana nema
na cikin gaggawa. Suna gama wayar yayi daidai
da suhail shima yana waya and his attention
yanaga wayar saboda mahaifinsa ne yakirasa
yabata baya! So sireenah bata da choice than tayi
tafiyarta batare da sunyi sallama ba don ta kagu
ta'isa gida. Tafiyar ta keda wuya yagama wayar
da yakeyi koda ya juyo baiganta ba ya dudduba
ko'ina banganta ba har ta gun da ake birthday
din,motocinsu tuni sun dade da barin harabar
gidan , baiji dadin hakan ba gashi baisan address
din gidansu ba, har aka gama birthday din he was
sad.
**********
Tun a mota tafara canza tufafinta daman dashi
taxo, tagoga shoe shiner dinta inshort takoma
yadda take a baya duk wanda yaganta baxaice
itace sarauniyar kyau ta daxu totally takoma
blacky. Sun yi ban kwana da muneerah cikin
kewar juna suka rabu. Allah sarki kawayen basu
damar hira ba balle sireenah tagaya mata wane
lover boy.
Koda sireenah taje gida bata tarar da mommy tee
a parlour ba shiya bata damar hiding tufafinta na
birthday a dakinta kafin taje sashen mommy tee,
abin haushi bawani aikin Kirki bane tea zata
hadamata da indomie wanda yan aikin ma zasu
iya. Tana cikin aikin ne yan biyu suka shigo
ransu a bace da alamu kwalliyar tasu yatashi a
banza. Oyoyo my twins yanaga kamar ranku
abace kodai banasara ne? Mommy tee kedai bari
wata banza tayi mana kwacensa da alamu jinin
sarautace, muna cikin zagaya wa da Hussai muka
hangoshi da wata munso muje ganin wacece
securities din gidan suka hanamu karasawa!
Tabdijan ko wacece tadebo ruwan dafa kanta tayi
kadan tayi sharing saurayi with my twins. Abinda
nake so daku find out yar gidan uban waye
nikuma zansan yadda zanyi da ita karshe ma na
salwantar da rayuwarta . Duk abinda suke fada
akan kunnen sireenah ta tsorata sosai gudun irin
rikicin nan yasa taki gaya masa asalin sunanta
tana sane da bakin hali na mommy tee mugunta
abune mai sauki a wurinta. Yanzu menene
mafita?....


muhd-Abba~Gana


For more vist

Www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

  1. khadijah a salahudeen15 August 2016 at 00:11

    NICE,yayi kyau,amma a karasa book 3 pls n pls

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).